Ba mu ci bashin N14.26bn ba — Gwamnatin Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Dauda Lawal ta bayyana cewa, ba ta ci bashin Naira biliyan 14.26 ba, amma cewa abin da ake gani yanzu ɓangare ne na bashin biliyan N20 da gwamnatin da ta gabata ta ranto.

Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa a sanar da ya fitar cewa babu wani bashi da jihar ta ci, a gida ko ƙetate, tun bayan da Gwamna Dauda Lawal ya karɓi ragamar mulkin jihar.

Ya ce, “Za mu so mu yi ƙarin haske kan rahoton Ofishin Kula da Bashi (DMO), Jihar Zamfara ba ta ci bashin biliyan N14.26 ba.

“Zamfara ba ta taɓa rubutawa tana neman bashi ba, haka ma ba ta taɓa kusantar Majalisar Jihar ko ta Taryya da buƙatar hakan ba.

“Yana da kyau a fahimci cewa, gwamnatin Zamfara da ta gabata ce ta kinkimi bashin biliyan N20 amma ta gagara karɓar kuɗaɗen baki ɗaya a wancan lokaci.

“Gwamnatin baya-bayan da ta gabata ta karɓi biliyan N4 daga biliyan N20 ɗin da waccan gwamnatin ta nema don aikin gina babban filin jirgin saman Zamfara, kodayake ba a yi amfani da kuɗaɗen ba.

“Bayan da muka shiga ofis ne muka fahimci cewa sharuɗɗan da aka gindaya a lokacin karɓar bashin sun hana dakatar da karɓar bashin ba tare da jihar ta tafka asara ba.

“Ragowar biliyan N16 daga biliyan N20 da jihar ta ranta a wancan lokaci shi ne biliyan N14.26 da DMO ke batu a kai.

“Har yanzu ragowar kuɗin na cikin asusun gwamnati ba a yi amfani da shi ba, za a adana shi don aikin filin jirgin sama,” in ji sanarwar.