Su waye Iyayen ‘Safara’u Kwana Casa’in’?

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A sakamakon halin da fitacciyar jarumar shiri mai dogon zango na ‘Kwana Casa’in’ Safiya Yusuf, wadda aka fi sani da Safara’u Kwana Casa’in ta samu kanta a wannan lokacin ya zama wajibi a yi wani abu domin ceto rayuwar wannan jarumar, ba don komai ba, sai don kasancewar ta ƙanwa, yaya, ‘ya wadda in sha Allahu nan gaba kaɗan take shirin zama uwa ga ya’yan da za ta haifai.

Idan muka yi duba ga rayuwar Safara’u tun a baya kafin shigar ta shirin ‘Kwana Casa’in’, bincike ya tabbatar da cewar ta shiga wata rayuwa ne da ta zamo ‘yar yawon duniya da ba ta jin kunyar ta fito ta yi abin da zuciyarta ta ayyana mata, wanda hakan ya kaita ga yin bidiyo da ya fallasa bayan ta zamo fitacciyar jaruma a shirin ‘Kwana Casa’in’. 

Sai dai samun kanta a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’ ya zamo mata hanyar kula da wasu abubuwa na rayuwar. Domin kuwa duk rashin kunyar mutum ko mace ko namiji idan ya samu kan sa a cikin harkar fim, ko don gudun abin da za a faɗa a kan sa, sai ya ɓoye wasu abubuwan da yake yi a rayuwarsa don kada mutane su gani a matsayin sa na jarumi.

A nan ba ina son na nuna ‘yan fim ba masu laifi ba ne ko wasu mutane da suke koyar da ingantacciyar tarbiyya. Amma dai ko babu komai harkar fim ta gyara tarbiyyar Jarumai masu yawa wanda ba don suna yin fim ɗin ba, to da abin da za su yi sai ya zarta hakan. Halin da Safara’u kaɗai take ciki a yanzu zai iya zamar mana misali, ina da yaƙini da har yanzu Safara’u tana yin fim ba za ta samu kanta a rayuwar da take ciki ba.

Tun bayan vullar bidiyon tsiraicin ta yau kusan shekaru biyu kenan jama’a a lokacin suka shiga tofin Allah ya tsine a kanta, suna faɗar magana mara daɗi tare da yanke mata hukunci irin na Alƙalan Dankali. Wanda shi jama’ar mu suka saba yi idan bala’i ya faɗa wa mutum maimakon a tausaya masa a bi shi da addu’a sai a yi ta aibata shi a daidai lokacin da ta ke buƙatar kulawa ta a jawo shi a jiki a nuna masa kuskure ne Allah zai iya yafewa matuƙar an yi tuba nagari.

Lamarin Safara’u ya zama kamar Mahaukacin da yake rawa a kasuwa ne. Duk lokacin da ka ga mahaukaci a kasuwa yana rawa ana yi masa dariya ana bin sa da tsokana ko ana jifan sa, duk waɗanda su ke yin wannan to babu ɗan uwan sa a ciki, kuma duk ɗan uwan sa da ya zo wucewa ya gani ko dai ya hana ko kuma ya wuce cikin ɓacin rai.

To, sai dai abin mamaki tun lokacin da wannan abu ya faru ga Safara’u iyayenta suka yi watsi da ita, mutane suka yi watsi da ita, aka bar ta da wasu ‘yan iskan yara suna sheƙe ayar su da ita. Wanda na yi imani da Allah bayan faruwar abin da malamai ne suka ja ta a jiki kamar yadda waɗannan yaran suka ja ta a jiki da tuni Safara’u ta zama cikakkiyar mace mai kamun kai da za ta zama uwa tagari ga yaran da za ta haifa.

Kuskuren farko da aka samu tun bayan faruwar wannan lamarin dai shine, fitar da ita daga cikin shirin ‘Kwana Casa’in’, domin yin haka shi ne sanadiyyar fusatar da ko da yake su daman neman kuɗi su ke yi da fim ɗin su, don haka ba za su so abin da zai taɓa musu kasuwar su ba. To amma bayan sun cire ta bai kamata iyayenta su yi watsi da ita ba domin Hausawa sun ce, hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka jefar, don haka su jawo ta a jiki su nuna mata ita ‘ya ce mai ‘yance kamar kowa, luma abin da ta faru da ita tsautsayi ne sai dai ta kiyaye abin da zai kai ta ga faɗawa hakan nan gaba. 

Su ma jama’ar gari bai kamata su yi watsi da ita ba, domin kuwa Safara’u ba ita kaɗai take rayuwa ba, za ta rayu da wasu yara ne ko dai ɗanka ko ‘yarka ko ƙanwarka, ko wani na kusa da kai.

Shin wai su waye iyayen Safara’u? Wanne dalilin ya sa suka yi watsi da ita suka barta a wajen ‘yan duniya? Sun haƙura sun bar wa duniya ita ne? Kuma wannan matakin da suka ɗauka ya yi daidai a gare su, suna ganin sun sauke nauyin tarbiyyar da Allah ya ɗora musu ne? Lallai a yanzu duk wani abu da ta yi a rayuwa zai koma zuwa gare su ne domin ko babu komai ta yi sunan da duk wanda ya san su iyayenta ne, idan sun je cikin taro za a rinƙa nuna su ana cewa ga Baban Safara’u can ko ga Mahaifiyar Safara’u can. Na san da haddar Qur’ani ta yi za su so su ji hakan, amma yanayin da take ciki a yanzu za su rinƙa gudun hakan. Don haka har yanzu lokaci bai ƙure musu ba na su jawo ta a jiki su nuna mata ita ‘ya ce kamar kowa, tana da damar ta rayu cikin aminci kuma ta kiyaye mutuncinta. 

Su ma ‘yan fim da suke ganin ai yanzu ba ta su ba ce musamman ma ‘yan Kannywwod, suna ganin Safara’u ‘yar fim ɗin ‘Daɗin Kowa’ ce don haka ba ta su ba ce, ba ta da rajista da su. To su kaɗai suka san da haka, jama’a suna kallon ta ne a matsayin ‘yar fim saboda abin ya shafe su kai tsaye, ko dai su yi wani abu don mutunta sana’arsu ko kuma a ci gaba da yi musu tofin Allah ya tsine saboda Safara’u ‘yar fim tana yin abin da bai dace ba. 

Su ma jama’a da suke ganin kamar abin bai shafe su ba, su ma daina tunanin hakan, abin ya shafi kowa, domin duniya a tafin hannu take a yanzu, domin idan ba ka tashi ka yi abin da ya dace ba ko da na addu’ar shiriya ga Safara’u ba ka tsaya kana tsine mata, kullum rawarta take yi da yaran da suka fi ta lalacewa, idan ba ka kalla ba yaran ka suna kallo suna ɗaukar wasu abubuwan da take yi har su rinƙa ba su sha’awa. Ƙarshe idan ba ka yi wasa ba sai ka samu irin Safara’u a gidanka. 

Su ma hukumomi, kamar Hukumar Hisbah suna da ta su gudunmawar da za su bayar domin kuwa, yanayin da Safara’u take ciki a yanzu ya yi kama da wani Bom da aka dasa wa yaranmu masu tasowa, wanda idan har ba a yi ƙoƙarin kwance shi ba, to idan har ya fashe ba a san illar da zai yi wa yaranmu masu tasowa ba, don haka idan har za su ɗauki nauyin samar wa Sadiya Haruna hanyar tsira da ceto ta daga halin da ta samu kanta a baya, wanda a yanzu Alhamdulillahi, ko babu komai sun yi rawar gani wajen saita rayuwar ta a yanzu. To ita ma Safara’u tana buƙatar irin wannan kulawar. 

Da fatan iyaye da jama’a da kuma Hukumar Hisbah za su yi abin da ya kamata wajen ceto rayuwar Safara’u daga hannun waɗancan yaran, domin kyautata rayuwar ta da ta yaranmu.