Man United za ta daƙile yunƙurin FA na dakatar da Ronaldo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester United ta ce za ta ɗauki dukkanin matakan da suka dace wajen daƙile yunƙurin hukumar FA game da shirinta na dakatar da ɗan wasan gaban ƙungiyar Cristiano Ronaldo, bayan abin da ya faru a filin wasa na Goodison Park cikin watan Aprilun da ya gabata.

Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, Erik ten Hag ya ce ɗan wasan gaban na Portugal ba zai lamunce duk wani rashin adalci daga hukumar ta FA ba.

Cristiano Ronaldo wanda ’yan sanda suka aikewa da takardar gargaɗi ya na da zavin daga yanzu har zuwa ranar litinin ɗin makon gobe don amsa tuhumar da ake masa ko kuma fuskantar hukunci.

Wani faifan bidiyo dai ya nuna yadda ɗan wasan na United mai shekaru 38 cikin fushi ya hankaɗe wayar wani yaro da ke ƙoƙarin ɗaukarsa hoto lokacin da ya ke fita daga fili bayan shan kaye a hannun Everton da ƙwallo 1 mai ban haushi, lamarin da ya ja hankalin mahukunta tare da kiraye-kirayen ɗaukar mataki kan abin da suka kira keta mutuncin ƙaramin yaron.

Matakin aikewa da gargaɗin ga Ronaldo dai ya biyo bayan dogon binciken da jami’an tsaro suka yi kan lamarin, sai dai har zuwa yanzu ba a ji ta bakin ɗan wasan ba, ko da ya ke wasu majiyoyi sun ce tuni ya yi nadamar abin da ya aikata tare da kiran yaron har gidansa, har ma da cin abinci tare.

A cewar Erik ten Hag ya tattauna da Ronaldo kan batun kuma ya bayyana masa cewa sam ba zai karɓi hukunci mai tsauri kan lamarin ba.