19
Aug
Daga AISHA ASAS Da yamma, a cikin cunkoso irin na Jihar Kano, Aisha Abubakar Usman, ke tsaye a gefen titi, ta na jiran lokaci mafi cancanta ta tsallake titin Zoo Road mai yawan kaiwa da komowa. Wannan layi na Zoo Road ƙwarai ya cancanci a kira shi da layin Kannywwod, kasancewar yana ɗauke da mafi yawa daga cikin masu harkar fim a garin na Kano. Kalmar Kannywwod suna ne da aka sanya wa masana'antar da ke arewacin Nijeriya, wato Hausawa. Kuma kalmar ta samo sunanta ne daga sunan Jihar Kano, inda ya zama mazauni ko in ce cibiyar mafi yawa…