Kasuwanci

Gobara ta lamushe wani ɓangare na Kasuwar Balogun ta Legas

Gobara ta lamushe wani ɓangare na Kasuwar Balogun ta Legas

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka yi wata gobara da ta lamushe shaguna da dama a kasuwar Balogun dake kan titin Martins Street a jihar Legas. Hotunan wannan ƙazamar gobarar da ta farmaki wani sashe na babbar kasuwar suna ta yawo a kafafen yanar gizo da yadda gabarar ta dinga ci ganga-ganga tana jawo asara. Jami'in kula da abokan hulda na Hukumar kashe gobara ta Legas yayin wata zantawar manema labarai da shi a wayar tarho a lokacin da gobarar take cigaba da ruruwa ya ba da tabbacin cewa, hukumar tana iya bakin…
Read More
Buhari ya ba da umarnin buɗe kamfanin simintin Ɗangote da ke Obajana

Buhari ya ba da umarnin buɗe kamfanin simintin Ɗangote da ke Obajana

Daga BASHIR ISAH Shugaba Buhari ya ba da umarnin a gaggauta buɗe masana’antar simintin nan ta Ɗangote da ke Obajana, Jihar Kogi. Gwamnati ta ba da umarnin haka ne a taron Majalisar Tsaro da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari ranar Juma'a. Bayanin sake buɗe masana'antar ya fito ne daga bakin Ministan Harkokin ’Yan sanda, Mohammed Dingyadi da takwaransa na Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola da kuma Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor yayin da suke yi wa manema labarai jawabi jim kaɗan bayan taron. Aregbesola ya ce, an cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Jihar Kogi da…
Read More
Amai da lashewa: Musk ya sake zawarcin sayen Kamfanin manhajar Tiwita

Amai da lashewa: Musk ya sake zawarcin sayen Kamfanin manhajar Tiwita

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai Biloniya, kuma attajiri mafi kuɗi a Duniya, Elon Musk ya sake waiwayar maganar sayen Kamfanin manhajar Soshiyal midiyar nan ta Tiwita.Musk ya yi wanna batu mai kama da amai da lashewa ne a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda jaridar Reuters ta rawaito. A kwanakin baya dai idan ba mu manta ba, Attajirin ya so ya sayi kamfanin na Tiwita, a kan farashin Dalar Amurka biliyan $44. Inda daga baya kuma ana tsaka da cinikin kuma muka ji Attajirin ya sake bayyana cewa, ya fasa sayen Kamfanin saboda wasu abubuwa masu…
Read More
Anya CBN zai iya farfaɗo da darajar Naira da ƙarin kaso 15.5% na kuɗin ruwa?

Anya CBN zai iya farfaɗo da darajar Naira da ƙarin kaso 15.5% na kuɗin ruwa?

Daga AMINA YUSUF ALI Kwamitin harkokin kuɗi na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yanke shawarar ɗaga darajar kuɗin ruwansa da kaso 15.5%. Kwamitin ya yanke wannan shawarar ne a ranar Talatar da ta gabata. Kuma ya yanke wannan hukunci ne, saboda a ceto Naira daga rugurgujewar da take ta fama a 'yan kwanakin nan, abinda suke sa ran zai ƙaro sassauci ga 'yan Nijeriya ta fuskar haɓakar tattalin arziki da kuma sauki a farashin kaya. Amma abin tambayar a nan shi ne, shin wannan mataki da CBN ya ɗauka zai kai ga kwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa? Jaridar ta…
Read More
FIRS ta gargaɗi hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan katsalandan a harkar haraji

FIRS ta gargaɗi hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan katsalandan a harkar haraji

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tattara haraji ta Nijeriya (FIRS) ta gargaɗi hukumomin gwamnati a kan tsoma baki a harkar haraji. Wato ɗora haraji, karɓar harajin da bibiyar waɗanda ba sa biyan harajin. Wannan jawabi dai ya fito daga shugaban zartarwa na hukumar FIRS, Mista Muhammad Nami. Kamar yadda yadda kamfanin dillancin labarai ya rawaito. Mista Nami ya ya yi ƙarin jan kunne ga hukumomi da ma'aikatun a kan yadda suke ɗaukar ma'aikatan da za su dinga karɓar harajin da gwamnatin tarayya take bin kamfanoni da mutane, masana'antu bankuna, da sauran cibiyoyin gudanar da kasuwanci ba bisa tsarin doka ba.…
Read More
Nijeriya ta maka Meta a kotu kan saɓa doka, ta nemi diyyar biliyan N30

Nijeriya ta maka Meta a kotu kan saɓa doka, ta nemi diyyar biliyan N30

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Nijeriya (ARON) ta maka kamfanin Meta, mamallakin Facebook da Instagram da kuma WhatsApp da abokin hulɗarsa AT3 Resources Limited, a wata Babbar Kotun Abuja. Cikin sanarwar da ta fitar ran Talata, ARCON ta ce rashin kiyaye dokar amfani da intanet wajen tallace-tallace ya sanya ta maka kamfanin a kotu. A cewar ARCON, tallace-tallacen da kamfanin Meta ke yaɗawa zuwa Nijeriya ta shafukasa na soshiyal midiya ba tare da kikaye ƙa'idojin da aka shimfiɗa ba hakan ya saɓa wa dokar talla ta Nijeriya. ARCON ta ce Meta na yaɗa tallace-tallacensa a Nijeriya ba…
Read More
Naira ta faɗo warwas zuwa 730 a Dala ɗaya

Naira ta faɗo warwas zuwa 730 a Dala ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Nairar Nijeriyar dai ta faɗo zuwa wani sabon matsayi, inda a safiyar Alhamis ɗin nan an sayar da Naira 730 a kasuwar ƙasa, wanda ya ragu da kashi 0.69 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata. Faɗuwar darajar canjin ta biyo bayan matakin da babban bankin ƙasar ya ɗauka na ɗaga darajar kuɗin ruwa zuwa sama da shekaru 20 sama da kashi 15.5 cikin ɗari, wanda ke nuna ƙaruwar kaso 150 daga kashi 14% da aka bayyana a taron MPC da ya gabata. Farashin da ya kai Naira 730 a dala shi ne mafi girma…
Read More
Matsin tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙara mafi ƙarancin albashi – Ministan Ƙwadago

Matsin tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙara mafi ƙarancin albashi – Ministan Ƙwadago

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, tana da shirin ƙarin ma fi ƙarancin albashi daga dubu 30 zuwa sama sakamakon matsin tattalin arzikin da ya addabi Duniya. Ministan Ƙwadago da ɗaukar aiki na Nijeriya, Dakta Chris Ngige, shi ya bayyana haka a taron bitar al'umma wanda ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya a Abuja. A cewar Ngige, dole gwamnatin ta duba wannan lamari saboda abinda yake faruwa na yanayin faɗuwar tattalin arziki a Duniya. Ya ƙara da cewa, wannan karyewar tattalin arzikin ta tava Duniya bakiɗaya.…
Read More
FIRS ta ƙaryata batun ta yafe wa wasu kamfanoni haraji

FIRS ta ƙaryata batun ta yafe wa wasu kamfanoni haraji

Daga AMINA YUSUF ALI Mista Muhammad Nami, shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa, (FIRS) ya bayyana cewa, babban aikin hukumar tasu shi ne tattara haraji ba wai su yafe haraji ga wa wani mahaluki mai biyan haraji ba. Mista Nami ya yi wannan bayani ne ranar Litinin ɗin da ta gabata a yayin da yake mayar da martani ga wani labaran da ya kira da ƙanzon kurege da suke ta yawo a kafafen yaɗa labarai a kan wai hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) ta yafe wa wasu kamfanoni haraji. Kamfanonin da aka rawaito cewa wai hukumar ta yafe wa…
Read More
Duniyar Ƙirifto Karansi: Yaushe pi za ta fashe ne? (2)

Duniyar Ƙirifto Karansi: Yaushe pi za ta fashe ne? (2)

Daga DANLADI Z. HARUNA Tun a farkon shekara ta 2020 ake ta hasashen za a soma aiki da Pi a matsayin kuɗin intanet, wannan ta sa wasu ɗaliban Malam Nikolas musamman na ƙasashen Asiya, suka yi awon gaba suke ta buɗe kantuna da sunan 'Pi Mall', inda aka ce suna saye da sayarwa ta amfani da kuɗin Pi. Da alama wannan abu yayi wa malamin daɗi, don haka ya ja wasu da dama cikin tsarin ta hanyar da ake kira 'Hackathon'. Sai dai ƙila hakan bai yi wa ɗaya daga waɗanda suka soma aikin daɗi ba. A watan Fabrairu na…
Read More