Alhasan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta Yamma a shekarar 1950

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alhassan Ɗantata, fitaccen attajiri a faɗin nahiyar Afirika ta yamma, wanda tushen arzikinsa ya samo asali daga sayar da Goro da Gyaɗa.

Haihuwa da nasaba;

Alhassan Ɗantata ya fito ne daga cikin zuri’ar Agalawa, iyayensa fatake ne masu yawon kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan. An haife shi a shekarar 1877, a wani ƙaramin ƙauye da ake kira Ɗanshayi a garin Bebeji, wanda ke da tazarar aƙalla kilomita goma sha-biyar daga garin Kano. Alhasan ɗaya ne daga cikin ’ya’yan Abdullahi wanda matarsa Fatima da ake kira Amarya ta haifa.

Shi Abdullahi ɗa ne ga wani mutum mai suna malam Ali, wanda ake yiwa laƙabi da Baba Talatin. Sun taso ne daga ƙasar Katsina da iyalensu kamar yadda suka saba, suka yada zango a garin Bebeji, bayan wani lokaci kuma sai Baba Talatin ya koma Madobi da zama, wanda a nan Allah ya yi masa rasuwa. Wannan dalilin ne ya zaunar da su a garin, wanda shi Abdullahi ya ci gaba da kula da iyalan har zuwa lokacin da suka kimtsa don ci gaba da tafiyar a shekarar 1877. Bayan sun shirya tsaf don tafiya izuwa garin Gonja, babbar cibiyar hada-hadar Goro ta ƙasar Ghana, sai matarsa Amarya ta haifi Alhassan a sansanin da suka yada zango a nan garin Bebeji.

Abdullahi mahaifin Alhassan ya rasu a shekarar 1885, lokacin Alhassan na da shekaru takwas a duniya, kuma yana da ƙanne kamar su; Malam Jaji, Malam Bala, Malam Sadi da sauransu. Duk suna ƙanana sosai a lokacin, don haka ba za su iya juya dukiyar mahaifin nasu ba.

Bayan an raba gado an ba wa kowa nasa kamar yadda shari’a ta tanadar, sai Amarya mahaifiyar Alhasan wadda dama ita ma tana kasuwanci kamar yadda mahaifiyar mijinta ke yi, ta yanke shawarar barin garin Bebeji inda ta bi ayarin fatake zuwa Accra ta ƙasar Ghana, inda a can ta ci gaba da yin kasuwancinta. Ta bar ’ya’yanta a Bebeji. Shi Alhassan ya kasance a qarqashin kulawar wata tsohuwar mata, wadda ta kasance baiwa ce, da ake kira da Tata. Alhassan ya samu duk wata kulawa da ake samu a wajen uwa, wannan dalilin ne ma ya sa tun a wancan lokacin ake kiransa da suna Alhassan Ɗantata.

Neman ilimi da gwagwarmayar rayuwar Ɗantata;

Alhassan Ɗantata ya yi karatun Alƙur’ani (Allo) a nan garin Bebeji, makarantar da ke ƙarƙashin kulawar ɗarikar Tijjaniyya. A matsayin almajiri yana da buƙatar abinda zai taimaka wa kansa, wannan ya sa ya fara tsakurar abinda ya samu na daga gado domin ya tallafi rayuwarsa. A matsayin Almajiri mai ɗaukar nauyin kula da kansa ta ƙangaren abinci da suture, har ma da tallafawa malaminsa, abu ne mai matuƙar wahala, don haka ya kan yi bara wani lokacin, wasu kuma su kan sanya shi aiki ya yi a biya shi. Aikin hannu, ko aikin qarfi kamar wata al’ada ce ta matasan zuri’ar Agalawa da Alhassan Ɗantata ya gada. Hakan kuma bai hana shi samun lokacin yin karatu ba. Alhassan ya yi nasarar tara ’yan kuɗaɗe a asusu, wanda Tata ke kular masa da shi.

Yana ɗan shekaru sha-biyar a duniya ya bi ayarin fataken Gonja, da niyyar kai wa mahaifiyarsa ziyara. Ya sari kaya a nan garin Bebeji ya tafi da su, waɗanda ya sayar da fiye da rabi a hanyarsu ta zuwa Accra.

Ya yi farin cikin ganin mahaifiyarsa da yadda ya sameta cikin kwanciyar hankali, tare da bunƙasar dukiyarta. Har ma ya yi fatan dukiyar za ta wadacesu su rayu tsawon lokacin da zai dawo ba tare da ya nemi kuɗi ba. Sai dai kwanansa ɗaya da zuwa sai ta ɗauke shi ta kai shi wajen wani malamin addini domin ya yi karatun Alƙur’ani, tare da umartarsa da ya zauna a wajensa kafin lokacin tafiyarsa ya yi.

Dantata bayan karatun Ƙur’ani, a ranakun Alhamis da Juma’a yana fita neman aiki, ya yi sosai a Accra fiye ma da yadda ya yi Bebeji, haka kuma yana bawa malamin kaso mafi tsoka na duk kuɗin da ya samu. Sannan yana yin barar abinci domin ya ci kuma ya kai wa malamin.

Bayan wasu ’yan kwanaki sai Alhassan ya dawo garin Bebeji domin ci gaba da neman ilimi, yayin da Tata ta ci gaba da ɗora shi a hanyar yin adani, inda ya ci gaba da ajiye kuɗi kullum a duk abinda ya samu.

Yadda rikice-rikice suka ritsa da Ɗantata;

A shekarar 1893 rikicin mulki da na fataucin bayi suka ɓarke a garin Kano, lokacin Ɗantata yana da shekaru sha-shida a duniya. A lokacin aka samu wasu gungun marasa rinjaye da suka valle daga Kano, suka yiwa garin Bebeji tsinke, inda suka kori mutanen garinsuka karkashe wasu da dama, sannan suka kame wasu a matsayin bayi. Alhassan da ’yan uwansa Bala da Sadi, na daga cikin waɗanda aka kama a matsayin bayi, daga baya Alhassan ya fanshesu da dukiya, suka shaƙi iskar ’yanci. Yanayin ya zowa Alhassan da tsauri a lokacin, saboda ƙaracin shekarunsa.

Faɗaɗa harkokin kasuwanci;

Bayan rikicin ya lafa, sai Ɗantata ya mayar da hankalinsa kan shirye-shiryen faɗaɗa harkokin kasuwancinsa. Ya fara amfani da sabbin hanyoyin kasuwanci, inda ya fara zuwa Ibadan da Legas, tare da inganta dangantaka tsakaninsa da takwarorinsa ’yan kasuwa. Ya kan sayi dabbobi ya yi musu shaida ya loda su a ƙaton jirgin ruwa ya riƙa kaiwa garuruwan; Accra, Kumasi, Sekodi, da Legas, daga can kuma ya saro goro ya kawo Kano ya rarraba wa ƙananan ’yan kasuwa. Shi ne ɗan kasuwa na farko a arewacin Nijeriya da ya fara haɓaka wannan hanyar kasuwancin, kuma ya ɗauki shekaru da dama yana yi. Wannan ƙoƙarin nasa ya jawo hankulan ƙasashen Turai wajen ƙulla dangantakar kasuwanci da shi.

Taimako;

Ɗantata ya taimaki mutane da dama rayuwarsa, ba iya ƙabilarsa ta Hausa ba, har da Yarabawa, da Inyamurai. Waɗanda ya samar musu da aiki a kamfanoninsa, da ya ke biyansu. Haka nan da yawa daga cikin ma’aikanta musamman Hausawa suna kwana a gidansa, haka nan yakan ɗauki ɗawainiyar sha’ani na ma’aikatansa idan ya taso, kamar biki ko suna. Sannan ya kan shiga cikin ma’aikatansu su yi aiki tare, haka ma idan watamatsala ko rigima ta tashi a tsakaninsu, yakan shiga ya sasanta, kuma ya kashe rigimar.

Sanadin rasuwarsa;

A shekarar 1955 Ɗantata ya kamu rashin lafiya, ganin yadda cutar ta tsananta, sai ya tara ’ya’yansa, da mai kular masa da ɓangaren kuɗi, wato Garba Maisikeli, ya faɗa musu cewa shi fa rayuwarsa tazo ƙarshe, babu abinda ya kamace su su yi illa haɗin kai. Ya ja hankalinsu da cewa, kar su bari wannan kamfanin na Alhassan Ɗantata and sons da ya gina, su bari ya rushe. Ya kuma roƙe su da su riƙi auren danginsu, su taimaki mabuƙata, sannan su yi hulɗar arziki da sauran attajirai.

Kwanaki uku bayan wannan huɗubar da ya yi musu, Alhasan Ɗantata ya rasu, a ranar Laraba 17 ga watan August 1955. A ranar aka binne shi a gidansa da ke Sarari. Ya rasu ya bar mata biyu, Umma Zariya da kuma Maimuna. Daga cikin ’ya’yansa akwai; Mamuda Ɗantata, Ahmad Ɗantata, Sunusi Ɗantata, (wanda ya haifi Mariya, ita kuma Mariya ta haifi Aliko Ɗangote). Aminu Ɗantata, da kuma Mudi Ɗantata.