NUT ta buƙaci gwamnoni su gaggauta biyan basukan da su ke binsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT) ta yi kira ga gwamnonin jihohin da malaman makaranta ke bi bashi da su yi amfani da ɗan lokacin da ya rage musu a kan karagar mulkin su biyan haƙƙoƙin.

Sakatare-Janar na ƙungiyar, Dokta Mike Ike-En ne ya yi wannan kira ranar Talata a Abuja albarkacin zagayowar Ranar Malamai ta Duniya wadda za a yi ranar Laraba.

A cewar Ike-Ene, akwai gwamnoni da dama da ba su kammala biyan bashin albashin da malaman firamare da na sakandare ke bi a jihohinsu ba.

Don haka ya ce, akwai buƙatar gwamnonin da lamarin ya shafa su yi ƙoƙarin biyan malaman haƙƙoƙinsu a tsakanin ’yan watannin da suka rage musu a kan mulki.

“Yawancin malaman sun koka kan rashin biyan su albashi a kan kari duk da tsadar rayuwar da ake fama da ita.

“A wasu jihohin, malaman firamare na bin gwamnatin jihar bashin albashi na watanni huɗu zuwa 18,” inji Ike-Ene.

Ranar 5 ga watan Oktoba ta kowace shekara Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware don gudanar da bikin Ranar Malamai ta Duniya da zummar yabawa da kuma ƙarfafa wa malaman makaranta gwiwa a faɗin duniya.