Kasuwanci

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR) ta mayar da Bitkoyin kuɗin ƙasarta

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR) ta mayar da Bitkoyin kuɗin ƙasarta

Daga AMINA YUSUF ALI Jamhuriyar mulki ta Afirka ta tsakiya (CAR) ita ma ta bi sahun El Salvador wajen mayar da Bitkoyin a matsayin kuɗinta na ƙasa. Jaridar Sierra Leone Telegraph ta bayyana cewa, Afirka ta Tsakiya wacce a kwanakin baya yaƙi ya yi wa raga-raga da ita, ta ƙaddamar da Bitkoyin a matsayin kuɗin ƙasarta na halaliya wanda za a iya yin dukkan wata hada-hadar ta kuɗi, kamar cinikayya, ko harkar banki da sauransu. Sai dai wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya jawo mata cece-ku ce, domin ana zargin ƙasar ta yi gaban kanta ne ba tare da…
Read More
Najeriya ce ta 8 a jerin ƙasashen da ake sayar da fetur da arha – Bincike

Najeriya ce ta 8 a jerin ƙasashen da ake sayar da fetur da arha – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai farashin fetur a ƙasashe da dama na Duniya na yin tashin gwauron zabon da bai tava yi ba. Hakan na faruwa ne saboda rashin samun shi a wadace da ba a yi yanzu a Duniya. Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, wani sabon rahoto da wani kamfanin binciken ƙwaƙwaf mai suna Zutobi ya fitar, ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta 8 a jerin ƙasashen da har yanzu ake sayen litar fetur arha. An dai buga wannan bincike a cikin watan Afrilu, inda farashin galan 1 ke daidai da dala 1.82. Ƙasashen…
Read More
Za a shiga wahalar fetur da ba a taɓa yi ba — IPMAN

Za a shiga wahalar fetur da ba a taɓa yi ba — IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Dillalan Man fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta yi gargaɗin cewa, 'yan Nijeriya za su ga wahalar man fetur da ba su taɓa ganin irinta ba a ƙasar, idan dai har hukumar mai ta NMDPRA ba ta biya su kuɗaɗen dakon mansu ba. Shugaban IPMAN na Shiyyar Kano, Bashir Ahmad Ɗan-Malam, shi ne ya yi wannan gargaɗi a taron manema labarai a Kano ranar Litinin. A cewarsa, rashin biyan kuɗin dakon, wanda a turance a ke kira ‘bridging claims’, wanda adadin sa ya haura Naira biliyan 500, ya sanya da yawa…
Read More
Za a rage zaman kashe wando idan gwamnati ta taimaki ƙananan masana’antu –Zainab Ali

Za a rage zaman kashe wando idan gwamnati ta taimaki ƙananan masana’antu –Zainab Ali

Daga AMINA YUSUF ALI Yau filin namu na Kasuwanci ya yi gam-da-katar da wata matashiya wacce ta fara kafa masan'antarta, inda daga rarrafe har ta kai ga babban matsayi, wato Hajiya Zainab Yusuf Ali. Wakiliyar Blueprint Manhaja, Amina Yusuf Ali, ta samu tattaunawa da matashiyar 'yar kasuwar, inda za ku ji faɗi-tashinta da kuma darussan da za a koya. A sha karatu lafiya.  MANHAJA: Wacece Hajiya Zainab?HAJIYA ZAINAB: Da farko dai cikakken sunana shi ne, Zainab Yusuf Ali an haife Ni  a ranar 2 ga Janairun 1985 a Tudun Maliki, Ƙaramar Hukumar Kumbotso. Na yi karatun Firamarena daga 1992-1998 a…
Read More
Ɗauke Hukumar SON daga tashoshin jirgen ruwa ne sanadin shigo da kaya marasa inganci Nijeriya – Darakta

Ɗauke Hukumar SON daga tashoshin jirgen ruwa ne sanadin shigo da kaya marasa inganci Nijeriya – Darakta

Daga AMINA YUSUF ALI Daraktan janar na hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki (SON), Farouq Salim, ya bayyana cewa, tattalin arzikin Nijeriya yana qara rugujewa sakamakon kayayyaki marasa inganci da ake shigo da su cikin ƙasar, inda hakan ya faru ne sakamakon ɗauke hukumar daga tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya.  Daraktan ya yi wannan furuci ne a taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Legas mai taken, 'kaya masu inganci suna ceto rayuka, kuma su bunƙasa tattalin arziki'. Salim ya ƙara da cewa, in dai kuwa za a cigaba da shigo da waɗancan kaya marasa inganci, to kuwa ƙasar…
Read More
Bankin Access zai rikiɗe zuwa babban kamfani nan da watan Mayu

Bankin Access zai rikiɗe zuwa babban kamfani nan da watan Mayu

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni da aka samu daga Bankin Access sun bayyana cewa, nan da 1 ga watan Mayu mai kamawa za su ƙara bunƙasa harkokinsu i zuwa kamfanin hada-hadar kuɗin ba wai iya banki za su tsaya ba kawai.  Manajan daraktan Bankin, Herbert Wigwe shi ya bayyana haka a wata takardar sanarwar da kamfanin ya rarraba ga masu hannun jari a bankin. A takardar, ya sanar da canza sunan kamfanin  daga Accass Bank zuwa sabon kamfani mai suna Access Holdings, PIc, ko Access Corporation. "Wannan canjin zai sa mu bunƙasa daga banki zuwa babbar harkar kasuwanci na Duniya"…
Read More
Sallah: Masu sayar da kaji a Kaduna sun koka da rashin ciniki

Sallah: Masu sayar da kaji a Kaduna sun koka da rashin ciniki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu daga cikin masu sayar da kaji, talo-talo da agwagi a Kaduna sun koka kan rashin cinikin kajin gabanin bikin ƙaramar Sallah ta bana. Masu sayar da kajin sun nuna damuwarsu a hira mabanbanta da Kamfanin Dllancin Labarai na Ƙasa (NAN) ta yi da su a ranar Talata a Kaduna. Sun ce lamarin abin damuwa ne matuƙa, duk da cewa suna da kyakkyawan fatan ganin canji da zarar ma'aikata sun samu albashin watan Afrilu. Wakilin NAN wanda ya ziyarci fitacciyar kasuwar sayar da kaji a Kantin Koli a Babbar Kasuwar Kaduna, ya hangi mutane…
Read More
Wajibi ne Afirka ta yi shirin tunkarar yunwar da za ta kunno kai – Adesina

Wajibi ne Afirka ta yi shirin tunkarar yunwar da za ta kunno kai – Adesina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka (ADB), Akinwumi Adesina ya gargaɗi ƙasashen Afirka cewa su gaggauta bazama wajen bunƙasa noma, domin su samu abincin da za su tunkari yunwar da za ta buwayi Duniya, nan ba da daɗewa ba. Adesina ya ce, “tilas Afirka ta yi shirin tunkarar gagarimar yunwar da babu makawa sai ta darkako duniya.” Da ya ke amsa tambayoyin wasu fitattun manema labarai a Babban Taron Cibiyar Afirka ta Atlantic Council, ya ce ƙasashen Afirka da za su fi jin jiki su ne Waɗanda rikice-rikice da tashe-tashen hankula suka fi yi wa katutu,…
Read More
Elon Musk ya saye Tiwita kan fiye ninkin dukiyar Ɗangote

Elon Musk ya saye Tiwita kan fiye ninkin dukiyar Ɗangote

Daga AMINA YUSUF ALI Mutumin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya samu damar mallakar kamfanin Tiwita akan farashin Dalar Amurka biliyan $44, fiye da ninkin biyu na dukkan arzikin da ma fi kuxi a Afirka, Aliko Dyangote ya mallaka.  Kamar yadda jadawalin biloniyoyi na jaridar Ingilishi ta Bloomberg ya bayyana, a yanzu haka dai ƙarfin arzikinsa da ke Amurka biliyan $20.4 ne. Kuma shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Afrika, kuma na 72 a Duniya. A hannun guda kuma shi Elon Musk shi ne na ɗaya a arziki a Duniya kuma ƙarfin arzikinsa…
Read More
’Yan Nijeriya Miliyan 33.4 na amfani da Kirifto Karansi duk da haramcin CBN – Bincike

’Yan Nijeriya Miliyan 33.4 na amfani da Kirifto Karansi duk da haramcin CBN – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI  Rahotanni sun nuna cewa, kaso 20 da shiga daga masu zuba hannun jari a harkar sulalla na yanar gizo da aka fi sani da Kirifto Karansi sun fara dillancinsa a kwanakin nan. Haka zalika sabon rahotan ya bayyana cewa kaso 35 na balagaggun mutanen Nijeriya suna zuba hannun jari a kasuwancin sulallan.  Kodayake a kwanakin nan Babban Bankin Nijeriya ya haramta amfani ko hada-hadar sulallan Kirifto karanci a dukkan bankunan Nijeriya. Amma duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa, kimanin 'yan Nijeriya miliyan 33.4 sun mallaki kadara ta Kirifto ɗin ko kuma suna hada-hadar cinikayyarsa.  Haka…
Read More