27
Jun
Daga AMINA YUSUF ALI A kwanakin nan ne dai wani kamfanin mai na asalin Nijeriya mai suna MOAHZ Oil and Gas, Wanda ɗaya ne daga cikin kamfanonin da suke ƙarƙashin rukunin kamfanoni na MOAHZ group, ya samu nasarar amsar kambun yabo daga ƙasar Turai saboda ingancin kaya da harkokinsa. Majalisar cinikayya ta ƙasar Birtaniya (EBA) ita ce ta jagoranci shirya taron da ba da wannan kambun girmamawar. A yayin da yake jawabin taya murna, shugabar gudanarwa ta majalisar EBA, Malama Anna Jones, ta bayyana cewa, manufar wannan taron ba da kyaututtukan da karramawa mai taken, 'Karramawar ingancin kaya na Duniya…
