04
Jul
Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da canjin kuɗaɗen ƙasar waje suka yi matuƙar wahalar gaske, Bankuna sun umarci masu neman sayen kuɗaɗen ƙasar wajen da su fara bin layin neman kuɗin tun wata guda gabanin lokacin da za su yi amfani da kuɗin. Bankuna sun ba da sanarwar tun a watan Mayun shekarar nan da muke ciki ta 2022. Bayan da wasu ɗalibai da kuma 'yan kasuwa suka yi ta ƙorafin yadda aka ja dogon lokaci kafin su samu canjin kuɗaɗen duk kuwa da sun cika dukkan sharuɗɗan da suka kamata. A wata wasiƙa da wata majiya ta bayyana…