Gyaran fata (1)

Daga AISHA ASAS

Babbar matsalarmu a kwalliya dai ba ta wuce rashin samun fatarmu a yanayin da mu ke buƙata, wanda hakan kan hana kwalliyar fita raɗau yanda za ta ƙayatar da mai kallo. Kamar yadda mu ka sani, ba ƙazanta kawai ce kan iya haifar da lalacewar fata ba. Sau da yawa mu kan yi tsafta amma mu kasa samun biyan buƙata.

Uwar gida ki kula da abincin da ki ke ci. Ki tabbatar ki na ba wa jikinki ingantaccen abinci dai-dai da halin da ki ke da shi. Na sani wasu kan jahilci kalmar abinci mai gina jiki, a na su fahimtar, sai da kuɗi mai yawa za ki iya ba ma jikin ki abincin da zai gina shi.

Hankalinmu kan tafi kan abincin ‘yan gayu waɗanda masu kuɗi ke ci a gidajensu, don haka sai mu fitar da kan mu daga cikin jerin waɗanda za su iya ba wa jikinsu nagartaccen abinci.

To uwar gida ba haka zancen yake ba, domin abinci mai gina jiki ya fi yawaita a cikin kayan mu na gargajiya da mu ke renawa. Misali zogale, kuka, dawa, rama, ‘yar unguwa, hatsi da sauran su. Sai dai matsalar kawai sanin yanda za a sarrafa su don samun abincin da zai gina jiki.

Zai yi kyau idan uwar gida za ta dinga bibiyan shafukan da suke ilimintar da mutane kan sha’ani na abinci da lafiyar jiki, don fahimtar ta yanda za ki tallafa wa fatarki ta ɓangaren abinci.

Yana da kyau ki san cewa ba ko wane mai, sabulu da kayan ƙawa ne fatarki za ta iya amsa ba, don haka ya kamata ki fara sanin abin da fatarki ke so kafin amfani da shi. Ki kula da rana, domin a cikin rana akwai abin alfanu ga fata, kuma akwai abin da ka iya cutar da ita, kuma lallai cutarwar ya fi alfanun yawa.

Inda fatarki za ta amfana da rana shine da safe, a lokacin da rana ta hudo, ba ta yi qarfi ba, zuwa ɗan lokacin da za ta fara zafi matsakaici. A wannan lokacin tana ɗauke da wani sinadari da yake amfanar da fata, amma a lokacin da ta tsananta ba abin da fata za ta samu sai cutarwa, don haka uwar gida ta guji shiga rana a irin wannan lokaci sai bisa ga lalura.

Duk da taka-tsan-tsan da uwar gida za ta yi, ance in kana da kyau ka ƙara da wanka.

Uwar gida za ta iya amfani da kankana wurin taimaka wa fatarta. Za ki yi amfani da tuwon cikin ta kina shafa wa fuska wuya kai har ma da jiki in da hali. Tsayin mintuna talatin kafin kiyi wanka. Tana sanya fata kyau da kuma kashe ƙwayoyin cuta da ka iya haifar da ƙuraje.

Har wa yau, za ki iya amfani da kankana idan kin haɗa ta da gurji a shafa a fuska da wuya tsayin mintuna talatin da biyar sannan a wanke. Yana magance matsalar ƙunar rana.