Kasuwanci

Dalilin IPMNAN kan dakatar da sayar da fetur a gidajen mai

Dalilin IPMNAN kan dakatar da sayar da fetur a gidajen mai

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Dillalan Fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta dakatar da sayar da fetur a gidajen mai a faɗin ƙasa. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da ƙungiyar ta aike wa mambobinta mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Mohammed Kuluwu da kuma kwanan wata 6 ga Fabrairun 2023. A cewar ƙungiyar, in ban da asara babu abin da manmobinta za su samu muddin suka ci gaba da sayar da fetur a cikin wannan yanayi. Wasiƙar ta ce, "Biyo bayan halin matsin da ake fuskanta wanda ya shafi hada-hadarmu da janyo mana asara, ana umartanku da ku dakatar da…
Read More
Yadda fitaccen biloniya ya yi asarar kaso 93% na dukiyarsa a Chana

Yadda fitaccen biloniya ya yi asarar kaso 93% na dukiyarsa a Chana

Daga AMINA YUSUF ALI Shahararren attajirin biloniyan nan ɗan ƙasar Chana mai suna, Hui Ka Yan ya yi asarar kaso 93% na dukiyarsa.  Hui Ka Yan, shi ne shugaban rukunin kamfanoni na  kamfani na Evergrande Group a lasar Chana. Kafin dukiyar tasa ta dulmiye, ya kasance yana da ƙarfin arzikin da ya kai Dalar Amurka biliyan 42. Amma zancen da a ke yi yanzu, dukiyar tasa ta dulmiye i zuwa, Dalar Amurka biliyan uku kacal! Biloniyan na ƙasar Chana, ya kasance ɗaya daga cikin hamshaƙan Attajirai masu dukiya da ƙasar ta Chana take ji da su. Amma a halin da…
Read More
Da jarin Naira 50 na fara kasuwanci – Matashi Dini Majia

Da jarin Naira 50 na fara kasuwanci – Matashi Dini Majia

DAGA MUKHTAR YAKUBU a Kano A wannan lokacin da ake ganin matasa suna da son su samu rayuwa cikin sauqi ba tare da sun tashi sun nemi na kansu ba. Don haka da yawa sai matasan suka zama marassa aikin yi da kuma dogon buri na yin rayuwa mai tsada. Sai dai ba a taru an zama ɗaya ba, domin kuwa Dini Muhammad Majia yaro ne matashi da tun farkon rayuwar sa ya taso da zuciyar neman na kansa, wanda a yanzu yana cikin matasan 'yan kasuwa a cikin garin Kano, wanda kuma yake da kishin samar wa matasa hanyoyin kasuwanci…
Read More
Sauyin kuɗi ya jefa ‘yan kasuwa a matsanancin hali – Sani Isah

Sauyin kuɗi ya jefa ‘yan kasuwa a matsanancin hali – Sani Isah

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yi kira ga gwamnati musamman Babban Bankin Ƙasa CBN akan a wadata al'umma da sabbin takardun kuɗi don rage matsanancin wahala da ake ciki. Shugaban rukunin Kamfanin Sani Asiya, Alhaji Sani Isah ne ya yi kiran da yake zantawa da 'yan jarida, inda ya ce tunda 'yan kasuwa suke a ƙasar nan basu taɓa tsintar kansu a hali irin wannan ba, kasuwa ta zama kamar a raba ƙwallo saboda mutane da ya kamata su zo su yi sayayya babu kuɗi a wajensu. Ya yi nuni da cewa akwai mutane da yawa da ba su…
Read More
Har yanzu dai Nijeriya ita ce jagaba wajen samar da fetur a Afirka – OPEC

Har yanzu dai Nijeriya ita ce jagaba wajen samar da fetur a Afirka – OPEC

Daga AMINA YUSUF ALI Duk da qalubale da matsalolin da ta sha fuskanta, ya zuwa ƙarshen shekarar 2022, Nijeriya ta kasance ita ce kan gaba wajen samar da man fetur a Afirka. Wannan lafazin ya fito ne da yawun Ƙungiyar ƙasashen masu samar da man fetur a Duniya (OPEC). OPEC ta bayyana cewa, Nijeriya ta ƙarƙare shekarar 2022 a matsayin qasar da ta fi kowacce samar da man fetur a Nahiyar Afirka. A cewar OPEC, Nijeriya a watan Disamba na shekarar bara ta samu ƙarin kaso 4% na man fetur ɗin da take samarwa. Wato gwari-gwari ta tashi daga samar…
Read More
CBN ya tswaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10

CBN ya tswaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa'adin daina karbar tsoffin takardun Naira ya zuwa 10 ga Fabrairu, 2023. Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya ba da sanarwar ƙarin wa'adin a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi. Ya ce, sai da CBN ya nemi amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kafin ɗaukar matakin tswaita wa'adin da kwana 10. “La'akari da halin da ake ciki, mun nemi yardar Shugaban Ƙasa kan waɗannan abubuwa: Sahalewar tswaita wa'adin da kwana 10 daga 31 ga Janairu zuwa 10 ga Fabrairu don ba ba da damar ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira daga hannun…
Read More
Mun ɗaura ɗamarar kawo sauyi ga ‘yan kasuwa a Kano – Alkamatu

Mun ɗaura ɗamarar kawo sauyi ga ‘yan kasuwa a Kano – Alkamatu

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Shugaban Kamfanin Alkamatu Brain Box Solution, wato matashin nan mai rajin ganin matasa da sauran al'umma sun samu damar tsayawa da ƙafafunsu, Kwamared Alkamatu Hussain Abdulkadir ya ce shirinsu ya kankama na ganin a taimaka wajen kanikancin kasuwancisu. Alkamatu ya ce lallai babu abinda ke gabansu yanzu haka da ya wuce ganin yankin Arewa ya ci gaba wajen harkokin kasuwanci da sauran hanyoyin dogaro da kai. Matashin da yake taka rawar gani wajen taimakon jama'a a Jihar Kano dama makwabtan jihohin Kano ya tabbatar da cewa sanin kowa ne kamar yadda ɗan Adam da…
Read More
CBN ya wayar da kan masu ta’ammali da POS a Zamfara

CBN ya wayar da kan masu ta’ammali da POS a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban Bankin Najeriya CBN ya gudanar da taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya ga ƙungiyoyin dake harkokin kasuwancin POS reshen jihar Zamfara kan mahimmancin shirin eNaira da canjin kuɗaɗen da ake ciki. Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na Maryam da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Alhamis wanda ƙungiyar masu gudanar da POS reshen jihar Zamfara suka shirya a hukumance. A nasa jawabin, Shugaban Babban Bankin na CBN reshen Gusau, Malam Buhari Abbas, ya ce ɗaya daga cikin dalilan bullo da tsarin eNaira da kuma sauya fasalin wasu kudaden Najeriya…
Read More
Shugaban Kasuwar Mile 12 a Legas ya kira taron zaman lafiya

Shugaban Kasuwar Mile 12 a Legas ya kira taron zaman lafiya

Daga DAUDA USMAN a Legas A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne Shugaban Kasuwar Mile 12 a Legas, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Dallatun Egbaland) a Abeokuta ta jihar Ogun mazaunin cikin garin Legas ya kira taron neman ƙarin zaman lafiya da haɗin kawunan 'yan kasuwar ta Mile 12 da kewayenta. Taron wanda ya ƙunshi dukkannin al'ummar kasuwar da shuwagabannin ɓangarori da dattawan kasuwar da Yarabawa da sauran ƙabilu masu gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar gaba ɗaya. Sakataren kasuwar Alhaji Balarabe Idiris ya jagoranci gabatar da taron kaɗan daga cikin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar akwai Alhaji Abdullahi Tukur Kura,…
Read More
Hana motoci daga Arewa shiga Legas ba daidai ba ne – RTEAN

Hana motoci daga Arewa shiga Legas ba daidai ba ne – RTEAN

….Ta buƙaci Gwamnatin jihar ta gaggauta janye matakin hanin Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa (RTEAN) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta gaggauta janye matakin hana motocin fasinja da suka fito daga Arewa shiga jihar. Cikin sanarwar manema labaraida ya fitar ranar Alhamis, Babban Sakataren RTEAN, Kwamred Yusuf Ibrahim Adeniyi, ya ce ƙungiyar ta samu labari daga reshenta na Jihar Kwara da wasu jihohin Arewa cewa Gwamnatin Legas ta ɗauki matakin hana motocin fasinja da suka fito daga Arewa shiga jihar. Ya ce, "Umarnin hakan ya fito ne daga jami'in Gwamnatin Jihar, Seyi Bamigbose…
Read More