Kasuwanci

’Yan sanda sun kama ɓarayi 50 a gobarar kasuwar Maiduguri 

’Yan sanda sun kama ɓarayi 50 a gobarar kasuwar Maiduguri 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane 50 da ake zargi da yin sace-sace a kasuwar Monday Market ta Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Kamilu Shatambaya ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba a Maiduguri. Ya ce jami’an rundunar da aka tura domin kare rayuka da dukiyoyin da gobarar ta afku a kasuwar, sun kama waɗanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu. Ya ce waɗanda ake zargin sun yi awon gaba da kadarorin waɗanda abin ya shafa…
Read More
2023: Yadda al’amuran zaɓe suka jawo tashin farashin man fetur zuwa Naira 300 kowacce lita

2023: Yadda al’amuran zaɓe suka jawo tashin farashin man fetur zuwa Naira 300 kowacce lita

AMINA YUSUF ALI Dillalan man fetur, a ranar Talatar da ta gabata sun bayyana cewa, tashoshin man fetur na Nijeriya da dama sun daina lodin man fetur a halin yanzu. Hakan ya faru ne sakamakon fargabar abinda ka- je-ya-zo a yayin tattara sakamakon babban zaɓe a faɗin ƙasar nan. Hakazalika, rahotannin sun bayyana cewa, hakan ya matuƙar jawo tsadar man fetur, inda ake sayar da man fetur a tsakanin Naira 194 zuwa 200 kowacce lita a gidajen man NNPC kaɗai, sai sauran gidajen man na 'yan kasuwa kuma ake sayar da su a kan Naira 250 zuwa 300 a kan…
Read More
Gobara ta tashi a kasuwar Monday Market a Maiduguri

Gobara ta tashi a kasuwar Monday Market a Maiduguri

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri Babbar kasuwar Maiduguri wadda aka fi sani da Monday Market tana ci da wuta, sakamakon tashin gobara da safiyar Lahadi. Ya zuwa haɗa wannan rahoto an ga ma'aikatan kashe gobara na ƙoƙarin daƙile yaɗuwar wuta zuwa sassan kasuwar. Daraktan Hukumar Kwana-kwanan a jihar, Umaru Kirawa, ya tabbatar da aukuwar gobarar sa'ilin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN). Ya ce ma'aikatan kashe gobara na jihar tare da haɗin gwiwar takwarorinsu suna aiki tukuru wajen shawo kan gobarar.
Read More
IMF ta nemi gwamnatin Nijeriya kan ta cire tallafin mai kafin nan kafin tsakiyar 2023

IMF ta nemi gwamnatin Nijeriya kan ta cire tallafin mai kafin nan kafin tsakiyar 2023

Daga AMINA YUSUF ALI Gidauniyar Kuɗi ta ƙasashen duniya, IMF ta nemi gwamnatin Nijeriya a kan ta cire tallafin mai kafin nan da tsakiyar shekarar da muke ciki ta 2023, sannan ta karkatar da kuɗin wajen gudanar da abubuwan cigaba. IMF ta ce ta yi wannan kira ne saboda Nijeriya ta cika maganarta da ta ce za ta cire tallafin man a tsakiyar shekarar 2023. Gudauniyar wacce take a Washington ta Amurka a wani rahoto da ta saki ranar Larabar makon da ya gabata ya bayyana cewa, ƙasar Nijeriya ta samu matsalar tattalin arziki bayan annobar COVID-19 tare da qari…
Read More
Farashin kaya ya tashi saboda ƙarancin Naira na cigaba da tsananta

Farashin kaya ya tashi saboda ƙarancin Naira na cigaba da tsananta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya sake tashi zuwa matsayi mafi girma da kashi 21.82 a watan Janairu daga kashi 21.34 cikin ɗari a watan Disambar bara. Wannan na zuwa ne a rahoton baya-bayan nan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, 2023. Sabon ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke fuskantar rashin matsalolin tattalin arziki sakamakon ƙarancin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima na Naira. Wannan ƙaruwar na Janairu yana nuna ƙaruwar kashi 0.47 idan aka kwatanta da 21.34 da…
Read More
Masu sayar da Naira za su fuskanci ɗauri a gidan yari – CBN

Masu sayar da Naira za su fuskanci ɗauri a gidan yari – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da ake tsaka da halin matsi a sakamakon canjin kuɗin Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sha alwashin cafkewa da gurfanar da duk wani mai POS ko makamancinsa da aka samu da sayar da takardun Naira a matsayin kuɗin hada-hada (cajis). CBN ya ja kunne cewa, wannan lafi ne da yake da alaƙa da rashawa kuma laifi ne da zai iya sa a kulle mutum a gidan kaso. A cewar babban bankin, an yarda da biyan kuɗin ladan hada-hada wanda ake cewa cajis. Kuma a cewar sa, ba a haramta wannan ba. Amma wannan…
Read More
Yadda za ku kai rahoton masu sayar da sabbin takardun Naira

Yadda za ku kai rahoton masu sayar da sabbin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fitar da wasu hanyoyi domin bai wa 'ya ƙasa damar kai rahoton masu sana'ar POS da ke cajin fitar hankali idan an zo cire kuɗi. Darakta a CBN, Mr Joseph Omayuku, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da suka shirya ranar Talata a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa. Omayuku ya gargaɗi masu wannan hali da su daina, kana ya shawarci jama'a da su yi amfani da waɗannan hanyoyi na ƙasa wajen kai rahoton duk wani mai POS da aka samu yana karɓar caji wuci misali: 07002255226; Telephone Ext: 711025…
Read More
Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a ci gaba da amfani da tsohuwar N200 nan da wata biyu. Ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa kai tsaye da safiyar Alhamis. Buhari ya ce ya tsawaita wa'adin amfani da N200 ne domin rage wa 'yan ƙasa raɗaɗin ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a faɗin ƙasa. A cewarsa, za a ci gaba da amfani da N200 ne daga ran 10 Fabrairu zuwa 10 ga Afrilun 2023. Sai ƙarin wa'adin in ji Buhar, bai shafi tsoffin N500 da N100 ba. Shugaban ya ce ƙofar CBN…
Read More
Takardun kuɗi: CBN ya ce ba zai yi biyayya ga Kotun Ƙoli ba

Takardun kuɗi: CBN ya ce ba zai yi biyayya ga Kotun Ƙoli ba

*Ya ce duk mai tsohon kuɗi ya kai CBN Daga AISHA ASAS Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da kuma N1000 sun daina amfani a hukumance tun daga ran 10 ga Fabrairu, 2023. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban CBN a Bauchi, Haladu Idris Andaza, yayin zantawarsa da manema labarai ranar Litinin a garin Bauchi. Ya ce, “A tsakanin awowi 24 da suka gabata, mun samu tambayoyi da yawa daga wajen mutane game da batun tsoffin kuɗi." A cewarsa, "domin kawar wa jama'a shakku, muna sanar da cewa a shirye CBN yake…
Read More
Ganduje ya rufe kanti a Kano saboda ƙin karɓar tsoffin kuɗu

Ganduje ya rufe kanti a Kano saboda ƙin karɓar tsoffin kuɗu

Daga HAMISU IBRAHIM a Kano Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da umarnin rufe katafaren kantin zamanin nan, wato Wellcare Supermarket, saboda ƙin karɓar tsoffin takardun Naira 200, 500 da kuma 1000. Muƙaddashin Hukumar Kare Muradin Kwastoma na Jihar Kano, Dokta Baffa Babba Dan’Agundi ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan rufe kantin. A cewar Dan’Agundi, aiwatar da umarnin na Gwamna ya zama wajibi sakamakon shagon ya ƙi karɓar tsoffin kuɗi wanda hakan ya saɓa wa umarnin Gwamna Ganduje da ya ce a ci gaba da amfani da tsoffin Naira a jihar. Ya ƙara…
Read More