Sai yaushe ‘ya’yan Arewacin Nijeriya za su daina nuna halin ko-in-kula ga mahaifiyarsu?

Daga MUHAMMAD NASEER LERE

Allah Sarki. Daga zuciyata nake burin ina ma abinda nake saƙawa mafarki ne ko hasashe. Cikin sauri nayi firgigif nace in da mafarki ne da nayi burin farkawa daga wannan mummunan barci, inda kuma hasashe ne da na la’anci wannan kimiyya. Amma sai dai lamarin na kama da gaskiya a dukkan alamu na zahiri da ƙwaƙwalwa ke iya taskancewa.

Me Ya Samu Mahaifiyarmu Arewa?

Yanki me yalwar arziki, yankin da yake sheƙi da ganyayen amfani gona masu albarka. Ko Birtaniya ta san ana noma masara da dawa a cikin mahaifarmu. Hatta ƙasashen irin su Chana sun san, ana ƙera fartanya da garma a Arewa. Haba dai, ai kowa ya san yankinmu ya yi ficen haifar da kayan abincin da fes zai iya ciyar da nahiyar Turai. Babu ma wanda zai yi kuskuren nuna mana an yatsa a fannin arzƙin noma tun ba yau ba. In ma dai za a ce an fi mu, to ba mara kunyar da zai ce ba mu iya ba.

Yankin da ya yi fice wajen soyayya da haɗin kai, haɗinkan da ya samar da Hausa/Fulani. Soyayyar da ta ba wa inyamuri damar gina shago da gida a Kaduna da Katsina. Me ya samu wannan kyakkyawar aqiba da nasaba, me ya samu wannan kyakkyawar fahimta abin koyi ga sauran yankuna? Me ya samu al’ummar wannan yanki mai albarka har ake musu kisan ƙare dangi, me ya samu wannan gado me armashi, kwarjini da daɗin labartawa ne? Ko dai ‘ya’yan Arewa sun mance da asalin uwarsu ne kam.

Na san ko lokacin da aka fafata rikicin Reinhard bonnke, da ya jawo kashe rayuwar sama da mutum 200 a Kano ranar 19 zuwa 20 ga watan Oktoban shekarar 1991, ba wanda zai yi tsammanin akwai ranar da zata zo da kullum sai an kashe rai a Arewa ba tare da an Arewan ya ji ko gezau ba. Balle har a yi tunanin Arewa za ta iya zama gidan kashe kai da kai. Za a ce, wai shin yanzu ne a fara kashe-kashe a Arewa?

Tabbas ba yanzu ba ne, amma shin lokacin rikicin (Abbatoir) na 1991, da aka kashe sama da mutum 1000 haka kowa ya zauna babu jimami? Duk da cewa za mu iya cewa wannan rikici ne na addini tsakanin Musulmi da Kiristoci, wanda tsautsayin ya afku a kan mayanka (Abbatoir) da tasirin rikicin har ya shiga garin Bauchi, In da kafin a ankara a shawo kan rikicin, sai da sama da mutum 1000 suka rasa rayukansu. Za ku iya tuna irin firgicin da Arewa ta shiga lokacin?

Yanzu dai a cikin wata guda ana iya kawo ƙarshen numfashin ‘yan Arewa 1000 ba tare da an dakatar haska film din labarina ko kwana casa’in ba. Masifar ta kai ga, cikin teburin me shayi za ka ji an ce “Jiya ‘yan bindiga sun kashe mutum 30 a wani ƙauye” me shayin zai cigaba da haɗa shayinsa ya yi addu’ar sauƙi, shi kuma mai ba da labarin zai karqare labarin da “A fasa min ƙwai guda uku” shikenan labarin ya zo ƙarshe a gurin. In ba sa’a ba, daga gurin zai wuce gidan sinima ya kalli ƙwallo. Da zurawa kulob ɗinsa, da kashe ‘yan yankinsa baƙin cikin zai iya zuwa kan-kan-kan idan ma cinsa ƙwallon bai zarce ba.

Waɗanda aka kashe idan ƙila suna Zamfara, Sokoto ne ko Kaduna, babu ruwansa. Waɗanda aka kashe ɗin nan qila fa suna da iyalai, ko a gyalensa. Waɗanda aka kashe ɗin nan lila suna da mata, biyu ko uku, babu ruwansa. To ina ruwansa tunda shi nasa matan suna lafiya. Idan na ce an ci Arewa da yaƙi bana jin akwai wanda zai ce na yi kalmar banza, saboda wannan bayyanannen zahiri ne da zai iya bayyana a iya ido kawai, ba sai an saka ƙwaƙwalwa an yi tunani ba. Hakan na nufin ko mahaukaci zai iya kiyaye irin mugun yanayin da Arewa ke ciki.

Wani abin haushin musamman kwanakin nan, ko kafafen labari sun daina wallafa ta’addancin da ake tafka mana. Sai wasu suka ɗauka kamar an samu tsaron da ake iƙrari ne, alhalin ana nan dai jiya i yau. Wannan lamari da ban mamaki yake haƙiƙa, ba so nake nace an siyasantar da Arewa ba, amma ba zan hana kowa wannan tsarkakakken tunanin ba. Domin wataƙila hakan na iya zama gaskiya. Ƙila mu ‘yan ƙauye za mu ce yanzu fa uwarmu tana zaune lafiya, saboda haka, za mu iya jefa ƙuri’a gidan jiya cikin salama.

Wannan lamarin fa wallahi ya fi na jiya muni, daga lokacin da aka fara kashe rai ana nuna rashin damuwa, daga lokacin an kai ƙololuwa na dukkan ha’ula’i. Wannan shi ne babban lasirin ƙara taɓarɓarewar Mahaifiya Arewa. Ko kuna ganin duk wanda za a msri uwarsa ya kasa yin komai ɗan arziki ne? Ko da baya iya motsa gaɓɓai duka, ko a fuska ya kamata ya nuna rashin jin daɗin marin mahaifiyarsa. Idan kuma yana da iko, ya kamata ya rasa hankalinsa wajen nuna daraja da ƙimarta. Ko da kuwa hakan zai kusanto da ajalinsa, a sannan ne zai zama yaron kirki.

Amma ku duba, an zagi mahaifiyarmu (Arewa), Hakan bai isa ba, an zubar da ƙimarta, an tozarta ta, an ƙasƙanta ta. Duk wannan abu ne wanda uwa za ta iya jurewa. Amma ta yaya ‘ya’ya za su jure ganin zubar da jinin mahaifiyarsu? Yau ga shi muna ganin yadda ake zubar da jinin Mahaifarmu, ana yage ‘ya’yanta a nono ana kashewa, ana cire zanen ɗiyarta ana yin fyaɗe, haƙiƙa Arewarmu na ganin masifa da bala’i. Ga ‘ya’yanta sun shagala da halin da take ciki. Ni dai ban san, ko akwai hanyar da ɗan arziki zai shagala da tunawa da halin da uwarsa ke ciki ba.

Ko ɗaya ba na nufin wai ‘yan Arewa sun zama ‘ya’yan banza a idon mahaifiyarsu Arewa. Sai dai ba sai nace sun gaza sauke hakkinta ba, duk mun san cewa mun gaza hakan. Yau idan za a kashe mutum 4 a Borno, wajibin ɗan Kano ne ya tashi takanas ta Kano ya je ya yi ta’aziyya, ina nufin inda a ce uwa muka ɗauki Arewan. Amma yau za a tashi ƙauye 3 a ƙaramar hukumar Giwa ba tare da ɗan cikin ƙaramar hukumar Soba, ko Lere ya ji gezau ba. In ma ya firgita, to ba tsoro ne ba na tausayi ba. Ina kuma a ce ya tura wa da ƙauyen tallafin kayan sakawa tun da an ƙona musu har takalma.

Ba wai ina maganar damuwa da ‘yan Arewan da ake musu kisan gilla a kudancin ƙasar ba ne. Ba wai ina son cewa me yabsa ba a damu da irin ɓarnar da ake yi wa Arewa a yankuna irinsu Ilori ba ne. Takaicin shi ne, abin da zai ɗiga ayar tambaya ga masu kallon gilmawar cigaban Arewa shi ne; in dai za a kashe ɗan Kaduna ɗan Kano bai rikirkice ba, ko kuma a kashe ɗan Kano ɗan Jigawa bai ruɗe ba, ko kuma dai zaftare yankunan Sokoto da Zamfara ba tare da ɗan Gombe ya ji gezau ba, to wa zai tsammaci wani zai damu da kashe ɗan Arewa a kudu? Wataƙila za ku ce ai ana damuwa, amma ku fara kawo wani iyali guda da ta’addanci ya rutsa da su da suke rayuwa me kyau. Muna ganin su a gidajen talabijin suna roƙon na ƙoƙo.

Wannan mummunan sakamakon da mahaifiyarmu (Arewa) ta samu, daga ina ta yi gadonsa ne kam? Mu dai mun karanta jiyanta babu abinda muka riska wanda ya yi kama da wannan. Duk wata lalacewa, ko wata musiba idan ta zo tare ake shanyeta, ko me kyau ko mummuna. Amma yanzu ƙuru-ƙuru rashin damuwa da halin da kowannenmu ke ciki ya zama jikinmu. Menene ya bambanta jiyan Arewa da yau ɗin ta? Sai nake tunanin ko wancan lokacin don saboda Arewa tana da; Shugaban ƙasa, Ministan harkokin tsaro, Janar ɗin Soji, komishinan ‘Yansanda, da sauran muƙamai ne. Ko da na dawo daga hayyacina, sai na fahimci ashe yanzu ma Arewan tana da duk abubuwan da na lissafo. Malam ba dole ma a rikirkice ba?1

Yanzu lokacin zave ya kunno kai, lokacin da Arewa ke tsammanin samun ‘yancin renon ‘ya’yanta cikin salama. Amma tun yanzu har ta fara zubda hawayen baƙin ciki, tare janyewa daga tsammanin da take ciki. E mana. Don Allah ta yaya za ka zo gurin Uwar da ake kashe ‘ya’yanta ka zo kana tiƙa rawa? So take ka faɗa mata tsare-tsaren da kake dashi na kiyaye zubar jinin iyalinta. Amma ka zo neman ƙuri’unta a maimakon ka lallashe ta, kawai ka kwale ana zuba maka baiti kana taka rawa cikin nishadi. Har ya manta a inda yake ake farautar bani Adam a kashe.

Akwai gyara a al’amuran nan. Arewa yanzu cike take da kukan marayu, ko sau ɗaya ban ga masu tseren neman mulkin ƙasar nan riƙe da wani maraya hannunsu da zimmar tausasa zuciyar uwar marayan ba. Ko baku lura ba, idan sun je kudanci sai sun zauna sun nuna abubuwan da za su yi wa kudancin idan sun lashe zaɓen. Kuma sharaɗi ne duk alƙawuran da za su yi ya zama ya yi kusa da hankali, ba abubuwan da daga ji kasan tatsuniya ce ba. Amma idan an zo neman quri’armu, sai a taru a yi casu kawai a watse. Haba! Ta bakin Hausawa, mun koma ‘ya’yan kishiya kenan!

Wannan lamari da baƙanta zuciya yake. Ina maganar hanyoyinmu da za a gyara? Wannan yawan rasa rayuka da ake ta sanadin haɗarin mota shi ma ya ƙara yawaita. Yanzu ka ji an ce an rasa rayuka 30 ko 20 sanadiyyar haɗari abu ne mai sauki. Haɗarin na faruwa ne sakamakon kasa gyara hanyoyin da kakanni suka samar. Har yanzu dai muna walagigi ne, amma zahirin wanda za mu amince wa kaso 80% ya gagara samuwa har yanzu. Wannan na biyo bayan rashin samun damar ganawa da mu ne da ba a yi. Kodayake wa zai so fuskantar ‘yan ta’adda gaba-da-gaba, da gaskiyarsu ai. Amma idan za a kama ƙaton ɗakin taro, a kirawo masu waƙa, a yi nishaɗi duk abu ne mai sauƙi. Kodayake kun san fa rayuwa sai da nishaɗi.

Kada wani ya ce nace a daina nishaɗi, ina! Rayuwa ai dole sai da nishadi. Amma mu har yanzu ba mu da lokacin nishaɗi a magana ta hankali. Domin ko ka kunna mana sauti babu abinda kunnuwanmu za su ji sai karar bindigu da kukan marayu. A maimakon mu taka mu yi rawa, sai dai mu taka da gudu saboda mugun firgicin da muke ciki. Ko kaɗan ba mu cancanci waɗanda za su zauna cikin hayyacinsu ba. Amma duk da haka, ba za mu iya haɗuwa waje guda mu ce e ko a’a ba. Kai ka ce mugun aiki muka aikata da muke fuskantar wannan masifa.

Yanzu ya rage namu, za mu ci gaba da zama teburin mai shayi muna hirar kashe ‘yan uwanmu ne, ko kuma kuka za mu yi ta shirgawa har sai labarin ya canza. Yanzu ya rage mana, ‘yan siyasa za su cigaba da zuwa suna ɗibar shoki da rawar Buga a gaban Uwarmu ne, ko kuma za mu kama hannunsu ne mu kai su gaban iyayen da aka kashe ‘ya’yansu, da kuma ‘ya’yan da aka yanka iyayensu a kan idon su? Wanna zaɓi ne na ni (Mai rubutu) da kuma kai (Mai Karatu). Ko dai mu ɗauki matakin sulhu da mahaifiyarmu Arewa mu zama ‘ya’yan arziƙi, ko mu zama akasin arziki a gare ta. Idan mun ɗinke guri ɗaya, mun fuskanci ciwukanmu, mun zama ‘ya’yan albarka ga uwa ɗaya, shikenan mun samu bakin zaren matsalarmu.

Allah ya cigaba da kariya ga Mahaifiya wacca ta haife mu Arewa, Uwa wacce ta ba mu harsuna, ta bamu al’adar Hausa da Fulani. Wacce ta ba wa iyaye da kakanninmu iskar shaƙa da kyakkyawan yanayi mai albarka, sannan ta shayar da su tarbiya daga rumbun su Shehu Ɗan Fodiyo. Muna rokon Allah ya tozarta duk mai burin ganin rugujewar mahaifiyarmu. Allah ya nuna wa duk mai burin durƙushewar Uwarmu Arewa, Allah ya tabbatar da cigabanta da bunƙasarta, Ameen.