Gwamnatin Birtaniya ta kori limami bayan zanga-zangar ƙin amincewa da wani fim da Musulmai suka yi

Daga AISHA ASAS a Abuja

Biyo bayan wata zanga-zanga da Musulmai suka yi a ranar Asabar ɗin da ta gabata kan wani fim da aka fara haskawa a gidajen sinima kan rayuwar ‘yar Manzon Allah, Nana Faɗima, wanda suke zargin an yi shi ne don cin zarafin Musulunci.

A kan haka ne gwamnatin ƙasar Birtaniya ta sallami wani malamin addinin Musulunci da ke aiki da ita daga muƙaminsa na mashawarcin hukuma, kan zargin sa da zama ummul haba’isin wannan zanga-zanga da Musulmai suka yi.

Masu zanga-zangar sun nemi da a soke kallon wannan shirin fim ɗin da ya kasance wata hanya ta cin zarafin mutane masu daraja a addinin Musulunci.

Sanarwar wadda Cineworld ta fitar ta biyo bayan rubutun da malamin mai suna Qari Asim, limami kuma cikakken lauya, mazaunin birnin Leeds na arewacin ƙasar ta Birtaniya ya yi a shafin sa na sada zumunta, inda ya bayyana alhininsa tare da matsayin fim ɗin a zuciyar kowane Musulmi mai kishin addinin sa. “Wannan fim ya sosa zukatan al’ummar Musulmi tare kuma da sanya su baƙin ciki,” a cewar sa.

Duk da cewa babu wata hujja da ta nuna shi a matsayin ja gaba a wannan zanga-zanga, sai dai ya shelanta yin ta a shafin sa na sada zumunta na Facebook, wanda ya kira haƙƙin faɗar albarkacin baki, yayin da ita gwamnatin ta kira shi da rashin sanin matsayin aikinsa da kuma rura wutar rigimar.

A takardar da aka bai wa limamin, gwamnatin ta bayyana wallafar da ya yi a Facebook a matsayin rashin dacewar aikin nasa da kuma na rajin kare haƙƙin Musulunci wanda aka kira da bayyana qiyaya ga waɗanda ba Musulmai ba.

Har wa yau, takardar ta bayyana kora ta nan take kuma ta gabaɗaya ga malamin, gwamnatin ta ce, furucin nasa ne ya haifar da zanga-zangar da ta yi sanadin ƙaruwar ƙiyaya a tsakanin masu bambancin ra’ayi a cikin addinin.

Wasiƙar ta ƙara da cewa, “wannan ya nuna da sa hannunsa dumu-dumu a wannan zanga-zanga, wanda hakan ya saɓa wa dokar aikinsa na mashawarcin hukuma.”

Wasan kwaikwayon ya kasance a matsayin fim na farko a kan rayuwar Fatima ɗiyar Manzon Allah, kuma ya ƙulla alaƙa tsakanin qungiyar da’awa ta Daesh a ƙarni na 21 da kuma wasu jiga-jigai a tarihi masu bin tafarkin sunna a Musulunci.

Da ya ke ƙorafi yayin ganawarsa da jaridar The Guardian, babban furodusa na shirin fim ɗin Malik Shlibak, ya bayyana damuwarsa kan irin yadda zanga-zangar ta yi tasiri a wuraren kallon shirin na sa, inda yake cewa, sarƙoƙin ƙofofin sinimar sun sha jijjiga wanda ya yi sanadiyar tsinkewarsu.