ukarofi

12353 Posts
Bakori zai jagoranci kwamitin yaɗa labaran Tinubu/Dikko 2027

Bakori zai jagoranci kwamitin yaɗa labaran Tinubu/Dikko 2027

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙwararren ɗan jarida, Ahmad Abdulkadir Bakori, zai jagoranci kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da kafafen yaɗa labarai na kamfen ɗin Tinubu/Dikko 2027, yayin da kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango, zai zama sakataren kwamitin. Kwamitin zai kula da yaɗa saƙonnin kamfen, hulɗa da kafafen yaɗa labarai da kuma daidaita sadarwar kamfen da jama’a. Naɗin ya kasance wani ɓangare na tsarin gudanar da harkokin yaɗa labarai da sadarwa na kamfen ɗin Tinubu/Dikko na zaɓen 2027. Ahmad Abdulkadir tsohon shugaban gida talabishin na Jihar Katsina yayi aiki a hukumar NBC inda yakai matsayin…
Read More
Kotu ta umarci APC ta sake zaɓen fidda gwani a kujerar majalisar wakilai ta Argungu da Augie

Kotu ta umarci APC ta sake zaɓen fidda gwani a kujerar majalisar wakilai ta Argungu da Augie

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ranar Laraba din nan ne kotun tarayya da ke zama a garin Birnin Kebbi ta yanke hukuncin ƙarar da Sameer Salihu ya shigar inda ya ke ƙalubalantar nasarar Umar Hassan (Turakin Augie) a zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a watannin baya.Kotun ta ce ta buƙaci jam'iyyar APC ta gudanar da sabon zaɓe a cikin sati biyu daga ranar da aka yanke wannan hukuncin.Sameer Salihu dai ya shigar da ƙarar ne inda ya ke ƙalubalantar nasarar Umar Hassan Turakin Augie saboda a cewar sa babu wata mazaɓa da aka tara mutane aka yi sahihin…
Read More
Zaben 2027: An shawarci ‘yan siyasa da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin tsafta

Zaben 2027: An shawarci ‘yan siyasa da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin tsafta

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar Gwagware Musa Adamu Kwamred Mannir Suleiman ya jijinawa uwar jam'iyar APC ta ƙasa da ta Jihar Katsina kan irin fitattaun mutanen da ta naɗa a kwanmitin daban daban na yaƙin neman zabe na 2026. Kwamred Suleiman ya bayana cewa Jam'iyar APC tayi hangen nesa da ta zaɓo mutane masu kima da daraja a wajen ya'yan jam'iyar APC " "Musamman a nan Jihar Katsina waɗannan mutane sun bautawa jam'iyar APC da tabbatar da jam'iyar ta zauna da ƙafafunta. Shugaban ƙungiyar ya kuma yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa da uwar jam'iyar APC ta Jihar da…
Read More
Ya rasu kwana guda kafin fitowar littafinsa na ƙarshe: Marubucin ‘Kane and Abel’ Jeffrey Archer ya mutu yana da shekara 86

Ya rasu kwana guda kafin fitowar littafinsa na ƙarshe: Marubucin ‘Kane and Abel’ Jeffrey Archer ya mutu yana da shekara 86

Daga AISHA ASAS Akwai marubutan da mutuwarsu ke rufe wani shafi kawai na rayuwarsu, amma akwai waɗanda mutuwarsu ke sa duniya ta sake waiwayar irin tasirin da suka bari a duniyar littattafai. Ga marubucin Birtaniya Jeffrey Archer, labarin rasuwarsa a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, ya zo ne a daidai lokacin da yake gab da rufe dogon tafiyar da ya yi a matsayin marubuci. Archer ya rasu yana da shekara 86, kwana guda kafin a fitar da littafinsa na ƙarshe mai suna 'Adam and Eve'. Kamfanin buga littattafansa, HarperCollins, ya tabbatar da cewa marubucin ya mutu cikin kwanciyar hankali a…
Read More
Daga marubuta 2,000 zuwa 25: National Book Awards ta bayyana waɗanda suka rage a gasar 2026

Daga marubuta 2,000 zuwa 25: National Book Awards ta bayyana waɗanda suka rage a gasar 2026

Daga AISHA ASAS A duniyar adabi, ba kowane littafi ne yake samun damar tsayawa a inda duniya za ta fara kallonsa da wata irin kulawa ba. Amma idan aka rage dubban littattafai zuwa wasu kalilan, sunayen marubutan da suka rage sukan fara ɗaukar wata sabuwar ma'ana. Haka abin ya faru a gasar National Book Awards ta 2026, inda aka bayyana ‘yan takarar ƙarshe 25 a ranar Talata, 6 ga Oktoba, bayan alkalai sun tantance kusan littattafai 2,000 da aka wallafa a bana. An raba waɗanda suka rage zuwa rukuni biyar: Fiction, Nonfiction, Poetry, Translated Literature da Young People’s Literature. A…
Read More
Godspower Oshodin ya fitar da littafinsa na farko bayan shekaru 14 yana rubuta shi

Godspower Oshodin ya fitar da littafinsa na farko bayan shekaru 14 yana rubuta shi

Daga AISHA ASAS Akwai littattafan da marubuci kan fara rubuta su da wani tunani a zuciya, amma kafin su isa hannun masu karatu, rayuwarsa da abin da ya gani a duniya sukan sauya yadda labarin yake. Wani lokaci kuma, tsawon lokacin da aka ɗauka kafin littafin ya fito shi kansa kan zama wani ɓangare na labarin marubucin. Haka abin yake da marubucin Najeriya, Godspower Oshodin, wanda ya fitar da littafinsa na farko mai suna 'Even the Devil Wears a Pretty Smile' a ranar Talata, 6 ga Oktoba, bayan shekaru 14 da fara tunanin littafin. A lokaci guda kuma, ya sanar…
Read More
‘Yan Najeriya sun samu gurbi a zagayen ƙarshe na gasar African Writers Awards

‘Yan Najeriya sun samu gurbi a zagayen ƙarshe na gasar African Writers Awards

Daga AISHA ASAS A duniyar adabi, akwai lokacin da aikin marubuci ya bar hannunsa ya shiga hannun alkalai. Daga nan, ba yawan kalmomin da ya rubuta ne kawai ake dubawa ba, ana duba yadda ya gina tunani, yadda ya ba da labari da kuma irin muryar da aikinsa ya kawo. A wannan makon, marubutan Afirka sun shiga irin wannan mataki bayan African Writers Awards ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka rage a gasar shekarar 2026 ranar Litinin, 5 ga Oktoba. Jerin ya ƙunshi ayyuka daga fannoni daban-daban da suka haɗa da waƙa, prose, gajerun labarai da adabin yara, tare…
Read More
AI na cikin manyan batutuwan da aka tattauna a taron Frankfurt Book Fair

AI na cikin manyan batutuwan da aka tattauna a taron Frankfurt Book Fair

Daga AISHA ASAS Duniyar littafi na canzawa a hankali, amma wasu sauye-sauyen sukan zo da tambayoyin da ba za a iya kauce musu ba. Yayin da fasahar AI ke ƙara shiga cikin rubutu da wallafe-wallafe, masana'antar littafi ta fara fuskantar tambayoyi kan abin da wannan fasaha za ta sauya da kuma abin da ya kamata a kare. A ranar, Laraba 7 ga Oktoba, an buɗe Frankfurt Book Fair karo na 78 a Jamus, inda marubuta, masu wallafa, masu fassara da sauran masu ruwa da tsaki a duniyar littafai suka taru, inda taron zai ci gaba har 11 ga Oktoba. AI…
Read More
Gidajen mai a Kebbi sun rufe sanadiyyar rage farashi

Gidajen mai a Kebbi sun rufe sanadiyyar rage farashi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Akwai alamar an je gyaran targaɗe an karye saboda yanzu haka al'amurra sun tsaya cik a waɗansu sassa na Nijeriya sanadiyyar rage farashin mai na naira sittin na wata ɗaya da gwamnatin ta sanar.A jihar Kebbi wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ya zagaya waɗansu wurare, ya tarar da gidajen mai a rufe sai dai kaɗan daga cikin su da suka buɗe sai dai ba nan gizo ke saƙa ba saboda maimakon a sami sauƙi daga inda aka fito yanzu ana sayar da shi naira 1500 zuwa da ɗari biyar da hamsin.Wani manajan da bai so a…
Read More
Buni ya raba babura 160 ga dakarun tsaron dazuzzuka da ke jihar

Buni ya raba babura 160 ga dakarun tsaron dazuzzuka da ke jihar

Daga SANI GAZAZ CHINADE a Damaturu Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da raba babura 160 da sauran kayan aikin tsaro ga masu gadin dazuzzuka na ƙasa da ke jihar domin inganta ƙarfin aikinsu da kuma ƙarfafa ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Dr. Mohammed Goje, ya wakilta, ya kuma amince da raba rigunan kare ruwan sama guda 900, takalman tsaro (boots) guda 900, barguna 900, fitilun hannu 900, da kuma gidan sauro guda 900 ga ma'aikatan. An tanadi waɗannan kayan ne domin tallafawa masu gadin dazuzzuka su 886 da suka kammala…
Read More