Nishadi

Na sha tsangwama sanadiyyar tsumburewar jikina, har ya sa ni tunanin kashe kaina – Jarumi Aki

Na sha tsangwama sanadiyyar tsumburewar jikina, har ya sa ni tunanin kashe kaina – Jarumi Aki

Daga AISHA ASAS  A cikin wata tattaunawa da Chude Jideonwo, shahararren jarumin barkwanci da ya fito daga Jihar Abiya da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya bayyana yadda tsayawar girman jikinsa ya zama babbar barazana ga walwalarsa tare da samun tsangwar da har ta sa shi tunanin ya kashe kansa ma ya huta. Jarumin ya bayyana cewa, saura ƙiris ya ɗauki ransa bayan da likita ya tabbatar wa mahaifiyarshi yana tare da laluran tsumburewar jiki, wanda hakan na nufin jikinsa ba zai ci gaba da girma daidai da shekarunsa ba. Jarumin ya…
Read More
Abba El-Mustapha ya yi rashin mahaifiya

Abba El-Mustapha ya yi rashin mahaifiya

Daga AISHA ASAS  Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, kuma tsohon jarumi a masana'artar Kannywood, Malam Abba El-Mustapha, ya yi rashin mahaifiyarshi mai suna Hajiya Aisha wadda ake kira da Gwaggo, a ranar Talatar da ta gabata. Sanarwar rasuwar wadda ta fito daga ɗan nata Abba El-Mustapha, yayin da ya wallafa a shafinsa na Facebook.  El-Mustapha ya bayyana rasuwar mahaifiyar tashi cikin jimami, tare da siffanta ta a matsayin rayuwarshi bakiɗaya.  “Na rasa mahaifiyata kuma duniyata, (Gwagwgo). Ya Allah ka jiƙan ta, ka gafarta mata kurakuranta, ka sa aljanna ce makomar ta. I will mourn you…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin haɓaka fannin ƙirƙira 

Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin haɓaka fannin ƙirƙira 

Daga AISHA ASAS  Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi alƙawarin sabunta fannin ƙirƙira a ƙoƙarin ganin sunan Nijeriya ya fita a matsayin babban birnin da damfara ta yada zango. Sabuwar Ministar Raya Al’adu da Inganta Tattalin Arziki, Hannatu Musawa ce ta yi wannan jawabi a lokacin da ta kai ziyara mafaifarta, Jihar Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata. Hannatu ta bayyana cewa, za a yi dukkan mai yiwa don ganin an goge ƙaurin suna da Nijeriya ta yi, na zama babbar ƙasa a duniya da ta fi yawaitar masu damfara. “Za mu mayar da…
Read More
Mahaifiyar Mawaƙi Wizkid ta zama riga mu gidan gaskiya

Mahaifiyar Mawaƙi Wizkid ta zama riga mu gidan gaskiya

Daga AISHA ASAS  Shahararren mawaƙin da tauraruwarsa ke haskawa a wannan zamani, Ayodeji Ibrahim Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, ya yi babban rashi, inda mutuwa ta ɗauke mahaifiyarsa mai suna Misis Jane Dolapo. An ruwaito cewa, Misis Balogun ta mutu ne a ranar Juma'a, sai dai har zuwa yanzu babu wani cikakken bayanin abinda ya yi sanadin ajalinta. Sannan ba a ji komai daga bakin ɗan nata mawaƙi Wizkid ba. Watakila hakan ba ya rasa nasaba da zamewarta ginshiƙi ga rayuwarsa, domin ta ba shi goyon baya, kuma ta kasance ƙwarin gwiwa gare shi akan harkar waƙan da…
Read More
Jaruma Hannatu Umar Sani ta rasu

Jaruma Hannatu Umar Sani ta rasu

Daga AISHA ASAS  A ranar Lahadin ta makon iiya, 20 ga watan Agusta, masana'antar Kannywood ta tashi da wani sabon rashi. Duk da cewa ta rasa ɗaya daga cikin tsofaffin jarumanta ne, hakan bai hana mutuwar ta zama abin alhini gare su da kuma masoyanta ba, sakamakon irin rawar da ta taka a lokacin da take masana'antar.  Jaruma Hannatu Umar ta amsa kiran mahalicci a gidan yayarta da ke unguwar Katampe a Birnin Tarayya, Abuja, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito.  Wani abin tava zuciya da mutuwar jarumar shi ne, ba ta tare da wata rashin lafiya bare har a…
Read More
Mawaƙiya Stephanie ta yi tsirara a Instagram don zagayowar ranar haihuwarta

Mawaƙiya Stephanie ta yi tsirara a Instagram don zagayowar ranar haihuwarta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitacciyar mawaƙiyar Ƙasar Ghana, Stephanie Benson, ta ciyar da idanun mabiyanta da wani rubutu mai daɗi. 'Yar ƙasar Ghana wadda take rayuwarta a Burtaniya, wacce ta cika shekaru 56 a ranar 17 ga watan Agusta, ta bai wa mabiyanta kallon yadda ta yi niyyar yin zama tare da mijinta a ranar ta ta musamman. A cikin wani launin fure da cakuletin hoto, Stephanie Benson ta shafe ilahirin jikinta da mai tare da shimfiɗa wasu furanni daga kafaɗunta ta kuma saukar da cikinta zuwa yankin jibiyarta. Ta kwanta saman qasa sannan ta watsa wasu cakuleti…
Read More
Sai bayan mutuwar babana da aurena ne na samu aka bar ni yin harkar fim – Ummi Tarore

Sai bayan mutuwar babana da aurena ne na samu aka bar ni yin harkar fim – Ummi Tarore

"Har yanzu Ina fuskantar ƙalubale a harkar fim" Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Aisha Adam Muhammad da aka fi sani da Ummi Tarore wata matshiyar da ta ke tashe a masana'artar fim ta Kannywood, a tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da kuma yadda a ƙasa da shekaru biyu ta yi finafinai fiye da 25. Ku biyo mu don jin yadda hirar za ta kasance: MANHAJA: Gabatar mana da kanki. UMMI TARORE: Sunana Aisha Adam Muhammad da aka fi sani da Ummi Tarore, an haife ni a shekarar 2002 a Jos, amma a Kano muke…
Read More
Ina mamakin yawaitar mutuwar auren jarumai mata – Pete Edochie

Ina mamakin yawaitar mutuwar auren jarumai mata – Pete Edochie

Daga AISHA ASAS Shahararren jarumin da ya ga jiya, ya ga yau, Pete Edochie, ya bayyana kaɗuwarsa kan yadda auren jarumai mata ke mutuwa ba ƙyaƙyautawa. Jarumin ya yi wannan ƙorafin ne a wata tattaunawa da ya yi a shirin nan na ‘WithChude’, inda ya bada misali da auren jaruma Chioma Akpotha, jaruma Ireti Doyle da kuma jaruma Tonto Dikeh, waɗanda igiyoyin aurensu suka tsinke. "Idan ka je masana'antarmu a yanzu, za ka tarar mafi yawan matanmu da suka yi aure a shekaru biyu zuwa uku baya, auren ya mutu. Na kuma yi matuƙar kaɗuwa da jin mutuwar auren Chioma…
Read More
Soke lasisin ‘yan Kannywood: MOPPAN da KSCB sun cimma matsaya

Soke lasisin ‘yan Kannywood: MOPPAN da KSCB sun cimma matsaya

Daga AISHA ASAS Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Malam Abba El-Mustapha ta janye yunƙurinta na ƙaƙaba wa 'yan fim dokar soke lasisinsu da ta shelanta yi a kwanakin baya. Hukumar ta ce, a yanzu za a sabunta wa masu harkar fim rijistansu ne a ƙarƙashin ƙungiyoyin masu shirya finafinai, waɗanda ke ƙarƙashin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, wato MOPPAN. Wannan sauyin ya biyo bayan ziyarar da ƙungiyar MOPPAN ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Dakta Ahmed Sarari ta kai wa shugaban hukumar ta tace finafinai. Bayanin wanda yake ƙunshe a wata takardar sanarwa ga manema labarai…
Read More
Mutane 1,040 ne suka amfana da tallafin kayan abinci da mawaƙi Rarara ya yi a Katsina

Mutane 1,040 ne suka amfana da tallafin kayan abinci da mawaƙi Rarara ya yi a Katsina

Daga AISHA ASAS Shahararren mawaƙin siyasa, kuma babban mawaƙin Jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, ya bayar da tallafin kayan abinci ga mabuƙata, a ƙoƙarin ganin ya bayar da tasa gudunmawa a samun sasaucin matsin rayuwa da ake ciki. Mawaqin ya bayar da wannan tallafi ne a mahaifarsa, Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Danja, ta Jihar Katsina, kamar yadda babban mai taimaka wa mawaqin a kafafen sada zumunta Rabi'u Garba Gaya ya bayyana. Rabi'u ya ce, Rarara ya gudanar da rabon kayan ne a mahaifarsa da ke Kahutu, sannan an bai wa kowanne mutum ɗaya daga cikin mutanen 1,040 ƙaramin buhun…
Read More