Kasuwanci

Majalisar Dattawa ta sake bai wa CBN umarnin ƙara wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira

Majalisar Dattawa ta sake bai wa CBN umarnin ƙara wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta sake umartar Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya gaggauta ƙara wa'adin daina karɓar tsoffin takardun Naira ya zuwa 31 ga Yuli, 2023. A ranar 15 ga Disamban da ya gabata CBN ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira na N200, N500 da kuma N1000, inda ya tsayar da 31 ga Janairu a matsayin lokacin da za a daina amfani da tsoffin takardun Naira da aka canza. Idan dai za a iya tunawa, a Disamba, 2022 Majalisar Dattawa ta bai wa CBN umarnin tsawaita wa'adin daina karɓar tsoffin takardun Naira, amma bankin ya yi biris da…
Read More
CBN ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 16

CBN ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 16

Daga BASHIR ISAH Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ba da sanarwar ƙarin kuɗin ruwa daga kashi 11.5 a bara zuwa kashi 16.5. A ranar Talata Emefiele ya ba da sanarwar haka a Abuja. Da ma dai CBN, ƙarƙashin kwamitinsa na dokar hada-hadar kuɗaɗe ya kaɗa ƙuri'ar neman ƙara kuɗin ruwan zuwa kashi 17.5.
Read More
CBN ya haramta wa masu POS canjin sabbin kuɗi a Abuja da Legas

CBN ya haramta wa masu POS canjin sabbin kuɗi a Abuja da Legas

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya haramta wa masu POS a Abuja da Legas harkar musayar sabbin takardun Naira da tsoffi. Cikin sanarwar da ya fitar, CBN ya zayyana wasu ƙa'idoji game da shirin musayar sabbin kuɗin don waɗanda aka sahale wa su kiyaye. Sanarwar ta nuna wasu bankuna biyar kaɗai aka amince wa gudanar da wannan shiri, wato Access Bank Plc, Zenith Bank Plc, United Bank for Africa Plc, First Bank sai kuma First City Monument Bank. “Ba duka ejent za su shiga shirin ba, sai wasu zaɓaɓɓu waɗanda aka miƙa bayanansu ga CBN da kuma bankunan…
Read More
Abdulsamad Rabiu ya shiga sahun mutane huɗu mafiya arziki a Afirka

Abdulsamad Rabiu ya shiga sahun mutane huɗu mafiya arziki a Afirka

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai sakamakon rahoton jaridar tattalin arziki ta Forbes ya bayyana AbdusSamad Isyaku Rabiu a matsayin mutum na 4 a jerin mutane mafiya arziki a Afirka. Wato ya ture Attajirin nan na ƙasar Masar, Nassef Sawiris, wanda a da shi ne mutum na huɗu mafi arziki a Duniya. Da ma a watannin da ba su wuce biyu baya ba, AbdusSamad Rabi'u wanda shi ne mallakinta rukunin kamfanonin BUA ya samu muƙamin mutum na biyu mafi arziki a Nijeriya bayan ya kere Attajirin da yake gabansa a arziki wato, Mike Adenuga. Jaridar Forbes ita ta…
Read More
Wa’adin tsofaffin takardun kuɗi: CBN ya ce mutanen karkara kada su damu

Wa’adin tsofaffin takardun kuɗi: CBN ya ce mutanen karkara kada su damu

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya, CBN a ranar Juma'a a garin Abuja ya bayyana cewa, mutanen karkara su sha kuruminsu game da batun samun sababbin kuɗin kafin nan da 31 ga watan Janairu da tsofaffin za su tashi daga aiki. Domin kuwa an riga an yi musu tanadin da ya kamata. A cewar Bankin, zai ƙaddamar da shirin canjin kuɗin a ƙauyuka da sauran wuraren da suka kamata a faɗin ƙasar nan daga ranar Litinin don bunƙasa amsar sababbin takardun kuɗin. Ya ƙara da cewa, za a yi wannan ƙaddamarwar ne don bunƙasa hanyoyin da mutanen karkara za…
Read More
Nijeriya ta fi dukkan Afirka shigo da janareto – Bincike

Nijeriya ta fi dukkan Afirka shigo da janareto – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI Wani sakamakon bincike da Hukumar Sabunta Makamashi Ta Duniya  (IRENA) ta gudanar ya bayyana cewa, Nijeriya ita ce jagaba wajen shigo da injin janareto a faɗin ƙasashen Afirka gabaɗaya.  Rahoton mai taken ECN ya bayyana dalilan da suka sanya 'yan Nijeriya suka dogara matuƙar dogara da janareto da kuma illarsa ga tattalin arzikin ƙasar da sana'o'i.  Sana'o'i da gidaje da dama a ƙasar sun dogara ne kacokan a kan injinan janareto don samun wuta saboda ƙarancin wutar lantarki a ƙasar.  Saboda haka, rashin isasshen sinadarin gas, tangarɗar na'urori da rashin wadatar tashoshin wutar su na daga…
Read More
Bankuna za su fara aiki ranar Asabar don canza tsofaffin kuɗaɗen masu ajiya – CBN

Bankuna za su fara aiki ranar Asabar don canza tsofaffin kuɗaɗen masu ajiya – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya, CBN ya bayyana cewa, bankuna za su dinga aiki a ranakun Asabar don samun damar canza wa masu ajiyarsu tsofaffin kuɗaɗensu zuwa sababbi. Kama Ukpai, shugaban tawagar CBN ta jihar Ebonyi a kan sababbin takardun Naira, shi ya bayyana hakan ranar Juma'ar da ta gabata a yayin gangamin wayar da kai ga 'yan kasuwa a kasuwar Eke dake Afikpo. Mista Ukpai ya shawarci al'umma da su ziyarci bankuna su ajiye tsofaffin kuɗaɗensu a canza musu da sababbi. Domin kuwa a cewar sa, babu gudu ba ja da baya wajen tabbatar da daina amsar…
Read More
Shirin Bankin Access na mallakar Bankin Sidian ya gamu da tazgaro

Shirin Bankin Access na mallakar Bankin Sidian ya gamu da tazgaro

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai yunƙurin da bankin Access yake yi na ƙoƙarin mallakar Bankin Sidian wanda babbar shalkwatarsa take a jihar Kenya ya haɗu da tazgaro, inji Bankin na Access a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata. Bankin ya ƙara da cewa, Wannan yarjejeniyar cinikayyar da aka ƙulla kusan watanni shida da suka wuce da za ta ba shi damar mallakar Bankin Sidian ɗin ta rushe. Don haka, ba za a cigaba da maganar ba. Bankin Access ya yi niyyar sayen kaso 83.4 na Banki Sidian da yake a Afirka ta Yamma. Tun a farkon…
Read More
CBN ya yi barazanar takunkumi ga bankunan dake raba tsofaffin takardun kuɗi

CBN ya yi barazanar takunkumi ga bankunan dake raba tsofaffin takardun kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sha alwashin hukunta bankunan da ke ci gaba da cika na’urorinsu na ATM da tsofaffin takardun kuɗi na Naira, a daidai lokacin da wa’adin cire kuɗaɗen ya gabato. Daraktan Sashen Kula da Harkokin Shari’a na CBN, Kofo Salam-Alada, wanda ya bayyana haka a wani taron wayar da kan jama’a a ranar Laraba 18 ga watan Janairu, 2023, a Kasuwar Computer Village da ke Legas, ya ce bankin ƙoli ya riga ya sanya ido ga bankuna kan lamarin. Daraktan wanda ya wakilci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babban bankin na da…
Read More
Netflix ya tafka asarar miliyan N250 saboda dakatar da amfani da ‘Naira Card’ da bankuna suka yi

Netflix ya tafka asarar miliyan N250 saboda dakatar da amfani da ‘Naira Card’ da bankuna suka yi

Daga WAKILINMU Kamfanin Netflix ya ce ya rasa mabiya 39,451 cikin kwana 40 a Nijeriya sakamakon daina amfani da katin hada-hadar kuɗi na 'Naira Card' da bankuna suka yi a kasar. Bayanan da jaridar News Point Nigeria ta tattara ranar Talata su nuna cewa, kimanin 'yan Nijeriya mabiya shafin kamfani su 39,000 ba su sabunta rijistarsu da kafar ba a tsakanin kwana 40 da suka shuɗe. Jaridar ta ƙara da cewa, bayanan da ta samu ɗin ba su nuna yadda tsarin yake dalla-dalla ba, kawai dai an hasashen cewa asarar ta kai ta sama da Naira miliyan 250. News Point…
Read More