Ganduje zai rufe bankuna uku a Kano saboda rashin biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin mulkin Abdullahi Umar Ganduje, ta ba da wa’adin makwanni biyu kacal ga bankunan kasuwanci da suke a Kano domin su biya bashin harajin rajistar kasuwancinsu ko kuma gwamnati ta garƙame bankunan. 

Bankuna da gwamnatin take yi wa sharaɗin dai su ne, First Bank, Ecobank da kuma Unity Bank.

An gurfanar da bankunan uku a wata kotun tafi-da-gidanka wacce take gudanar da Shari’a a ƙarƙashin Babban Majistare Ibrahim Gwadabe.

A zaman kotun na ranar Alhamis ɗin da ta gabata a jihar Kano ne dai kotun ta gurfanar da bankunan inda ta tuhume su da laifin ƙin biyan haraji ga gwamnatin jihar Kano. Sannan ta umarce su da su biya kuɗin da ake bin su bashi ga ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da kuma ma’adanai ta jihar Kano. 

A cewar alƙalin kotun, laifin da bankunan suka aikata ya sava da dokar sashe na 8 da na 9, sannan hukuncin wanda ya saɓa waccan dokar yana cikin sashe na 14 na dokar kasuwanci ta shekarar 2014, dukkan a kundin tsarin mulkin Kano.

Jami’ar yaɗa labarai ta ma’aikatar kasuwancin ta jihar Kano, Sa’adatu Sulaiman, ta bayyana cewa, Alƙalin kotun ya bai wa bankunan wa’adin tsahon makwanni biyu su biya kuɗaɗen da ake bin su ko su fuskanci kulle wuraren sana’arsu har sai sun biya waɗancan kuɗaɗe.

Idan za a iya tunawa, a bara ma hukumar tattara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta garqame sassa biyar na bankin Guaranty Trust Bank a Kano saboda rashin biyan haraji ga gwamnatin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *