14
Jan
Daga AMINA YUSUF ALI Wata matashiyar mai suna Angela Job Emodiae, wacce ta yi ikirarin cewa ta haɗa Naira biliyan guda a cinikin ƙuli-ƙuli, ta yi amanta ta lashe. Inda ta bayyana cewa ta faɗa ne kawai don saboda raha. Idan za a iya tunawa, a ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, 7 ga watan Janairun 2023 matashiyar mai suna Angela wacce take zaune a garin Jos ta jihar Filato, mamallakiyar kamfanin Anjees Food, ta wallafa a shafinta na dandalin Fesbuk cewa, ta haɗa Naira biliyan guda a kan cinikin ƙuli-ƙuli. Sannan ta ƙara da cewa, a wannan shekara…
