01
Sep
Daga FARFESA FARUK SARKINFADA Haƙiƙa ilimin kimiyya da fasaha baiwa ce ta Ubangiji Ya keɓanci wasu daga cikin bayinsa da ita, wanda su kuma suke da haƙƙin sanar da wanda Ubangiji ya so. Amma kuma amfaninsa da tasirinsa da yin aiki da shi ya shafi kowa da komai. Don haka ba sai mutum ya karanci ilimin kimiyya da fasaha a makaranta ya cancanta ya san shi ko ya yi aiki da shi ba. Ma fi sauƙin sanar da ilimin kimiyya da fasaha ga al’umma shi ne samar da shi da koyar da shi cikin yarensu, ta yadda zai yi sauƙin…
