Mu sanar da ‘ya’yanmu abin da yake ɓoye (1)

Daga AISHA ASAS

Wata ƙaramar yarinya ‘yar shekara tara ta tambaye mahaifiyarta, mama menene jima’i? cikin hanzari wannan mahaifiyar ta katse zancen cikin faɗa ta ce “kar na sake jin wannan kalmar daga bakinki.”

Kwanaki bayan haka, ta je wa maigadin gidan nasu da tambaya irin wannan.

Cikin tatausan lafazi irin na yaudara ya ce mata, “jima’i wani abu ne me kyau, kuma duk wadda ba ta yin shi ba ta kyau ta ba.” Za ka koya min?” ta tambaye shi. a taƙaice wannan tambayar ce ta ba wa mai gadin damar lalata yarinyar tsayin lokaci kafin iyayen su farga.

Tambayata a nan, shin laifin waye? Mai gadin da ya yi wasa da hankalinta ya yaudare ta? Ko mahaifiyarta? Babu shakka kaso tamanin bisa ɗari na laifin zai tafi ga mahaifiyarta.

Wannan darasi na yau na da matuƙar muhimmanci, don haka na ke kira gare ki ya ke uwa, ki yi masa fahimta ta sani ba ta ra’ayi ba. Domin mun jima mu na kallon waɗanda ke koyar da ‘ya’yansu wani abu da ya shafi wannan ɓangare a matsayin rashin kunya ko abin da bai dace ba.

Wani kaso mai ɗan nauyi a ‘ya’yamu da suka samu kansu a gurɓataciyar hanya ya samo asali ne daga ɓoye-ɓoyen da mu ke masu akan sha’anin da ya zama haƙƙinmu mu sanar da su. Idan ma ba mu yi ba, wasu za su sanar da su, sai dai babu tabbacin za su samu bayyanin a kyakkyawar siga kamar yadda ke uwa za ki yi. Ba za ki musanta hakan ba idan kin yi duba da yadda kafafen sada zumunta suka zama jiki ga ‘ya’yanmu da kuma yadda suke da hanyoyi masu sauqi na samun bayyanai ko gani da ido kan sha’anin da ya ɗaure masu kai.

Yana da kyau ya ke uwa ki sani, yana daga cikin tarbiyya bayyana wasu al’amurra da suke ɓoye ga yaranki. Misali: kwanciyar aure, jinin al’ada (Haila) da sauran su. Sai dai ba ina nufin bayyana su kai tsaye ba, sai dai yin bayanin cikin hikima da kuma ƙoƙarin dasa ma’anar da kike so su yi wa abin a shekarunsu don kare su daga cin zarafi.

‘Yar shekara tara idan za ki yi mata bayani daban yake da na ‘yar sha biyu. Hakazalika ‘yar sha biyu ba za ki yi mata bayyanin da za ki yi wa ‘yar sha biyar ko sha shida ba. Ma’ana ki yi masu bayanin da shekarunsu za su iya xɗauka.

Misali: yaronki ɗan shekara tara zuwa goma ya tambaye ki, “mama menene fyaɗe? Idan ki na aiki ne ki ce ma sa ya jira ki kammala. Bayan kin samu nutsuwa, ki zaunar da shi kusa da ke, cikin hikima da kwanciyar hankali za ki tambaye shi inda ya ji kalmar. Amsar da zai ba ki ce za ta sanar da ke matakin ɗauka kan lamarin. Ma’ana idan wurin abokanai ne za ki ɗauki matakin nisanta shi da su. Bayan kin kammala da wanan matsalar, sai ki fara amsa tambayarsa da cewa, “fyaɗe wani mummunan abu ne da Allah ke fushi da mai yin sa. Kuma iyaye ke yin kuka idan ɗansu ya yi. Fyaɗe zalunci ne kuma duk wanda ke yin sa ba zai shiga aljanna ba. “

Wannan amsar ce ƙwaƙwalwarshi zata iya ɗauka. Kuma babu wanda zai canza masa ma’anar ta ya amince da shi. Kinga zai taso da tsanar kalmar tare da nisantar duk wanda ya ji ance ya yi fyaɗe, duk da cewa bai san ya akeyin fyaɗen ba.

Akwai shekarun da sai ‘ya’yanki sun kai su ya kamata ki sanar da su abin da yake ɓoye, wanda a lokacin ne za su fahimce ki. A lokacin da duniya ta ke zaune ƙalau zan ce za ki iya jira har ‘ya’yanki su kai shekara sha uku zuwa sha biyar kafin ki yi masu bajikolin sirrin ɓoye. Amma a wannan zamani da mu ke ciki a yanzu zan iya cewa tun yaranki na takwas ya kamata ki fara yi masu jan kunne da tsorata su akan ababen da za a iya amfani da su wurin cutatar da su. Idan sun kai goma ki fara fahimtar da su dai-dai da yanda ƙwaƙwalwarsu zata iya ɗauka.

Ilimin jima’i saninsa ga yaranmu na da muhimmanci ko da ba su tambaye mu ba. Domin a baya ne kalmar ta ke a ɓoye, amma a yanzu ta zama ruwan dare sakamakon yadda kunya ta yi ƙaranci a tsakanin mutane. Wannan ne zai sa yaro tun bai isa komai ba ta ke fita daga cikin jerin baƙin kalmomi a kunnenshi. Walau dai ya ji ta a yarenshi ko a Turanci. Kuma sanannen abu ne rashin sanin ma’anar abu a wurin yaro na hana ƙwaƙwalwarshi hutu.