Amai da lashewa: Musk ya sake zawarcin sayen Kamfanin manhajar Tiwita

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai Biloniya, kuma attajiri mafi kuɗi a Duniya, Elon Musk ya sake waiwayar maganar sayen Kamfanin manhajar Soshiyal midiyar nan ta Tiwita.
Musk ya yi wanna batu mai kama da amai da lashewa ne a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda jaridar Reuters ta rawaito.

A kwanakin baya dai idan ba mu manta ba, Attajirin ya so ya sayi kamfanin na Tiwita, a kan farashin Dalar Amurka biliyan $44. Inda daga baya kuma ana tsaka da cinikin kuma muka ji Attajirin ya sake bayyana cewa, ya fasa sayen Kamfanin saboda wasu abubuwa masu kama da muna-muna da yake zargin mahukunta kamfanin da yi masa.

Kuma idan za mu iya tunawa, kamfanin bai yarda da waccan janye ciniki da Musk ɗin ya yi ba, inda ba su yi ƙasa a gwiwa ba, suka maka shi a kotu a watan Oktoba inda suka nemi kotu ta tilasta masa ƙarasa cinikin Tiwita da aka fara a watan Afrilu ta hanyar biyan waɗancan maƙudan kuɗaɗe su kuma su mallaka masa kamfanin.

A yanzu haka wancan ribas da Musk ɗin ya yi na cewa, ya dawo da kansa ya ce zai sayi kamfanin a kan wancan farashin na Dalar Amurka biliyan 44 da aka yi masa tun a baya, shi ya kawo wannan ƙarshen wannan Shari’a tsakanin kamfanin da Attajirin.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata 3 ga Oktoba, Musk, Shugaban zartarwa ba kamfanin motocin lantarki na Tesla ya aike wa da Alqalin kotun Delaware ta Chancery, kotun dake gudanar da shari’ar tasu a kan ya amince zai cigaba da cinikin na kamfanin Tiwita. Kuma majiyarmu ta bayyana cewa, vangarorin biyu sun zauna a teburin sulhu sun fuskanci juna, har ma alƙalin ya sallame su, amma ya buƙaci su dawo washegari don a ƙara daddale maganar.

Kodayake, Biloniya ya bayyana cewa, ya yi aman ne ya lashe ne game da sayen Kamfanin bayan ya gano cewa, sayen Kamfanin zai ƙara hanzarta masa cimma burinsa na ƙirƙirar wata manhajar ta komai da komai da ake kira ‘X’.

Amma wasu masu nazari a kan al’amarin suna ganin cewa, Musk ya yi haka ne don ya samu ya guje wa shari’ar da ake yi game da cinikin. Domin ya hango alamun rashin nasara a ciki. Sannan ya san ko ya ƙi, ko ya so, kotu za ta iya tursasa shi ya sayi Tiwita ko yana so, ko ba ya so.