Kahutu Rarara ya taya Tinubu murna tare da gwangwaje shi da waƙar zaɓen 2023

Daga AISHA ASAS a Abuja

biyo bayan tabbatar da jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa, babban mawaƙin jam’iyyar, Dauda Kahutu Rarara, ya taya zaɓaɓɓen ɗan takarar murna tare kuma yin alƙawarin zai shirya tsaleliyar waƙa da zata shiga layin makaman yaƙin neman zaɓe.

Rarara ya bayyana hakan ne a wata ziyarar taya murna da ya kai wa tsohon gwamnan Iko, shugaban jam’iyyar APC kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu.

Babban mawaqin ya nuna jin daɗin sa kan nasarar da tsohon gwamnan ya samu tare kuma da nuna mubaya’arsa gare shi da kuma ƙungiyar da yake jagoranta ta 13×13.

Da ya ke nasa jawabin, zaɓaɓɓen ɗan takarar ya nuna jin daɗin sa ga ziyarar da mawaƙin ya kawo masa, ya kuma ƙara da bayyana godiyar sa ga samun goyon bayansu da yake fatan yin aiki da su don ganin an cimma nasara a zaɓe mai zuwa.

Daga ƙarshe, mawaƙin ya yi alƙawarin rera wa ɗan takarar waƙa don bada tasa gudunmawa a yaƙin neman zaɓe tare kuma da nuna goyon bayansa ga jam’iyyar APC.