Nishadi

Ina ƙarami na yi wa mahaifiyata tallan kayan girki – Kamaye

Ina ƙarami na yi wa mahaifiyata tallan kayan girki – Kamaye

Daga UMAR GARBA, a Katsina Ɗan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye a cikin shirin 'Daɗin Kowa' na tashar Arewa 24 baya ga kasancewar sa ɗaya daga cikin mutanen da suka ƙirƙiri masana'antar shirya finafinai ta arewacin Najeriya, wato Kannywood, ya kuma yi fice a fannoni daban daban na rayuwa kama daga rubuta littattafai, mashiryin shiri gami da bada umarni a finafinan da masana'antar ta kwashe shekaru tana shiryawa. Wakilin Manhaja a Katsina Umar Garba, ya haɗu da fitaccen jarumin a wurin taron ƙungiyar marubuta ta arewacin Najeriya da ya gudana a jihar inda ya tattauna da Kamaye…
Read More
Fim ɗin ‘Wani Gari’ ne ya tada min da tsimin son harkar fim – Zulai Uwa ta Gari

Fim ɗin ‘Wani Gari’ ne ya tada min da tsimin son harkar fim – Zulai Uwa ta Gari

"Mujallar Fim ce ubangidana a Kannywood" Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Hajiya Zulaihat Abdullahi Bebeji da aka fi sani da Uwa ta Gari ko Attajira, jaruma ce da mafi yawan finafinta a uwa ta ke fitowa. Ta shafe aƙalla kusan shekara 20 a masana'atar fim ta Kannywood. A hirarta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da irin gwagwarmayar da ta sha har zuwa wannan lokaci. Ku biyo mu: BLUEPRINT MANHAJA: Da wa muke tare? HAJIYA ZULAIHATU: Sunana Zulaihatu Aliyu Abdullahi Bebeji, ana yi min laƙabi da Hajiya Zulai Bebeji ko Hajiya Zulai Uwa ta Gari, a yanzu…
Read More
Yanzu matan Kannywood za su iya harkar fim ba tare da an ga fuskarsu ba – Halima Ben Umar

Yanzu matan Kannywood za su iya harkar fim ba tare da an ga fuskarsu ba – Halima Ben Umar

Daga AISHA ASAS Labarin yunƙurin da mata ke yi, don kafa tarihi a masana'antar finafinai ta Kannywood ta hanyar shirya fim ɗin da mata zalla suka yi aikinsa, tuni ya karaɗe kunnuwan dubunnan al'ummar Hausa, kai ma har da wasu ɓangarori na wannan qasa tamu mai albarka. Da yawa sun tofa albarkacin bakinsu da bayyana ra'ayinsu. Wasu na ganin abin a matsayin cigaba, yayin da wasu ke ganin sa a matsayin hurimin da su matan bai kamata su shiga ba, sannan wasu kuma na  ganin abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Da wannan ne shafin Nishaɗi na…
Read More
Nancy Ajram: Sarauniyar Mawaƙan Larabawa

Nancy Ajram: Sarauniyar Mawaƙan Larabawa

Daga AISHA ASAS Kiɗa da waƙa wata daɗaɗɗiyar al'ada ce ko in ce ɗab'i da ba kasafai kake samun al'ummar da ba ta da irin nata da ta ke nishaɗanta da ita ba. Wannan ne ya sa duk inda ka ratsa za ka tarar da kiɗa da waƙa ya rigaka zuwa, sai dai ka tarar da ba irin wanda ka baro ne a inda ka fito ba. Za mu iya kiran waƙa a matsayin wasiƙu zuwa ga zukatan mutane, hakan zai sa da wahala ka rasa wadda aka yi domin taka zuciyar. Kazalika bincike ya tabbatar waƙa na kan gaba…
Read More
‘Yan wasan fim biyar da suka fi arziki a duniyar finafinai

‘Yan wasan fim biyar da suka fi arziki a duniyar finafinai

Daga AISHA ASAS Bincike ya tabbatar cewa, ba waɗanda suka fi samun roman aikinsu a duniyar nishaɗantarwa kamar masu harkar fim da kuma masu buga wasan ƙwallo, hakan ya biyo bayan irin so da ƙaunar da mutane ke yi wa wannan ɓangare guda biyu. Sanannen abu ne, mutane mafi rinjaye na duniya na sha'awar kallon finafinai, walau waɗanda ake yi a yarensu ko na wasu al'ummar. Wannan ne ya sa harkar fim ta zama cikin jerin farko da ke samar da kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga mata da maza musamman ma matasa, musamman a vangaren jarumai,…
Read More
A na ci gaba da ɗaukar shirin ‘Zo Mu Zauna’ Zango na uku

A na ci gaba da ɗaukar shirin ‘Zo Mu Zauna’ Zango na uku

DAGA MUKHTAR YAKUBU A yanzu haka dai an ci gaba da ɗaukar shirin fim ɗin 'Zo Mu Zauna' mai dogon zango wanda a ke shaska shi a tashar Rarara da ke Kan YouTube wanda fitaccen marubucin labarai, kuma Furodusa Naziru Alkanawy yake ɗaukar nauyin shirya shi. Ko da yake tun bayan kammala zango na biyu mutane da suke bibiyar shafin na YouTube na Rariya domin kallon fim ɗin suke ta tambaya a rashin ganin fim ɗin, wanda hakan ya sa a ke tambayar ko dai fim ɗin an jingine shi ya tafi hutun dole? A yanzu dai an ci gaba…
Read More
Waƙa a wurina gado ce, inji Hajara Idris

Waƙa a wurina gado ce, inji Hajara Idris

“Sanadin soyayya na fara waƙa” “Harkar fim aba ce mai kyau, sai dai ga waɗanda suka ɓata ta" DAGA ABBA MUHAMMAD Hajara Idris, wadda aka fi sani da Hajjo a masana’antar waƙoƙi da finafinan Hausa, sabuwar mawaƙiya ce kuma jaruma. Domin bata jima da bayyana a masana’antar, duk da ta daɗe da fara waka. Hajjo dai ɗiya ce ga fitaccen mawaƙin asharallen nan da ke zaune a Kaduna, wato marigayi Idi Moris, kuma ita ce babbar ‘yarsa. Hajara yarinya ce son kowa ƙin wanda ya rasa. Haka kuma ba ta da girman kai, ba ta da ƙin mutane, ga ta…
Read More
Kannywood: An gudanar da taro kan haƙƙin mallaka a Kano

Kannywood: An gudanar da taro kan haƙƙin mallaka a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Ƙungiyar kare haƙƙin mallaka na hoto mai motsi wato (Audio Visual Rights Society of Nigeria -AVRS) ta gudanar da taro na musamman, da dukkanin masu ruwa da tsaki, waɗanda ke amfani da kayan kirkira na hoto mai motsi, a Jihar Kano. Taron, wanda da ya gudana a Kannywood Hall da ke kan titin Muhammadu Buhari, a Tudun-Yola da ke cikin birnin Kano. Tunda farko a jawabinsa shugaban ƙungiyar na ƙasa Mahmood Ali-Balogun, ya ce, maƙasudin taron shi ne, karɓo haƙƙoƙin finafinan da ake haskawa a otel-otel da wuraren cin abinci da wuraren aski da manyan Bas…
Read More
Za a yi fim na farko wanda mata zalla ne suka shirya a Kannywood

Za a yi fim na farko wanda mata zalla ne suka shirya a Kannywood

Daga AISHA ASAS Da yamma, a cikin cunkoso irin na Jihar Kano, Aisha Abubakar Usman, ke tsaye a gefen titi, ta na jiran lokaci mafi cancanta ta tsallake titin Zoo Road mai yawan kaiwa da komowa. Wannan layi na Zoo Road ƙwarai ya cancanci a kira shi da layin Kannywwod, kasancewar yana ɗauke da mafi yawa daga cikin masu harkar fim a garin na Kano. Kalmar Kannywwod suna ne da aka sanya wa masana'antar da ke arewacin Nijeriya, wato Hausawa. Kuma kalmar ta samo sunanta ne daga sunan Jihar Kano, inda ya zama mazauni ko in ce cibiyar mafi yawa…
Read More
Ɓarayi sun dira gidan Jarumi Saka tare da buƙatar miliyan 20

Ɓarayi sun dira gidan Jarumi Saka tare da buƙatar miliyan 20

Daga AISHA ASAS Ɓarayi ɗauke da makamai sun afka wa gidan fitaccen jarumi barkwanci a masana'antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood, Hafiz Oyetoro, wanda aka fi sani da Saka. A ranar Litinin ɗin da ta gabata, a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun. Kamar yadda makusanci kuma abokin jarumin Kayode Soaga ya bayyana wa manema labarai, ɓarayin sun dira gidan Saka suna masu neman ya ba su zunzurutun kuɗi har miliyan 20, ko kuma su aika shi lahira. "Ɓarayin sun shigo ne wuraren ƙarfe biyu na dare, ɗauke da manyan bindigogi taƙil da alburusai da kuma wasu makamai. Ba ɓata…
Read More