12
Jun
Daga AMINA YUSUF ALI Wata kotu ta umarci a garƙame dukkan rassan ɗaya daga cikin manyan Bankuna Nijeriya wato Bankin Zenith. Kuma ta nemi bankin da ya warware harƙallar Naira biliyan 1.9 da take zargin su da yi. A cikin watan Mayun da ya gabata ne dai aka wayi gari da ganin wasu jami'an tsaro sun rufe tare da kange dukkan rassan Bankin Zenith da suke a garin Owerri a jihar Imo. Hakan ya biyo bayan umarnin kotu da ta nemi jami'an da su aikata hakan don ladabtarwa ga bankin. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan rufe bankin umarnin kotun masana'antu…
