Nijeriya ta zama koma baya da matsayin ƙasa mafi samar da man fetur a Afirka

Daga AMINA YUSUF ALI

A cikin watan Agustan bana ne dai ƙasar Nijeriya ta koma samar da abinda bai wuce ganga 972,000 ta man fetur a kowacce rana. A yayin da ƙasashen Angola da Libya suka yi mata zarra ta hanyar samar da adadin da ya wuce wanda take samarwar kamar yadda ƙungiyar ƙasashen masu samar da man fetur (OPE) ta rawaito.

OPEC ta saki waɗannan alƙalumman ne wannan watan Satumbar shekarar 2022 da muke ciki. Ita kuma ta samu wannan rahoto daga hukumar daidaita farashin mai ta Nijeriya.

Dama tun a a makon da ya gabata ne dai jaridar Ingilishi ta Punch, ta bayar a rahoton cewa, adadin man da Nijeriya take samarwa ya ruguzo zuwa ƙasa da ganga miliyan guda a rana guda tun cikin watan Agusta, 2022, kuma shi ne adadi ma fi ƙanƙanta da ta tava samarwa. Domin a baya takan samar da ganga miliyan kowacce rana.

Da ma kafin watan Yulin 2022 tana samar da gangan 1,083,899 daga watan Yulin ne zuwa yau adadin ya yu ta raguwa zuwa ganga 972,394, abinda ya ba wa ƙasashen Angola da Libiya damar shan gaban Nijeriya su yi mata zarra a fagen.

A yanzu haka dai qasar Angola ita ce ja gaba a Afirka gabaɗaya a cikin watan da ya gabata zuwa yau, don yanzu haka tana samar da wajen gangar mai miliyan 1.187 a kowacce rana.

Ƙasar Libiya ita ke biye da Angola, don tana samar da ganga miliyan 1.123 kowacce rana daga watan Agusta zuwa yau.

Hakazalika, ƙasar Saudiyya ma adadin man da take samarwa kowacce rana ya ƙaru a yayin da na Nijeriya ya yi matuƙar yin ƙasa.