Soke lasisin ‘yan Kannywood: MOPPAN da KSCB sun cimma matsaya

Daga AISHA ASAS

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Malam Abba El-Mustapha ta janye yunƙurinta na ƙaƙaba wa ‘yan fim dokar soke lasisinsu da ta shelanta yi a kwanakin baya.

Hukumar ta ce, a yanzu za a sabunta wa masu harkar fim rijistansu ne a ƙarƙashin ƙungiyoyin masu shirya finafinai, waɗanda ke ƙarƙashin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, wato MOPPAN.

Wannan sauyin ya biyo bayan ziyarar da ƙungiyar MOPPAN ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Dakta Ahmed Sarari ta kai wa shugaban hukumar ta tace finafinai.

Bayanin wanda yake ƙunshe a wata takardar sanarwa ga manema labarai da kakakin ƙungiyar ta MOPPAN na ƙasa, Al-Amin Ciroma, ya sa wa hannu, a ranar Laraba. Ya bayyana cewa, an cimma matsaya ne a lokacin da Shugaban MOPPAN, Dakta Sarari ya kai ziyarar taya murna ga shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha a ofishinsa don taya shi murnar naɗin da aka yi masa, tare kuma da zayyane masa manufofin kafa ƙungiyar MOPPAN.

Al-Amin ya ce, Dakta Sarari ya soma da faɗa wa shugaban cewa, ƙungiyar MOPPAN ce kaɗai ƙungiyar da Gwamnatin Tarayya ta sani a Arewacin Nijeriya ta hanyar Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya, kamar yadda sashe na 17(2) da (3) na dokar hukumar ta 2008 ta tanada.

Dakta Sarari ya yi ƙarin bayani kan dokokin, inda ya ce, ya kamata ace dukka dokokin jiha da na tarayya su yi aiki tare, ba wai su dinga cin karo da juna ba.

Ba a nan ya tsaya ba, shugaban ƙungiyar, ya tunatar da hukumar doka ta sashe na 84 na kundin dokokin KSCB, inda ya ce, “dukka masu harkar shirye fim za su kasance membobi masu rajista a ƙungiyoyin da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta yarje masu.”

Kazalika ƙungiyar ta shawarci hukumar da ta duba yiwuwar ƙirƙiro da wani ɓangare da zai bayar da gudunmawa wurin cigaban masana’antar don ganin harkar fim ta bunƙasa.

A nasa jawabin shugaban hukumar Abba El-Mustapha ya nuna godiyar sa ga shugaban ƙungiyar MOPPAN, ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda ƙungiyar ta yi hanzarin shigowa lamarin, ya tabbatar masa da ya karɓi shawarwarin da ya kawo, ya kuma ƙara da cewa, a shirye hukumar ta ke da ɗaukar duk wata shawara daga ƙungiyar tare da haɗa gwiwa da ita wurin ciyar da masana’antar gaba.

Daga ƙarshe ya ce, hukumar tasa ta amince da a sabunta wa masu harkar fim ɗin rijista kamar yadda MOPPAN ta nema, kafin ya qara godiya ga shugaban tare da tabbatar masa ƙofarsa a buɗe ta ke don aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyar don ciyar da harkar fim gaba.