Anya CBN zai iya farfaɗo da darajar Naira da ƙarin kaso 15.5% na kuɗin ruwa?

Daga AMINA YUSUF ALI

Kwamitin harkokin kuɗi na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yanke shawarar ɗaga darajar kuɗin ruwansa da kaso 15.5%.

Kwamitin ya yanke wannan shawarar ne a ranar Talatar da ta gabata. Kuma ya yanke wannan hukunci ne, saboda a ceto Naira daga rugurgujewar da take ta fama a ‘yan kwanakin nan, abinda suke sa ran zai ƙaro sassauci ga ‘yan Nijeriya ta fuskar haɓakar tattalin arziki da kuma sauki a farashin kaya.

Amma abin tambayar a nan shi ne, shin wannan mataki da CBN ya ɗauka zai kai ga kwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa?

Jaridar ta Nairametrics ta rawaito cewa, a kwanakin baya ne wato a watan Nuwambar shekarar 2021 Naira ta ƙara shiga halin ha’ula’i bayan da bankin ajiya na tarayyar Amurka wanda shi ne takwaran CBN ya ba da sanarwar zai yi garambawul a kan tsare-tsaren ta na canjin kuɗi.

Wato gwari-gwari za ta kawo tsarin taka-tsan-tsan a kan lamarin canjin Dala da kuma qarin darajar kuɗin ruwa na bankunansu.

Kuma tabbas hakan aka yi. Amma a cewar rahoton Nairametrics, sam Nijeriya ba ta da wannan tsarin. Inda ta fi kauri shi ne, faɗa ba cikawa. A cewar sa ya kamata a ce tuntuni ta riga ta ɗauki irin wannan mataki. Amma sai dai a watan Mayun shekarar nan ta 2022 ta ƙara kuɗin ruwan da kaso 13, sai yanzu kuma da ta ƙara shi ya kai kaso 15.

Don haka a cewar rahoton, abinda ya kamata dai kawai wannan kwamitin sha’anin kudi na CBN ya kamata su ƙara ɗage damtse wajen gyara al’amura. Musamman duba da yadda yaƙin tsakanin ƙasashen Rasha da Yukiren yake qara girgiza tattalin arzikin Duniya.