Kasuwanci

Bankin UBA zai fara harkokinsa a ƙasar Dubai

Bankin UBA zai fara harkokinsa a ƙasar Dubai

Daga AMINA YUSUF ALI Bankin UBA ya faɗaɗa harkokinsa, inda har yanzu haka ya bude sabon reshensa a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (Dubai). Shi dai wannan reshe na UBA an buɗe shi ne a cibiyar hada-hadar kuɗin ta qasar Dubai (DIFC). Sannan ya samu lasisin fara hada-hadar sa, kuma humakar saita al'amuran kuɗin na Dubai (DFSA), shi zai cigaba da gudanar da da al'amuran bankin. Wannan faɗaɗa harkokinsa da bankin UBA ya yi ana ganin zai qara sa wa ya samu qarin damarmaki a gabas ta tsakiya, Afirka, da Asiya ta kudu, wanda ya ƙunshi ƙassashe 72 tare da ƙiyasin alumma…
Read More
SON ta haɗa kai da Kwastam don yaƙar shigo da kaya marasa inganci

SON ta haɗa kai da Kwastam don yaƙar shigo da kaya marasa inganci

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tabbatar da ingancin kaya ta Nijeriya (SON), sun haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastam) domin yaƙar shigo da kayayyaki marasa inganci cikin ƙasar nan. Darakta janar na hukumar SON, Mallam Farouk Salim, a yayin wata ziyara da kai zuwa Shalkwatar Kwastam a Abuja, ya jaddada irin muhimmiyar rawar da hukumar ta Kwastam take takawa a wajen yaƙi da shigo da kayayyaki marasa inganci a Nijeriya. Hakazalika, Mista Salim ya nuna yabawarsa ga irin gudunmawar da jami'an hukumar suka ba hukumarsu a baya, kuma suna sa ran su yi musu abinda ya…
Read More
Buhari ya ƙara farashin fetur zuwa N179 a asirce

Buhari ya ƙara farashin fetur zuwa N179 a asirce

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi ƙarin kuɗin fetur ba tare da sanarwa ba, inda a yanzu ta amince a sayar da lita ɗaya na fetur a kan N179 maimakon N165 da aka sani a baya. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da kamfanin mai na NNPC Limited ya miƙa wa dillalan mai tare umartan su a kan su sauya nasu farashin daga yau Talata, 19 ga Yuli, 2022. Wannan na zuwa ne bayan da matsalar ƙarancin fetur ta sake kunno kai a ƙasar wanda hakan ya sanya 'yan kasuwar mai ɗin ke ta sayar da…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da sabon kamfanin NNPC bayan sauya masa fasali

Buhari ya ƙaddamar da sabon kamfanin NNPC bayan sauya masa fasali

Daga BASHIR ISAH A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da sabon Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPC Limited), wanda hakan ya sauya wa kamfanin fasalin gudanarwa daga ƙarƙashin gwamnati zuwa ƙarƙashin 'yan kasuwa wanda zai ci gaba da gudana ta hanyar hannun jari. Wannan na nufin kamfani NNPC Limited zai ci gaba da gudana ne a matsayin mai zaman kansa amma ba na gwamnati ba kamar yadda aka sani. Da yake jawabi yayin taron ƙaddamarwar Shugaba Buhari ya ce, "Mun sauya fasalin kamfanin fetur ɗinmu ne a yau 19 ga Yulin 2022 domin ƙarfafa shi. “Daga yanzu NNPC…
Read More
Haraji: Gwamnatin Ebonyi ta garƙame reshen Bankin GT a Abakaliki

Haraji: Gwamnatin Ebonyi ta garƙame reshen Bankin GT a Abakaliki

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin jihar Ebonyi ta garƙame reshen Bankin GT na garin Abakaliki babban birnin jihar sakamakon rashin biyan haraji. Gwamnatin ta bayyana cewa, ta kulle bankin ne sakamakon qin biyan haraji ga gwamnatin jihar Ebonyi. Kuma ta sha alwashin za ta cigaba da kulle shin har sai ya biya harajin da ake bin sa. Tawagar masu ruwa da tsaki na ofishin hukumar tattara haraji ta jihar sun ziyarci bankin a safiyar ranar Talatar da ta wuce sannan suka ba da umarnin kulle shi a nan take. Shugaban tawagar, Okoro Celestine, wanda shi ne shugaban hadaɗɗiyar hukumar tattara…
Read More
Me ya sa jami’in kuɗin kamfanin sumuntin Ɗangote yin murabus?

Me ya sa jami’in kuɗin kamfanin sumuntin Ɗangote yin murabus?

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai Babban jami'in kula da harkokin kuɗi a kamfanin sumuntin Ɗangote ya yi murabus daga muƙaminsa a kamfanin.  A ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne dai Kamfanin sumuntin na Ɗangoten ya ba da rahoton barin aikin da babban jami'in kuɗin na kamfanin, Mista Guillaume Moyen, ya yi.  Kamfanin ya bayar da sanarwar ne a yayin ganawa da hukumar canjin kuɗin ta Nijeriya. Inda ya bayyana cewa, Mista Moyen ya bar muƙaminsa ne, don ra'ayinsa na ƙashin kai kuma ya yi ne a ranar 30 ga watan Yunin 2022.  Hakazalika, kamfanin ya…
Read More
Abinda ya sa kamfanin Shell ya fasa sayar da kadarorinsa na Nijeriya

Abinda ya sa kamfanin Shell ya fasa sayar da kadarorinsa na Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin mai na Shell ya fasa sayar da kadarorisa wato gine-gine sa da kayan aiki da yake da su a ƙasar nan. Hakan ya biyo bayan bin umarnin kotun ƙolin da kamfanin ya yi bayan da mazauna garin Bayelsa suka  ɗaukaka ƙara a kan kamfanin.  Babban kamfanin man ya bayyanana daina harkokin kasuwancinsa a Nijeriya a watan Mayun 2021. Daga bisani kuma al'ummar yankin Aghoro ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa ta shigar da kamfanin ƙara  kan a biya su diyyar ɓarnar da yoyon fayif ɗin man kamfanin ya jawo wa al'ummar garin wanda ya faru ranar…
Read More
Bankuna sun nemi masu neman canji su fara bin layi wata guda kafin buƙata

Bankuna sun nemi masu neman canji su fara bin layi wata guda kafin buƙata

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da canjin kuɗaɗen ƙasar waje suka yi matuƙar wahalar gaske, Bankuna sun umarci masu neman sayen kuɗaɗen ƙasar wajen da su fara bin layin neman kuɗin tun wata guda gabanin lokacin da za su yi amfani da kuɗin.  Bankuna sun ba da sanarwar tun a watan Mayun shekarar nan da muke ciki ta 2022. Bayan da wasu ɗalibai da kuma 'yan kasuwa suka yi ta ƙorafin yadda aka ja dogon lokaci kafin su samu canjin kuɗaɗen duk kuwa da sun cika dukkan sharuɗɗan da suka kamata.  A wata wasiƙa da wata majiya ta bayyana…
Read More
Ganduje zai rufe bankuna uku a Kano saboda rashin biyan haraji

Ganduje zai rufe bankuna uku a Kano saboda rashin biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin mulkin Abdullahi Umar Ganduje, ta ba da wa'adin makwanni biyu kacal ga bankunan kasuwanci da suke a Kano domin su biya bashin harajin rajistar kasuwancinsu ko kuma gwamnati ta garƙame bankunan.  Bankuna da gwamnatin take yi wa sharaɗin dai su ne, First Bank, Ecobank da kuma Unity Bank. An gurfanar da bankunan uku a wata kotun tafi-da-gidanka wacce take gudanar da Shari'a a ƙarƙashin Babban Majistare Ibrahim Gwadabe. A zaman kotun na ranar Alhamis ɗin da ta gabata a jihar Kano ne dai kotun ta gurfanar da bankunan inda ta tuhume su…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta amshe ragamar tafiyar da filayen jiragen sama daga jihohi

Gwamnatin Tarayya za ta amshe ragamar tafiyar da filayen jiragen sama daga jihohi

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Tarayya ta bayyana ƙudurinta na amshe ragamar tafiyar da harkar sufurin wasu filayen jiragen sama daga hannun gwamnatocin jihohi. Hadi Sirika, Ministan harkar sufurin jiragen sama, shi ya bayyana haka a yayin taron ƙara wa juna sani na hukumar sufuri a sararin samaniya (FAAN) wanda aka gudanar a Abuja. A cewar Sirika, filayen jiragen saman da gwamnatin Tarayyar za ta ƙwace su ne, na jihohin; Kebbi, Jigawa (Dutse), Bauchi da kuma Gombe. Sannan ya ƙara da cewa, da yawa ma daga filayen jiragen saman da suke mallakin jihohi a Nijeriya za a amshe su daga…
Read More