ukarofi

12353 Posts
Gwamnatin Zamfara za ta raba hannun jari a kamfanin ɗangote ga mutane 36,176

Gwamnatin Zamfara za ta raba hannun jari a kamfanin ɗangote ga mutane 36,176

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta amince da wani shiri na bai wa mazauna jihar 36,176 damar mallakar hannun jari a Kamfanin ɗangote, a wani mataki na ƙara inganta shigar jama’a harkokin zuba jari da ƙarfafa tattalin arzikinsu. Ma’aikatar Jinƙai da Agajin Gaggawa ta jihar ce ta bayyana hakan, inda ta ce shirin zai bai wa mazauna damar cin gajiyar hanyoyin zuba jari da kuma shiga cikin harkokin kasuwanci da ke gudana a ƙasar. A ƙarƙashin shirin, ana sa ran kowane mai cin gajiyar zai samu kusan hannun jari 20 ta hanyar tayin sayar…
Read More
Ribadu: Nijeriya ta samar da tsaron bai-ɗaya na kare bututun mai

Ribadu: Nijeriya ta samar da tsaron bai-ɗaya na kare bututun mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da tsararren tsarin aiki da zai jagoranci yadda jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki za su kare kadarorin man fetur, daƙile satar ɗanyen mai da lalata bututun mai, tare da hana tace mai ba bisa ƙa’ida ba. Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi gargaɗin cewa wannan mataki ba zai cimma manufarsa ba sai hukumomin tsaro, kamfanonin mai da ’yan kwangilar tsaro sun tabbatar da cikakken aiwatar da tanade-tanadensa. Ribadu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin, lokacin da ya ƙaddamar da Tsarin Aiki…
Read More
Kara jarin bankunan Nijeriya bai ƙara rance ga ’yan kasuwa ba – Bankin Duniya

Kara jarin bankunan Nijeriya bai ƙara rance ga ’yan kasuwa ba – Bankin Duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bankin Duniya ya bayyana cewa duk da matakan da bankunan Nijeriya suka ɗauka na ƙara jarinsu, hakan bai haifar da gagarumar ƙaruwar rancen kuɗi ga ’yan kasuwa da sauran jama’a ba. A cikin rahotonsa na watan Oktoba na shekarar 2026 kan halin da tattalin arzikin Nijeriya yake ciki, Bankin Duniya ya ce takardun bashi da Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Nijeriya (CBN) suka fitar sun kai kusan kashi 22 cikin 100 na jimillar kadarorin bankunan ƙasar a farkon shekarar 2026. Wannan ya nuna ƙaruwa daga kusan kashi 18 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin…
Read More
Bankin Duniya: Talauci zai ragu yayin da tattalin arziki ke bunƙasa – Tinubu

Bankin Duniya: Talauci zai ragu yayin da tattalin arziki ke bunƙasa – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya yi maraba da rahoton Bankin Duniya na watan Oktoba 2026 kan halin da tattalin arzikin Nijeriya yake ciki, mai taken ‘Bayan Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya: Yadda ƙarin Kuɗaɗen Shiga Ya Sauya Abubuwan Da Jihohi Ke Ba Fifiko’. A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Tinubu ya ce sakamakon binciken Bankin Duniyar ya tabbatar da cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa a fannin tattalin arziki sun fara haifar da sakamako mai kyau, tare da aza harsashin samun ci gaba mai ɗorewa. Shugaban ya kuma yi tsokaci kan bayanin Bankin Duniyar cewa…
Read More
2027: Jam’iyyun adawa sun fara tattaunawa da Atiku, Obi, Makinde da wasu kan ƙudurin G100

2027: Jam’iyyun adawa sun fara tattaunawa da Atiku, Obi, Makinde da wasu kan ƙudurin G100

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyun siyasa na adawa a Nijeriya sun fara tattaunawa da ’yan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyunsu domin aiwatar da ƙudurin da aka cimma a taron G100 na jam’iyyun adawa, gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa Salihu Moh. Lukman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a madadin jam’iyyun haɗin gwiwar a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026. A cewar sanarwar, shugabannin ƙasa da sakatarorin ƙasa na jam’iyyun adawa guda shida sun gana da ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun guda biyar, a wani…
Read More
2027: IGP Disu ya yi alƙawarin ’yan Nijeriya za su yi alfahari da ’yan sanda

2027: IGP Disu ya yi alƙawarin ’yan Nijeriya za su yi alfahari da ’yan sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa yadda jami’an ’yan sanda za su gudanar da ayyukansu kafin zaɓen 2027, lokacin zaɓen da kuma bayan kammala shi, zai sa al’umma su yi alfahari da rundunar ’yan sandan ƙasar. Disu ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin ’yan jarida bayan ƙaddamar da wani littafi mai suna The Origin of Women in Nigeria Police Force, wanda Dame Stella Okuyiga, mai shekara 96 kuma tsohuwar Mataimakiyar Kwamishinan ’Yan Sanda mai ritaya, ta rubuta. Okuyiga na cikin mata 20 na farko da suka…
Read More
2027: Dole INEC ta tashi tsaye wajen yaƙi da labaran ƙarya na AI

2027: Dole INEC ta tashi tsaye wajen yaƙi da labaran ƙarya na AI

Yayin da ’yan Nijeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, barazanar tashin hankali da ka iya biyo bayan yaɗa labaran ƙarya ta sa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yin kira ga masu zaɓe da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da bin doka da oda a lokacin zaɓe da kuma bayansa. A zaman Majalisar Dattawa na makon da ya gabata, shugaban majalisar dattawan ƙasar ya gargaɗi ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga sahihancin sakamakon zaɓe, musamman a…
Read More
Ƙungiyar ma’aikatan lafiya sun tsunduma yajin aikin gargaɗi a Katsina

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya sun tsunduma yajin aikin gargaɗi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta jihar Katsina, wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin MHWHUN, NANМN da NUAHP, ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon kwanaki bakwai, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin jihar wajen magance buƙatunta. A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Comrade Ibrahim A. Balange, ta ce ta riga ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki bakwai a hanyar aikewa da wasiƙa. Sai dai ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cikar wa’adin da kuma damar da aka bai wa gwamnati domin warware matsalolin,…
Read More
Mu na da yaƙinin cewa INEC za ta dawo da sunan Gwarzo cikin ’yan takarar gwamnan Kano – NDC

Mu na da yaƙinin cewa INEC za ta dawo da sunan Gwarzo cikin ’yan takarar gwamnan Kano – NDC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano u Jam’iyyar NDC a Jihar Kano ta bayyana fatan cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta dawo da sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa cikin jerin ’yan takarar zaɓen gwamnan jihar na 2027, idan aka gano cewa kuskure ne aka yi wajen cire sunayensu. Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ne ya bayyana hakan ranar Aluhamisu, inda ya ce jam’iyyar ta kai ƙorafinta ga uwar jam’iyya ta ƙasa, wadda ita ma ta miƙa batun ga INEC. Kazalika, Mai Riga ya ce hukumar zaɓen ta…
Read More
Tawagar Garry na shakkun cancantar Pantami na PDP a Gombe

Tawagar Garry na shakkun cancantar Pantami na PDP a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Rikicin shari’a kan tikitin takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP ya sake ɗaukar sabon salo, bayan lauyoyin da ke wakiltar mai neman takarar gwamna, Hon. Usman Aliyu Garry, sun shigar da ƙorafi ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), suna ƙalubalantar cancantar jam’iyyar ta tsayar da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takararta a zaɓen 2027. A cikin wata wasiƙa da suka aika wa shugaban INEC, lauyoyin Garry sun nuna damuwa kan ko PDP ta bi ƙa’idojin doka da suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu da kuma tsayar da ’yan takara…
Read More