Samun man fetur a Arewa babbar nasara ce

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Na san ko ba duka ba, amma akasarin ‘yan Arewa sun shiga cikin murna da farin ciki, sakamakon gano man fetur da aka yi a Kolmani, wani ƙauye da ke iyakar Jihar Gombe da wani ɓangare na Jihar Bauchi. Ko da yake wasu ƙananan maganganu sun fara tasowa daga bakin wasu lauyoyi da ke Jihar Gombe suna ƙorafin cewa, yankin da ake magana a kai da ke kusa da samu man fetur bai shiga ƙauyen Barambu a ƙaramar hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi ba, yana cikin Gombe ne. Har ma sun yi barazanar shiga kotu don neman fassarar inda iyakokin jihohin biyu suka tsaya, domin tabbatar da ko Jihar Bauchi na da rabo a cikin wannan arzikin ƙasa da aka samu.

Ko da yake yanzu ba a kan wannan batu nake son yin sharhi ba. Amma dai abu ne da ya kamata a duba shi da kyau, kuma a ɗauki matakin warware shi tun da wuri, domin kuwa yana iya zama ƙalubale mai girma nan gaba. Sai dai kuma abin takaicin shi ne mu a Nijeriya ba a cika ɗaukar abu da muhimmanci ba, musamman a lokacin da yake farko farkonsa, sai ya ta’azzara har ya fara zama alaƙaƙai sannan a fara xaga hankali ana tunanin yadda za a shawo kansa. Kaico!

A cikin jawabin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022 lokacin ƙaddamar da fara aikin haƙar mai a wannan yanki na Arewa maso Gabashin Nijeriya ya bayyana cewa, duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fuskanta, da yadda farashin man fetur ke hawa da sauka a duniya, Nijeriya ta iya samun jarin Dalar Amurka Biliyan 3, da wasu kamfanonin ƙasashen waje suka saka a wannan aikin haqo mai a Arewa, abin da ya ce ba ƙaramin abin a yaba ba ne da ya kamata a jinjinawa wannan gwamnati mai ci.

Babu shakka kamar yadda ya faɗa abin jinjina ne sosai, kuma ya kamata Arewa da al’ummar ta su yi da gaske wajen tabbatar da ganin sun kare wannan dukiya da arzikin da Allah ya tabbatar musu da shi, bayan tsawon lokaci ana ta kwan gaba kwan baya a kan za a samu man ko ba za a samu ba. Har wani izgili ‘yan kudu suke yi wa Arewa bisa tunanin, aikin neman mai a Arewa, huhulahu ne! Amma daga lokacin da wata jarida a kudu Daily Times wasu shekaru can baya ta tava bugawa a kanunta cewa, The Mallams are coming! Wato ‘Yan Arewa na tafe. Ya tabbatar da cewa hasashen da ake yi fa zai iya zama gaskiya.

Alhamdulillahi, aikin haƙar mai a Arewa ya tabbata, sakamakon jajircewa, kishin cigaban Arewa, da aiki tuƙuru da aka yi, bayan miliyoyin Naira da aka zuba cikin wannan aikin. Wasu ‘yan Arewa ma da dama ba su san faɗi tashin da ake yi ba, sai labarin fara aiki kawai suka ji. Shi ma ɗin kuma sai ya gamu da halin mu na ‘yan Nijeriya, inda aka riƙa izgili da abin ana masa kallon tatsuniya ce! Abin da ba su sani ba shi ne kansu suke kwancewa zani a kasuwa.

Ko babu komai dai gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta cancanci a yaba mata, saboda hovvasan da ta nuna wajen tabbatar da ganin wannan mafarki da aka daɗe ana yi wa Arewa ya yi nasara, duk kuwa da ƙalubalen da aka riƙa fuskanta game da aikin. Yankin Arewa maso Gabas da yankin Arewa maso Tsakiya sun zama yankuna masu samar da ɗanyen man fetur, babban jigon da ke samar wa Nijeriya kuɗaɗen shiga, don tafiyar da manyan ayyuka da muhimman ayyukan gwamnati. Daga yanzu za a ƙara ganin kima da darajar Arewa da ‘yan Arewa don sun daina zama wa sauran yankunan Nijeriya kaska, ko cima zaune.

Domin sanin muhimmancin wannan aiki da tarihin gwagwarmayar da aka sha wajen neman inda za a samu man fetur a Arewa, na tattauna da wani masanin harkokin ma’adinan ƙasa da albarkatun man fetur, Malam Ibrahim Sabo wanda ya fayyace min yadda abin yake da nake. Muhimmancin abin ya sa ni ganin ya kamata in ɗan yi bayanin su kaɗan, ko jama’a za su yaba da abubuwan da Gwamnatin shugaba Buhari ta yi wa yankin Arewa a wannan ɓangaren.

Da wahala mai karatu ya fahimci haƙiƙanin yadda man fetir ke samuwa, har a kai ga amfanuwa da shi, ba tare da cikakkiyar shimfiɗa akan shi man fetir ɗin ba, inda ake samunsa, matakan da ake bi don tabbatar da samuwarsa, da kuma yadda ake kai wa ga amfana da shi. Duk waɗannan abubuwa mai ra’ayin sanin harkar da ta shafi man fetir na buƙatar sanin su saboda gujewa Molon ka wajen zayyana bayani.

Man Fetir, ɗaya ne daga cikin arzikin da Allah ya yi wa bayinsa a doron ƙasa, wanda ake samun sa cikin wasu nau’ikan duwatsu da ake kira a turance ‘Sedimentary Rocks’. Duk inda ka ji an samu man fetir a duniya to, daga waɗannan nau’in duwatsun ne, ko ya zama shi man ya yi tafiya daga cikin su zuwa ma’adanarsa wato abin da ake kira Reservoir a turance, kuma a kan samu wajen adanar tasa da ba a duwatsun da na yi bayanin su a baya ba, amma da matuƙar wuya don basu da yawa a duniya.

Bugu da ƙari, ba ko wanne irin nau’in dutsen Sedimentary ne yake iya samar da man fetir ba, dole wanda zai iya samar wa ya zama yana ɗauke da wasu sinadarai wanda asalin su daga ƙananan halittu ne, ko dai na ƙananan dabbobi ko kuma tsirrai, masu ɗauke da Sindarin Carbon da na Hydrogen, wanda wasun su da wahala ido ya iya ganin su, ba tare da an haɗa da taimakon na’urar microscope mai ƙara girman abubuwa ba.

Wannan dutse na Sedimentary na samuwa ne daga wasu duwatsun sakamakon farfashewa da suke yi, sai kuma ruwa, iska ko ƙanƙara mai tafiya su ɗauke su daga inda suka farfashe, su yi ta tafiya har su kaisu inda zasu ajiye su, sakamon ƙarfinsu na tafiya ya ragu, ko ya ƙare. Wannan waje da su ke zuwa su jibge waɗannan fasassun duwatsun su ake kira a turance ‘Basin’, wato kamar wata gaɓa ko wani rami da yake a waje mai gangara. Akwai wata hanyar ta daban da ake samun Duwatsun Sedimentary amma ba zai yiwu a kawo su duka a wannan taƙaitaccen rubutu ba.

A Nijeriya yankunan da suke da irin wannan bezin ɗin dake da tarin duwatsun Sedimentary, sun haɗa da Sakkwato, yankin Tafkin Chadi, Tudun Binuwai wanda ake kira Benue Trough, Bida a Jihar Neja, yankin Naija Delta da kuma ɓangaren Dahomey wanda ke yankin Jihar Legas.

Cikin waɗannan gaba ɗayansu, yankin Naija Delta ne kawai ke samar da man Fetir ga Nijeriya a halin yanzu, sai kuma ƙalilan daga yankin Dahomey. Yanzu kuma tafiya ta fara ƙarasowa Arewa.

Bayan samuwar duwatsun Sedimentary a waje to, akwai wasu ƙa’idoji da dole sai an same su sannan a fara batun yiwuwar samun mai ko rashin yiwuwarsa, da suka haɗa da dutse mai samar da mai, dutse mai rumbun ajiyar mai, dutse mai rufe saman rumbu saboda hana ficewar man ko asararsa, sai kuma tarkon da zai kame wannan man waje ɗaya a cikin rumbun dutsen.

A baya na ambaci wasu sinadarai da ake buƙata a dutse kafin ya zama zai iya samar da mai to, wannan dutsen idan aka yi dace bincike ya tabbatar cewa akwai waɗannan sinadaran na Carbon da Hydrogen ko daga ƙananan dabbobi ko kuma tsirrai to, za a ɗauke shi a matsayin dutse da zai iya samar da mai wanda ake kira a turance ‘Source Rock’, hakan kuma na yiwuwa ne kaɗai idan dusten ya binnu a can cikin ƙasa yadda zafin cikin ƙasar zai iya dafa shi ya matse shi da taimakon takurewar da ƙasar ta ke yi.

Wannan dutsen a Nijeriya shi ne ‘Shalle’, amma akan iya samun wani nau’in dutsen ya bada haka a wasu yankunan na duniya. A Naija Delta dutsen ‘Akata Shale’ shine ke samar da wannan man. Wani dutsen da ke ba da makamashi na iya samar da man fetir wani kuma iya iskar gas, wani kuma duka biyun.

To, bayan wannan sai kuma a samu wani dutsen da shi kuma aikin sa shine ya zama rumbun ajiyar wannan man da zai fito daga dutsen da aka dafa da zafin ƙarƙashin ƙasa, wannan dutsen kuma shi ake kira Rumbun Ajiyar Mai. Shi ma kuma yana da wasu ƙa’idoji da sai sun cika zai iya wannan aiki. Misali, na yankin Naija Delta shine Agbada, na yankin Gongola kuma a Arewa shi ne Dutsen Bima.

Dutsen ƙarshe shi ne zai yi rumfa wa wannan rumbun saboda adana mai daga tafiya zuwa sararin ƙasa, wanda hakan zai iya sawa a yi asararsa, ko kuma ya je ya haxe da ƙasa a rasa wasu sinadaran; hakan sai ya sa idan aka yi rashin sa’a sai man ya zama ya wofinta.

To, bayan haka a cikin kuma rumbun dole yanayi ya samu, wanda zai tattare man waje ɗaya, ya zama kamar jakar ajiya a cikin rumbun. Na san da yawan mutane suna tunanin mai a cikin ƙasa ne kamar yadda suke ganin rijiyar ruwa a gidajen su to, ba haka ba ne. Tamkar dai ka ce ruwa ne da ke naso a cikin soson katifa, wanda ke fita a hankali, lokacin da takura ta ragu ko aka huda shi.

Bayan mun kammala sanin ƙa’idojin da ake buƙata kafin a mayar da hankali a ko wanne waje don neman man fetir to, za mu yi duba kuma zuwa ga matakan da ake bi har a kai ga cin moriyar wannan mai ƙarƙashin haka akwai wasu matakai da za a iya kasa su gida uku. Na ɗaya, matakin binciken alamomin samuwar mai. Sai na biyu na tabbatar da samuwar man da kuma matakin fitar da mai don amfani da shi.

A matakin farko ana amfani ne da ilimin binciken ma’adinan ƙarƙashin ƙasa, don nazartar yanayin wajen daga kan duwatsu, samuwar rumbun ajiyar mai, yiwuwar samun jakar da ke ajiye da man, da kuma rumfar da za ta lulluve wannan yanayin. Daga nan sai wasu bincike da ake gudanarwa da ya shafi gutsuro wannan dutsen da ɗebo ƙasar wajen don gwajin ɗabi’arsa ta sinadarai, musamman inda aka samu yoyon mai daga rumbun ajiya saboda hujewar wannan rumfar da ta lulluɓe wannan yanayin da ke samar da mai.

To daɗi a kan haka, akwai wasu aune-aune da ake gabatarwa don a ga hoton cikin ƙasa, a samu ƙarin ƙarfin gwiwa na wajen da man ke kwance shi ma yana nan nau’i-nau’i, saboda taƙaitawa ba zan ambato su ba.

Bayan samun nasara da ƙarfin gwiwa a mataki na farko, mataki na biyu sai kuma a je ga tonon rijiya don tabbatar da samuwar abin da ake hasashe, domin gani ya kori ji. Nan ne za a ga shin akwai man? Shin menene yanayin man? Yaya yawan sa? Mene ne iyakarsa? Idan an fara ɗebowa kwalliya za ta biya kuɗin sabulu ko ɓata lokaci za a yi? Sannan yaya kyan man ya ke? Ya yanayin zafin ƙarƙashin ƙasar wajen ya ke? Mene ne ƙarfin takurar wajen ya ke, saboda kaucewa qarfin iska da ka iya fita ta haifar da asarar dukiya da rai? To, ƙarƙashin wannan ma akwai rijiyoyi da ake tono har matakai uku.

Da farko ana haƙa rijiyar bincike ta kintace, saboda babu tabbacin inda man yake. Cikinta kawai so ake aga shin da man nan a ƙasa? Wanne iri ne? Ya yanayin zafin wajen da takurarsa, wanne zurfi ne zai kai ga wannan rumbun ajiyar da sauran abubuwa da ake buƙatar sani na bincike. Sai kuma a kai ga rijiyar tantance yawan man, inda jakar shi take, da kuma sanin iyakarsa da kuma ƙididdige arzikin man bisa lura da kuɗin da za a kashe don devo shi, saboda kar ya zama asara ce za ta biyo baya.

Sannan akwai kuma rijiyoyi na ƙarshe wanda daga su ne ake fara ɗebo wannan man bayan an riga an san ina yake kwance. Wannan rijiyar ce ta ƙarshe a matakin neman mai, daga ita sai cin moriyar doguwar wahala da aka yi idan an dace da yawan man da kuma sauran ƙa’idojin.

A harkar binciken neman man fetir da ake yi a wannan yanki na Arewa, a baya an tona rijiyoyin neman mai kimanin guda 23, a yankin gavar Chadi ko a ce bezin ɗin Borno, inda ba a samu komai ba sai tarin iskar gas. Wannan bincike ya faru ne ƙarƙashin sashin masu kula da neman mai a yankunan da ake binciken mai, wanda a baya suke ƙarƙashin ma’aikatar NAPIMS na kamfanin albarkatun arzikin man fetir wato NNPC a yanzu.

Farfesa Nuhu George Obaje, wanda yake ƙwararre ne a ɓangaren nazarin yankuna masu yiwuwar samar da man fetir ya bayyana cewa, rijaya ta farko da aka fara tonawa a yankin Tudun Binuwai wato ‘Benue Trough’ wanda Bauchi da Gombe ke ƙarƙashinsa, kuma aka fi sani da ƙaramin bezin ɗin Gongola, ita ce rijiyar Rafin Kolmani ta ɗaya wacce kamfanin mai na Shell Nigeria Exploration and Production Company (SNEPCO) suka yi a shekarar 1999. Zurfin ta ya kai kimanin mitoci dubu uku ba a samu komai a rijiyar ba sai tarin iskar gas da ya kai dunqulen kafa Biliyan 33 da kuma mai ɗan kaɗan. Wannna ita ce kaɗai rijiyar da wannan kamfani na SNEPCO ya tona a yankin Gongola.

Sauran Rijiyoyi biyu da aka tona a wannan yanki na Gongola sun haɗa da Kuzari ta farko da Nasara ta farko, wanda kamfanin mai na Elf Petroleum Nigeria Limited (TotalFinaElf) ya tona, su ma a shekara ta 1999, masu kimanin zurfin mitoci 1,666, sai kuma wanda kamfanin mai na Chevron su ma suka yi cikin shekara ta 2000 wanda ta kai zurfin mitoci 1,500, duk waɗannan rijiyoyi ba a yi nasarar samun komai a cikinsu ba na mai.

Sai dai masana a wannan fannin na harkar neman albarkatun mai sun bayyana cewa ya kamata zurfin rijiyoyin ya fi haka yawa saboda ta iya yiwuwa ba a kai inda man yake ba, saboda sau tari dama sai an tarar da iskar gas, wacce ke zama kamar hula a saman mai sannan gaba da ita a samu man ko kuma in babu a rasa.

Saboda taimakon sabbin dabarun fasahar zamani kan aikin gudanar da binciken neman mai irin su 3D seismic wato hoton ƙarƙashin ƙasa da ake samarwa ta hanyar amfani da gudun ƙara don bambance ɗabi’un abubuwan da ke ƙarƙashin ƙasa (kamar dutse, iska da ruwa), da wasu fasahohin kuma, sai a shekarar 2019 ne shugaban qasa Muhammadu Buhari a ranar 2 ga watan Fabrairu ya ƙaddamar da fara aikin tonon rijiyar Kolmani ta biyu wacce ke kusa da ƙauyen Barambu da ke ƙaramar hukumar Alƙaleri a Jihar Bauchi, kuma an tona wannan rijiya ne zuwa zurfin mitoci 4,110, wanda kun lura akwai bambamcin mitoci dubu tsakanin wannan rijiya da kuma rijiya mafi zurfi da aka tona a baya.

A wannan rijiya ne aka tabbatar da samuwar mai a yankin Arewacin Nijeriya, kuma ita wannan rijiya ta Kolmani ta 2, ita ta kawo ƙarshen hasashe da kai ruwa rana da ake da wasu da basu yarda da yiwuwar za a iya samun man fetur a Arewa ba.