CBN ya taƙaita cire kuɗi a POS zuwa dubu N20 a rana ɗaya

*Ya fitar da sabbin dokokin hada-hadar kuɗi

Daga WAKILINMU

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya taƙaita yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa a na’urar POS a rana ɗaya zuwa N20,000, a banki kuma ba za su wuce N100,000 ba a mako guda.

Hakan na ɗaya daga cikin irin matakan da babban bankin ya ce zai fito da su domin taƙaita yawon tsabar kuɗi a hannun mutane.

Ana sa ran wannan tsari ya soma aiki ya zuwa ranar tara ga watan Janairu, 2023.

Wannan na zuwa ne a lokacin da CBN ke shirye-shirye sakin sabbin takardun Naira da aka sake wa fasali don fara kashewa daga ranar 15 ga Disamba.

Wannan bayanin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da CBN ya fitar ranar Talata mai ɗauke da sa hannun Darakta a bankin, Haruna Mustafa.

CBN ya fitar da wasu sabbin dokoki waɗanda yake so a fara aiki da su wajen hada-hada da tsabar kuɗi a ƙasar nan.

Ya ce dokokin za su fara aiki ne daga ranar tara ga watan Janairun 2023.

Haka nan, sabbin dokokin na CBN na da nasaba ƙudurin da bankin ke da shi na taƙaita amfani da tsabar kuɗi wajen hada-hada.

  • Sabbin dokokin da CBN ɗin ya fitar sun haɗa da:Babu wanda zai cire sama da N100,000 a mako a tsakanin ɗaiɗaikun mutane, sannan N500,000 ga hukumomi in dai a cikin banki ne. Mai buƙatar cire sama da haka kuwa, za a dora masa harajin kaso biyar cikin 100 ga ɗaiɗaikun mutane, sannan kaso 10 ga hukumomi.
  • Wanda zai ciri kuɗi a asusun da ba nasa ba, ba zai iya cire kuɗin da suka haura N50,000 ba.
  • N100,000 kawai za a iya cirewa ta na’urar ATM a mako ɗaya, sannan N20,000 a rana ɗaya.
  • Daga kan N200 zuwa ƙasa za a riƙa lodawa a cikin na’urorin ATM.
  • N20,000 za a iya cirewa ta POS a rana ɗaya.
  • A duk lokacin da buƙatar cire kuɗi fiye da abin da aka ƙayyade ta taso, a nan, ɗaiɗaikun mutane na iya cire miliyan biyar a cikin wata ɗaya, sannan hukumomi su cire miliyan 10, tare kuma da biyan haraji kamar yadda aka nuna a ƙa’ida ta (1).