Bayan cire tallafin mai, me ya kamata Tinubu ya yi?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani bidiyo da ke nuna yadda wasu jami’an Hukumar Kula Da Shigi Da Fice ta ƙasa suke buɗe wata ƙofa da ke kan iyakar Nijeriya, ya ɗauki hankalin ‘yan Nijeriya a cikin wannan mako mai ƙarewa. A cikin bidiyon an ji sautin wasu mutane da ke magana cikin harshen Turanci suna nuna murna da sake buɗe iyakokin Nijeriya.

Ko da yake bincike ya nuna wannan bidiyo tsohon ɗauka ne tun cikin shekarar 2020, amma me ya sa aka sake fitar da shi a wannan lokaci da sabuwar gwamnati ke ƙoƙarin daidaita zamanta? Shin ‘yan Nijeriya ba su san iyakokin ƙasar nan sun daɗe a buɗe ba ne?

Wannan ya tuno min da wani mutum da na gani ana hira da shi a labarai, yana bayani kan fatansa ga sabuwar gwamnati. Abin mamaki sai na ji yana roƙon sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya buɗe iyakokin Nijeriya, don a samu a cigaba da hada-hadar kasuwanci ta ƙasa da ƙasa.

To, kenan wannan na nufin talakawan Nijeriya ba su san da an daɗe da buɗe boda ba ne, ko kuwa dai halin ƙuncin da ake ciki ne, wanda a baya aka danganta shi da matsalar rufe iyakokin ƙasa da rashin shigo da kayan abinci daga waje, har yanzu yake dukan ‘yan ƙasa?

Bincike ya nunar da cewa, tsohuwar gwamnatin da ta gabata, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ita ce ta ba da umurnin rufe iyakokin ƙasar nan a cikin watan Agusta na shekarar 2019, don daƙile ayyukan fasa-ƙwaurin kayan abinci, musamman shinkafa, da masu safarar shigo da makamai don ayyukan ta’addanci a cikin ƙasa.

Wannan a cewar tsohuwar gwamnati zai taimaka wajen inganta masana’antu na cikin gida, ƙarfafa gwiwar manoma da samar da wadatar abinci a cikin ƙasa. A sakamakon haka an fuskanci tashin farashin kayan masarufi musamman shinkafa, wanda hakan ya sa rayuwar ‘yan Nijeriya ta shiga matsanancin yanayi. Manyan ‘yan kasuwa da qanana suka fuskanci matsalar durƙushewa.

Yayin da manoman shinkafa a cikin ƙasa suka mayar da hankali wajen noma da samun riba mai yawa saboda hana shigo da shinkafar waje, sai dai wacce ake fasa-ƙwaurinta a voye.

Sai dai a sakamakon koke-koke da shawarwarin masana tattalin arziki gwamnatin tarayya ta ba da umarnin buɗe wasu iyakokin da aka kulle a ranar 16 ga watan Disamba na shekarar 2020, waɗanda suka haɗa da bodar Nijeriya da ke Idoroko a Jihar Ogun.

Wacce lokacin buɗe ta ne aka ɗauki wancan bidiyo da na yi magana a farkon wannan sharhi. Sai kuma bodar Nijeriya da ke Jibiya a Jihar Katsina, da bodar Kamba a Jihar Kebbi, da kuma wacce ke Ikom a Jihar Kuros Riba.

Daga bisani kuma shugaban ƙasa na wancan lokacin, a ranar 22 ga watan Afrilu na shekarar 2022 ya ba da umarnin sake rufe bodar Ikom, yayin da aka canza ta da bodar Ikang duk dai a Jihar Kuros Riba, sakamakon wasu dalilai na tsaro.

Tun daga sannan manyan iyakokin Nijeriya sun cigaba da kasancewa a buɗe, in ban da ƙananan fiye da 30 da har yanzu ba a buɗe ba, musamman waɗanda ke kan iyakar ƙasashen Kamaru da Chadi, saboda wasu dalilai masu nasaba da tsaro.

Masanin harkokin kasuwanci kuma mamba a Hukumar Kula Da Babbar Kasuwar Abuja, Sa’in Gamji, Isma’il Aliyu Entifa ya bayyana cewa, rufe iyakokin ƙasa da gwamnati ta yi a wancan lokacin ya yi tasiri sosai a harkokin kasuwanci, da cigaban masana’antu, musamman ma ƙananan masana’antu da ake da su a Nijeriya waɗanda ke fitar da kayayyakin da suke sarrafawa zuwa maƙwabtan ƙasashe.

Kuma rufewar ta shafi matasa da dama da ke gudanar da ayyukan su a waɗannan masana’antu suna samun abin dogaro da kai. Sannan kuma an samu koma baya wajen samun kuɗaɗen shiga da ake samu daga cinikayyana ƙasa da ƙasa.

Buɗe iyakokin ƙasa da cigaba da hada-hadar kasuwanci babban cigaba ne, ba kawai ga gwamnati ba, har ma da masu masana’antu na cikin gida. Domin ba da damar shigo da kayayyakin da ake sarrafawa a waje, zai ƙara wa na gida ƙwarin gwiwar inganta nasu, don su yi kafaɗa da kafaɗa da na sauran sassan duniya.

Kamar yadda aka samu cigaba ta fuskar kafa kamfanonin casar shinkafa a cikin ƙasa, yanzu dama ce da manoman mu da masu masana’antu za su ƙara inganta yadda suke gyara shinkafar da ake fitarwa kasuwanni, domin ya dace da yadda kamfanonin ƙasashen waje suke gyara nasu. Sannan idan kayan abinci ya wadata a kasuwanni zai kawo raguwar farashi, yadda talaka zai samu sauƙin sayen kayan masarufi da kula da iyalinsa.

Yanzu da hankalin ‘yan Nijeriya ya tashi daga kan batun buɗe iyakokin ƙasa zuwa ga batun soke cigaba ba da tallafin man fetur, da kuma ƙarin farashin litar mai da ya jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali, saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi da kuɗaɗen sufuri suka yi. Kallo ya koma kan yadda sabuwar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu za ta shawo kan lamarin.

Duk da kasancewar gwamnatin ta samu damar shawo kan ƙungiyoyin ma’aikata da na ‘yan kasuwa da suka yi barazanar tafiya yajin aiki na qasa baki ɗaya, har sai gwamnati ta canza ƙudirinta. Yadda sabon shugaban ƙasa zai tunkari lamarin ta hanyar da samar wasu dabaru na sassauta halin da talakawan ƙasa suka shiga.

Ƙungiyoyin ‘yan ƙwadago dai na buƙatar a ƙara wa ma’aikata albashi, kuma a daina ɓullo da tsare tsaren da za su ƙara wa talakawa da ƙananan ma’aikata wahala da ƙunci. A rage ɓarnar dukiyar talakawa wajen tafiyar da harkokin gwamnati, da almubazzarancin da ake yi a matakan gwamnati daban-daban. Wannan kuma ya zo daidai da shawarwarin da wani ƙwararre kan tattalin arziki, kuma malami a Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe, Dr Isa Abdullahi ya bayar dangane da yadda gwamnatin tarayya za ta shawo kan matsalolin tattalin arziki da za a fuskanta sakamakon janye tallafin mai da ƙarin farashin mai da ta yi.

Dr Isa Abdullahi ya ɗora alhakin rashin samun ciniki da faɗuwar kasuwar man fetur a akasarin gidajen man fetur na ƙasar nan, kan tsadar farashin litar man fetur da aka samu. Ya bayyana cewa, an samu raguwar masu sayen man fetur da kimanin kaso 40 cikin ɗari, idan aka kwatanta da watannin baya, kafin janye tallafi. Jama’a ba sa iya zuwa sayen man fetur sosai kamar da, kuma ko sayen za a yi ba a sayen lita da yawa, saboda tsadar rayuwa da rashin kuɗaɗe a hannun jama’a.

A cewarsa, dole idan gwamnati tana son ta kawo sassauci kan wannan matsalar da ‘yan Nijeriya suka sake fuskanta, sai ta yi amfani da kuɗaɗen tallafin da ta ce ta janye zuwa ga yadda zai yi tasiri a rayuwar talakawa, ya inganta rayuwarsu. A samar da tallafin sana’o’i ga marasa ƙarfi ta yadda masu ƙananan kasuwanci za su farfaɗo, matasa su samu ayyukan yi. Gwamnati ta farfaɗo da masana’antu da za su riƙa samar da ayyukan yi ga matasa.

Gwamnati ta fitar da dokar sauke farashin kayan masarufi zuwa yadda talaka ba zai yi fargabar shiga kasuwa ba. A basu tallafin ilimi, da lafiya, ya zama yaran talakawa da sauran ‘yan ƙasa za su yi karatu a dukkan matakan ilimi kyauta ko a biya kuɗin da bai taka kara ya karya ba.

Kuma abin da za a nemi su biya idan sun je asibitoci neman lafiya, musamman asibitocin gwamnati bai wuce ɗan abin da kowa zai iya ba, ba tare da ya ƙuntata ba. Wannan zai taimaka a samu sauƙin rayuwa, yadda ƙarin farashin mai ba zai jefa shi cikin ƙunci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *