05
Jul
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A wannan mako filin Nishaɗi ya zanta da wata matashiya 'yar fim da ta shiga harkokin finafinai da ƙafar dama, Rahina M. Bello, wata matashiya ce da cikin ƙanƙanin lokaci ta yi fina-finai da yawa, a zantawarta da wakilinmu a Kano, za ku ji yadda a cikin shekara guda (Heena) ta shirya finafinai goma. Ku biyo mu: MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatunmu?Rahina: Sunana Rahina M. Bello amma an fi sanina da Heena. Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?An haifeni a barikin Sojoji na Ibadan, babana Soja…