02
Aug
Daga AISHA ASAS Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya wato, MOPPAN ta gargaɗi masu amfani da ita wurin neman biyan buƙatunsu na siyasa, ta ja kunnen su da su daina amfani da sunanta yayin harkokinsu na siyasa. Gargaɗin ya zo ne a wata takarda ga manema labarai da Kakakin Al-Amin Ciroma, MOPPAN na ƙasa, ya rattaba wa hannu. Al'Amin ya ce, "Ana jawo hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki gami da shugabanni a matakin jiha da na ƙasa cewa, ƙungiyar MOPPAN ba ƙungiya ce ta siyasa ba, kuma ba ta da alaƙa da wata jam'iyya." Wannan tunatarwar tana zuwa…