ukarofi

11670 Posts
Kungiyar ɗaliban Nijeriya ga Atiku: Dawo da tallafin fetur babbar matsala ne

Kungiyar ɗaliban Nijeriya ga Atiku: Dawo da tallafin fetur babbar matsala ne

*Ba mu da alaƙa da siyasa, inji Shugaban NAN Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar ɗaliban Nijeriya ta ƙasa (NANS) ta soki ƙudirin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa, hakan na iya sake jefa ƙasar cikin irin matsalolin tattalin arziki da tsarin tallafin ya haifar a baya ko ma fiye. Shugaban NANS na ƙasa, Kwamared Akinteye Babatunde Afeez, ya ce, matsayar ƙungiyar ba ta da alaƙa da siyasa, sai dai ta samo asali ne daga abin da take ganin shine masalahar ƙasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya,…
Read More
Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, ya rasu jiya

Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, ya rasu jiya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamred Emmanuel Ugboaja, ya rasu yana da shekaru 60 bayan fama da doguwar jinya. An bayyana rasuwar Ugboaja ne a jiya Alhamis, yayin da Majalisar Zartarwa ta ƙasa ta NLC ke gudanar da taro a Enugu. Rahotanni sun ce, Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero, ne ya sanar da mambobin majalisar labarin rasuwar bayan iyalan marigayin sun aika da wasiƙar sanarwar rasuwar. Kwamred Ugboaja, wanda ƙwararren lauya ne kuma gogaggen ɗan ƙungiyar ƙwadago, ya zama Babban Sakataren NLC na biyar a watan Agustan 2019, inda ya gaji Peter Ozo-Eson. Ya…
Read More
Asabar za a gabatar da littafin ‘Tambarin Zamani’ na matashiya Salma Mailambu

Asabar za a gabatar da littafin ‘Tambarin Zamani’ na matashiya Salma Mailambu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Ya zuwa yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa na babban taron gabatar da littafin waƙoƙi mai suna ‘Tambarin Zamani’, wanda matashiyar mawaƙiya, Salma Saeed Mailambu, ta rubuta. Za a gudanar da taron ne a gobe Asabar 29 ga Agusta a ɗakin taro na gidan Mambayya dake Unguwar Gwammaja a cikin birnin Kano. Ana sa ran zai samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman malamai da ɗalibai da masu nazarin waƙoƙi da al'adun gargajiyar Hausa. Littafin Tambarin Zamani dai wasu waƙoƙi ne daga cikin fitattun waƙoƙin Salma Saeed Mailambu guda 20 aka…
Read More
Bauchi: Harin ramuwar gayya ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya a Gamawa

Bauchi: Harin ramuwar gayya ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya a Gamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu mutane shida suka samu raunuka sakamakon wani rikici tsakanin matasan garuruwan Buskuwa da Mabani da ke ƙaramar Hukumar Gamawa a Jihar Bauchi. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta fara bincike kan lamarin, tare da kama wani mutum da ake zargi da hannu a rikicin. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Alhamis, ya ce ’yan sanda sun samu rahoton lamarin ne ranar Laraba daga wani mazaunin ƙauyen Buskuwa mai shekaru 55. Ya ce rikicin ya samo asali ne…
Read More
Tallafin mai: Atiku na rikitar da ’yan Nijeriya — Fadar Shugaban ƙasa

Tallafin mai: Atiku na rikitar da ’yan Nijeriya — Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da bayar da bayanai masu karo da juna kan shirinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban ƙasa a 2027. Aminiya Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce Atiku da mataimakansa sun bayar da bayanai daban-daban kan yadda shirin dawo da tallafin zai kasance cikin mako guda. A cewar Onanuga, mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya fara cewa gwamnatin Atiku za ta dawo da tallafin…
Read More
NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa N1,270 duk da rangwamen Dangote na kai kaya kyauta

NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa N1,270 duk da rangwamen Dangote na kai kaya kyauta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya ƙara farashin litar man fetur (PMS) daga N1,250 zuwa N1,270 a gidajen mai na kamfanin da ke Abuja da kewaye. ƙarin N20 ya zo ne duk da shirin matatar Dangote na raba fetur ba tare da kuɗin jigilar kaya ba zuwa wasu wurare 10 a Nijeriya, ciki har da Abuja, inda ake sayar da litar kan N1,185. Wani binciken kasuwa da aka gudanar a Abuja ya nuna cewa farashin fetur ya bambanta daga gidan mai zuwa wani, inda ake sayar da litar tsakanin N1,230 da N1,299.…
Read More
Katsina: Rashin jituwa ta ɓarke tsakanin Raɗɗa da Masari hadimin Shugaban ƙasa

Katsina: Rashin jituwa ta ɓarke tsakanin Raɗɗa da Masari hadimin Shugaban ƙasa

Daga UMAR GARBA a Katsina Rashin jituwa da ke tsakanin Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da Hadimin Shugaban ƙasa, Ibrahim Masari, ya sa aka gayyaci jami’an tsaron Gwamna Radda zuwa Abuja. Rikicin ya fara ne bayan da wasu matasa suka rushe wani babban allon siyasa da ke ɗauke da hoton Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Rahotanni sun bayyana cewa matasa ’yan bangar siyasa sun lalata allon sakamakon an sanya ɗan ƙaramin hoton Gwamna Radda, amma an sanya manya-manyan hotunan Shugaba Tinubu da kuma mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari. An yi zargin cewa jami’an tsaron Gwamnan…
Read More
Mauludi: Lokaci ne na jaddada aiki da koyarwar Annabi Muhammad –  Idris

Mauludi: Lokaci ne na jaddada aiki da koyarwar Annabi Muhammad –  Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi riƙo da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman wajen kyautatawa, zaman lafiya, haƙuri, adalci da haɗin kai. Idris ya bayyana hakan ne a saƙonsa na taya Musulmi murnar zagayowar Maulidin Annabi Muhammad (SAW), inda ya ce bikin wata dama ce ta tunawa da kyawawan halaye da koyarwar Manzon Allah. Ya ce waɗannan halaye suna da muhimmanci musamman a lokacin da Nijeriya ke fuskantar sauye-sauyen tattalin arziki da sauran ƙalubale. Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin jagorancin…
Read More
Yadda gagarumin mauludin Manzon Allah na Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani ya ƙayatar a Kaduna

Yadda gagarumin mauludin Manzon Allah na Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani ya ƙayatar a Kaduna

Daga ZAHARADDEEN ILIYASU a Kaduna Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ta gudanar da gagarumin taron Maulidin Manzon Allah (SAW) na watan Rabi’ul-Awwal na shekarar 1448/2026 a Kaduna, inda aka shafe tsawon dare ana gudanar da ibadu da shirye-shirye daban-daban domin ƙarfafa soyayya ga Manzon Allah (SAW) da kuma koyarwarsa. Taron ya ƙunshi karatun Alƙur’ani, zikiri, rera yabo da salati ga Manzon Allah (SAW), gaisuwar sada zumunci, rabon kyaututtuka da takardun shaidar kammala haddace wasu littattafai, tare da gudanar da addu’o’i na musamman a ƙarshen taron. A yayin taron, babban Shehin Zawiyyar, Shehu Isma’ila Umar Almaddah, ya gabatar da dogon…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Dala ya yaba wa Malami mai nama kan samar wa matasa ayyukan yi

Shugaban ƙaramar hukumar Dala ya yaba wa Malami mai nama kan samar wa matasa ayyukan yi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Surajo Imam, ya yaba da ƙoƙarin fitaccen ɗan kasuwar gasashen naman rago, Alhaji Malami Mai Nama, wajen samar wa matasa ayyukan yi da kuma bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Kano. Surajo Imam ya bayyana hakan ne a wajen buɗe wani sabon katafaren wajen sayar da gasashen naman rago na Alhaji Malami Mai Nama, da ke kan Titin Ibrahim Taiwo a Kano, ranar Laraba. Ya ce kasuwanci na ci gaba da bunƙasa a Jihar Kano, yana mai cewa Alhaji Malami ya fara sana’ar ne da tallan nama a kwano, kafin daga…
Read More