19
May
Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kaduna (KAEDCO) yana fuskantar barazanar rasa lasisin gudanar da kamfanonin saboda bashin Naira biliyan 51.93. Kamfanin KAEDCO ya amshi sanarwa daga hukumar kula da ƙa'idojin wutar Lantarki (NERC) a ranar Litinin xin da ta gabata. Inda ake umartar Bankin game da niyyar NERC na soke lasisinsa na gudanarwa. Wasu rahotanni da suka bayyana a ranar Talatar da ta gabata sun bayyana cewa, KAEDCO ta tara wa kanta bashin Naira biliyan 41.49 a tsakanin shekaru 2015 zuwa 2021, wanda Hukumar rarraba wutar ta Nijeriya a kan sari (NBET) da MO suka…
