Ba za a soke sakamakon zaɓe ba, inji Shugaban INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shawarci jam’iyyun siyasa da ke ƙorafi da su nemi haƙƙinsu a kotu idan ba su gamsu da yadda zaɓen ke gudana ba, inda ta ƙara da cewa kiraye-kirayen da wasu jam’iyyu ke yi kan shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya yi murabus bai dace ba.

Idan dai ba a manta ba a ranar Litinin ne wakilan jam’iyyar PDP, Dino Melaye da Emeka Ihedioha suka fice daga babban taron INEC na ƙasa da ke Abuja bisa zargin tafka maguɗi a zaɓe.

Wakilan wasu jam’iyyu, ciki har da na SDP, LP da ADP, sun tsaya akan ra’ayi iri ɗaya.

Sun zargi INEC da karya dokar zaɓe ta hanyar ci gaba da tattara sakamakon zaɓe tare da sanar da sakamakon zaɓen duk da cewa ba a sanya sakamakon a manhajar duba sakamakon INEC ba.

Da yake jawabi a ranar Talata, babban sakataren yaɗa labarai na shugaban hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce “sakamakon da ke fitowa daga jihohi na nuni da tsari na gaskiya.”

Sai dai ya buƙaci jam’iyyun da su ba da damar kammala faɗin sakamakon, idan kuma ba su gamsu ba za su iya zuwa kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *