Kasuwanci

AMPAT ta nemi majalisar Kano ta zartar da doka mai tsanani kan masu kwacen waya

AMPAT ta nemi majalisar Kano ta zartar da doka mai tsanani kan masu kwacen waya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ƙungiyar Masu Hada-hadar Wayoyin Hannu ta Jihar Kano (AMPAT), ta yi kira ga majalisar jihar da su samar da doka mai tsanani da za ta riƙa hukunta masu kwacen waya a Kano. Kakakin ƙungiyar, Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ne ya yi wannan kiran. Ya yi nuni da cewa rashin tsatsauran matakin hukunci na doka na taimakawa wajen ta'azzarar kwacen wayoyin da ɓata gari suke. Ya ce, masu kwacen wayar sukan yi sanadin lahanta mutane da jawo asarar rayuka wanda mummunar ta'adar tasu ba shi da maraba da fashi da makami. Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ya…
Read More
Mene ne gaskiyar batun dakatar da Opay da Palmpay?

Mene ne gaskiyar batun dakatar da Opay da Palmpay?

Assalam alaikum. Kamar yadda muka sani, mutane na ta yaɗa jita-jitar cewa wai CBN na shirin dakatar da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta internet; Opay da Palmpay, amma Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi ƙarin haske kan waɗannan jita-jita. Babban Bankin ya musanta waɗannan rahotannin inda ya bayyana su a matsayin ƙarya ce tsagwaronta. A cewar rahoto, Daraktan wucin gadi na fannin watsa labarai na Babban Bankin, Mista Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyana hakan 2023, a birnin tarayya Abuja, inda ya ce labarin ƙanzon kurege ne kawai. Rahotannin da aka yi ta yaɗawa waɗanda aka ce sun fito daga bakin…
Read More
CBN zai rufe asusun bankin da ba a haɗa su da BVN ba

CBN zai rufe asusun bankin da ba a haɗa su da BVN ba

Daga AMINA YUSUFU ALI A halin yanzu Babban Bankin Nijeriya, CBN ya shirya tsaf don ganin ya rufe asususn bankunan da ba a haɗa musu BVN a jikinsu ba. Wannan wani mataki ne da suka ɗauka don ganin an rage zambar intanet a bankuna. Blaise Ijebor, Daraktan sashen kula da tsautsayi na CBN shi ya yi yi wannan sanarwar a taron shan ruwa da aka gabatar a ranar alhamis ɗin da ta gabata. Ijebor ya bayyana cewa, mazambatan intanet suna amfani da hanyoyi da dama wajen damfarar asusun da ba haɗa shi da BVN ba. Wanda yake sauƙaƙa musu zambar…
Read More
Rikicin kamfanin Seplat: kotu ta ba da umarnin Brown ya koma bakin aiki amma har yanzu an dakatar da shi a Nijeriya

Rikicin kamfanin Seplat: kotu ta ba da umarnin Brown ya koma bakin aiki amma har yanzu an dakatar da shi a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Wata kotun Tarayya a jihar Legas ta janye batun umarnin da aka bayar ga shugaban zartarwa na kamfanin Seplat Energy, Roger Brown a kan ya koma bakin aikinsa. Rahotanni sun bayyana cewa, mako huɗu da suka wuce kotun ta ba da umarnin sanya takunkumi ga Brown game da ya bar cigaba da kula da al'amuran shugabancin kamfanin. Inda aka sallame shi daga muƙaminsa. An ba wa Brown odar sauka daga muƙaminsa ne bayan masu ruwa da tsaki guda biyar daga kamfanin na Seplat sun zarge shi da wariyar launin fata da azabtar da 'yan Nijeriya ma'aikatan…
Read More
Duk da wadatar takardun Naira masu POS na cajin wuce hankali

Duk da wadatar takardun Naira masu POS na cajin wuce hankali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu masu sana'ar POS su na cigaba da cajin abokan cinki fiye da kima duk da wadatar takardun Naira a Nijeriya. An gano cewa wasu masu POS a Babban Birnin Tarayya, FCT, na caji tsakanin Naira 300 zuwa N200 kan Naira 5,000 da aka cire. Romanus Chukwu, wani abokin ciniki da aka gani a ɗaya daga cikin wuraren da ke Nyanya, ya ce, har yanzu cajin yana da yawa idan aka kwatanta da lokacin da takardun kuɗi suka yi ƙaranci. Chukwu ya yi kira ga masu sana'ar da su koma karɓar Naira 100 da aka saba…
Read More
Mun gamsu da jagorancin shugabannin Kasuwar Mile-12 a Legas

Mun gamsu da jagorancin shugabannin Kasuwar Mile-12 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Wani ɗan kasuwar gwari dake Kasuwar Mile-12 a cikin garin Legas, Alhaji Auwalu na Ubanliba kuma mai bai wa shugaban kulawa da cigaban kasuwanci ɓangaren tumatiri shawara ta musamman, Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano, ya bayyana cewar shi da sauran al'ummar kasuwar suna cigaba da gamsuwa tare da amincewa da jagorancin shuwagabanni kasuwar gaba ɗaya. Alhaji Auwalu na Ubanliba ya yi wannan tsokacin ne a kasuwar Mile-12 a lokacin da yake zantawa da Jaridar Manhaja a Legas dangane da harkokin kasuwancin tumatiri a kasuwar, inda na Ubanliba ya cigaba da cewa haqiqa Abdulgiyasu Sani Rano yana…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Balogun da ke Legas

Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Balogun da ke Legas

Da safiyar Talata aka samu aukuwar gobara a kasuwar wadda ta laƙume wani sashe na kasuwar. Jaridar Premium Times ta rawaito cewar gobarar ta tashi ne a sashen da galibi takalman mata ake sayarwa. Da yake tabbatar da aukuwar iftila'in, hadimin Gwamnan Legas kan harkokin yaɗa labarai, Jubril Gawat, ya ce jami'an kwana-kwana sun dira kasuwar domin kashe gobarar. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu ƙarin bayani a hukumance game da abin da ya haddasa gobarar da kuma asarar da aka tafka a dalilin gobara.
Read More
CBN ya umarci bankuna su fito aiki ranakun ƙarshen mako

CBN ya umarci bankuna su fito aiki ranakun ƙarshen mako

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna da su ƙara kwanakin aikinsu zuwa Asabar da Lahadi. CBN ya ce ya yanke hakan ne domin tabbatar da wadatar kuɗi a bankuna don amfanin jama'a. Bankin ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a ta bakin Daraktansa, wato Isa AbdulMumin. Sanarwar ta ce tuni CBN ya fara tura kuɗaɗe zuwa bankuna a sassan ƙasa baki ɗaya. “CBN ya ba da umarnin bankuna su loda kuɗi a cikin na'urorin ATM, sannan su ci gaba da aiki har da ranakun karshen mako. “Bankuna za su yi aiki a…
Read More
Gobara ta ƙara lamushe shahararriyar kasuwa a Borno

Gobara ta ƙara lamushe shahararriyar kasuwa a Borno

Daga AMINA YUSUF ALI Gobara ta lamushe wata kasuwa da ake kira Gamboru a cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Kasuwar Gamboru ita ce kasuwar sayar da kayan gwari mafi girma a garin Maiduguri. Ya zuwa haɗa wannan labari ba a san musabbabin gobarar ba, amma majiyarmu ta bayyana cewa, an rasa dukiya ta ɗaruruwan miliyoyin Nairori. Gobarar ta afku ne bayan ɓarkewar wata gobarar daban a sassafiyar Asabar ɗin a kasuwar Biu da ke a Kudancin jihar Borno.
Read More
CBN ya bai wa bankuna odar ci gaba da karɓar tsoffin kuɗi

CBN ya bai wa bankuna odar ci gaba da karɓar tsoffin kuɗi

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ba da umarnin bankuna su ci gaba da karɓa da kuma ba da tsoffin tarkadun kuɗi na N200 da N500 da N1000 har zuwa 31 ga Disamban 2023. CBN ya amince da hakan ne domin cika umarnin Kotun Ƙoli biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke ran 3 Maris inda ta buƙaci da a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin har zuwa ƙarshen wannan shekarar. Muƙaddashin Daraktan Sadarwa na bankin, Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyna amincewar CBN na ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin a sanarwar da ya fitar…
Read More