25
Nov
Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da ƙasar Nijeriya take fama da matsanancin ƙaranci da tsadar kayan abinci kama daga hatsi har kayan masarufi, musamman shinkafa wacce aka fi amfani da ita a kodayaushe. A yanzu haka ƙasar ta ƙulla wata yarjejeniya da ƙasar Masar don ta dinga kai musu shinkafa. A yanzu haka dai ƙungiya mai zaman kanta ta manonman shinkafa a Nijeriya (RIFAN) da wani kamfani mai zaman kansa a Nijeriya sun rattaba hannaye a wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninsu da ƙasar ta Misira don a fara sayar musu da shinkafar da aka noma a gida Nijeriya. Wannan…
