16
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa ta cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen waɗanda za su fafata a zaɓen 2027 saboda jam’iyyunsu sun gaza miƙa rajistar mambobinsu kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada. INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, inda ta ce ta ɗauki matakin ne bisa hukuncin Kotun ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya tabbatar da cewa wajibi ne dukkan jam’iyyun siyasa su miƙa rajistar mambobinsu kafin gudanar da sahihin zaɓen fitar da…
