Mene ne gaskiyar batun dakatar da Opay da Palmpay?

Assalam alaikum. Kamar yadda muka sani, mutane na ta yaɗa jita-jitar cewa wai CBN na shirin dakatar da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta internet; Opay da Palmpay, amma Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi ƙarin haske kan waɗannan jita-jita.

Babban Bankin ya musanta waɗannan rahotannin inda ya bayyana su a matsayin ƙarya ce tsagwaronta.

A cewar rahoto, Daraktan wucin gadi na fannin watsa labarai na Babban Bankin, Mista Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyana hakan 2023, a birnin tarayya Abuja, inda ya ce labarin ƙanzon kurege ne kawai.

Rahotannin da aka yi ta yaɗawa waɗanda aka ce sun fito daga bakin AbdulMumin, sun yi ikirarin cewa CBN zai dakatar da asusun kamfanonin ne saboda ana yin amfani da su wajen aikata zamba.

Wani ɓangare na labarin na cewa, “Idan ka san kana amfani da OPAY, PALMPAY ko ɗaya daga cikin CHINA APPs ko POS ɗin su, ka daina ajiye manyan kuɗi a ciki ko kuma ka daina amfani da su.”

“CBN na daf da dakatar da asusun su saboda ana amfani da su wajen aikata zamba.”

Opay da Palmpay dai sun fito sun ƙaryata waɗannan labaran inda suka ce sam CBN ba ta bincikarsu kan aikata wani rashin gaskiya.

Ya kamata mutane mu yi watsi da irin waɗannan batu.

Daga Muhammad Awwal, 08062327373