Gobara ta lamushe wani ɓangare na Kasuwar Balogun ta Legas

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka yi wata gobara da ta lamushe shaguna da dama a kasuwar Balogun dake kan titin Martins Street a jihar Legas.

Hotunan wannan ƙazamar gobarar da ta farmaki wani sashe na babbar kasuwar suna ta yawo a kafafen yanar gizo da yadda gabarar ta dinga ci ganga-ganga tana jawo asara.

Jami’in kula da abokan hulda na Hukumar kashe gobara ta Legas yayin wata zantawar manema labarai da shi a wayar tarho a lokacin da gobarar take cigaba da ruruwa ya ba da tabbacin cewa, hukumar tana iya bakin ƙoƙarinsa don ganin an daƙile gobarar don hana ta cigaba da ruruwa.

“Mun amsa kiran da aka yi mana a take zuwa gurbin da ibtila’in ya afku. Kuma motocin aikinmu guda biyu ma yanzu haka suna ƙasa kuma suna iya ƙoƙarinsu don ganin an kashe gobarar ba tare da ɓata lokaci ba.

Kodayake dai, har yanzu ba a san musabbabin wannan gobara ba, amma ‘yan Nijeriya da dama suna kakabin yawan afkuwar gobara a wannan kasuwar musamman ma a dai-dai wannan lokaci da ‘yan kasuwar suke ƙara cika shagunan su da sabbin kaya don jiran cinikin watan Disamba.

Hakazalika, da ma tun a shekarun 2019, 2020, 2021 da ma farkon shekarar 2022 da muke ciki, akwai rahotannin afkuwar gobarar a wannan kasuwar wanda ya jawo salwantar kaya masu daraja da dukiyoyi.