Nishadi

Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Daga BASHIR ISAH Da SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitaccen ɗan jaridar nan kuma jarumin Kannywood, har wa yau Kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Al-Amin Ciroma, wanda mutane suka fi sani da Baban Lukman na cikin shirin fim ɗin nan mai dogon zango, 'Labarina', ya bayyana cewa, yana nan da ransa, bai mutu ba saɓanin wata sanarwar mutuwarsa da aka yaɗa. Ciroma ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 46 da ya yi aka kuma yaɗa a soshiyal midiya da yammacin ranar Alhamis bayan da labarin ‘mutuwarsa’ ya karaɗe kafafen sada zumunta,…
Read More
Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Yusra Yusuf Yunusa wadda aka fi sani da Yusra AGM matashiyar da ta yi fice a wajen rubuta labarin fim a masana'atar Kannywood. A tattaunawarta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma irin faɗi-tashin da ta yi har ta kai ana karbar rubutunta a Kannywood. A sha karatu lafiya: MANHAJA: Muna son ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu? YUSRAH YUSUF: Sunana Yusrah Yusuf Yunusa, wacce aka fi sani da Yusra AGM Bashir kamar yadda ake kira na. Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinka? Nayi karatu a Mai…
Read More
Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Daga WAKILINMU Fitacciyar jaruma a masana'antar fina-finai ta Nollywood, Mercy Aigbe, ta bayyana sunanta na Musulunci biyo bayan musuluntar da ta yi. Ta bayyana sunan ne a wajen taron lacca na Ramadan da addu'a ta musamman da suka shirya ita da mijinta, Kazeem Adeoti. Hakan na ƙunshe ne cikin wani faifan bidiyon tattaunawar da aka yi da ita wanda aka yaɗa a kafar sada zumunta na zamani. An jiyo ta tana cewa, “Insha Allah, sabon sunana shi ne Hajiya Meenah Mercy Adeoti. Meenah mai ɗauke da harafin H."
Read More
Da yawan mawaƙan Arewa ba su san ta yadda za su amfana da basirarsu ba – Haidar Blog

Da yawan mawaƙan Arewa ba su san ta yadda za su amfana da basirarsu ba – Haidar Blog

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Fasihin mawaqin Hausa, kuma ɗan kasuwar dake dillancin waƙoƙin Hausa a yanar gizo, mai suna Aliyu Abubakar, da ake wa laƙabi da Haidar Blog, ya bayyana wannan kyakkyawan fata da buri da yake da shi ne a kan mawaqa da dukkan waɗanda Allah Ya yi wa baiwar basirar na suna amfanuwa da basirar tasu don ƙara samun ƙwarin gwiwa gare su. Tare kuma da yin kira ga matasa da su ƙara ƙaimi wajen neman ilimi, wanda da shi ne rayuwar bawa take yin haske kuma komai ke zuwar masa a sauqaqe, a wata tattaunawa…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Jarumi Adam A. Zango

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Jarumi Adam A. Zango

Daga LARABI LARABEEN Zuwa ga jarumi Adam A. Zango, Ina fata wasiƙata ta same ka cikin ƙoshin lafiya. Game da maganar da ka yi cewa, ba za ka ƙara aure ba har abada, haba don Allah! Bai kamata ka ce haka ba. Da ma tin filazal fitattun mutane kan sha fama da matsaloli kala-kala. Amma kai naka kuskuren ya samo asali a kan yadda kake zaɓen macen aure mai kyawu fuska fiye da kyawun ɗabi'a da tarbiyya. Wata matsalar taka kuma ita ce, ka daina auren macen da take son Adam A. Zango na Film. Ka nemi macen da take…
Read More
Nijeriya ta samu Naira miliyan 278 daga sinima a watan Fabrairu

Nijeriya ta samu Naira miliyan 278 daga sinima a watan Fabrairu

Daga AISHA ASAS A ranar Talata da ta wuce, Ƙungiyar Masu Haska Finafinai ta Ƙasa, wato Cinema Exhibitors Association of Nigeria, CEAN, ta sanar da cewa, harkar kasuwar finafinai a Ƙasar Nijeriya ta samu ci baya a watan Fabrairun wannan shekara, domin kasuwar finafinai ta tsaya a iya samun Naira miliyan 200 da 78. Shugaban ƙungiyar Ope Ajayi, ya shedawa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, a cikin wata tattaunawar da suka yi cewa, sun samar wa Nijeriya Naira miliyan 278 a cikin watan Fabrairu, wanda ya yi ƙasa da abinda aka samu a watan Janairu da ya wuce da suka…
Read More
An mayar da shari’ar jaruma Hadiza Gabon Babbar Kotun Musulunci

An mayar da shari’ar jaruma Hadiza Gabon Babbar Kotun Musulunci

Daga AISHA ASAS Kotun Majistare da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, ta tattara, ta miƙa shari'ar da ake yi da fitaciyyar jaruma a masana'antar finafinai ta Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon zuwa babbar kotun shari'a. A ranar Juma'ar da ta wuce, Alƙali Isiyaku Abdulrahman, me jagorantar shari'ar da ake gwabzawa tsakanin jaruma Hadiza Aliyu Gabon da wani mutum zuwa Babbar kotun Musulunci da ke Tudun Wada. Wannan ya biyo bayan zargin da alƙalin ke yi na lauyan mai ƙara na ƙoƙarin ɓata wa kotu lokaci, don haka ya ba shi zaɓi kafin yanke hukuncin. "Kana da zaɓi biyu, ko…
Read More
TikTok ya gamu da cikas

TikTok ya gamu da cikas

Daga BASHIR ISAH A safiyar ranar Alhamis dandalin TikTok ya gamu da cikas, lamarin da ya jefa dubban masu amfani da manhajarsa a faɗin duniya cikin mawuyacin hali. A cewar shafin intanet na DownDetector mai bibiyar ire-iren waɗannan batutuwa, matsalar ta fara ne da misalin ƙarfe 09:40 agogon GMT daidai da ƙarfe 04:40 agogon ET. Ya zuwa haɗa wannan labari, kimanin mutum 3,000 sun shigar da ƙorafi rashin aikin manhajar TikTok mallakar wani kamfanin Chana mai suna ByteDance. Masu amfani da manhajar a sassan duniya, ciki har da mazauna Birtaniya da London, ne suka yi ƙorafi kan matsalar da aka…
Read More
Yadda faɗuwar Peter Obi ta hana jarumi Kanayo O. Kanayo bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Yadda faɗuwar Peter Obi ta hana jarumi Kanayo O. Kanayo bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Daga AISHA ASAS Sanannen jarumi a masana'antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood, Kanayo O. Kanayo, ya bayyana tsabar baƙin cikin sa kan yadda Peter Obi bai amshi mulkin ƙasar nan a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023. Jarumin ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, sakamakon yana layin waɗanda suke iqirarin an yi murɗiya a zaɓen, domin Peter Obi, na Jam'iyyar LP ne ya samu quri'u mafi rinjaye. Kanayo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a jiya, wanda ya yi daidai da ranar mauludin haihuwarsa cewa, zuciyarsa cike ta ke da ɓacin rai duk…
Read More
Na sha wahala a fim ɗin ‘Farida Nabil’ – Haruna Talle Maifata

Na sha wahala a fim ɗin ‘Farida Nabil’ – Haruna Talle Maifata

Daga IBRAHIM HAMISU Haruna Talle Maifata wani fitaccen jarumin ne da ya yi fice a masana'atar fim ta Kannywood, inda ya fi fitowa a matsayin ɗan daba ko mugu, a tattaunawarsa da Ibrahim Hamisu a Jos, za ku ji dalilan da ya sa ya ke fitowa a mugu da kuma irin nasarorin da ya samu a masana'atar. ku biyo mu: MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu? HARUNA: Da farko dai ni sunana Haruna Talle maifata. Za mu so jin taƙaitaccen tarihinka? An haifeni a Jos ta Jihar Plateau, na yi karatun primary da secondary, sannan…
Read More