Nishadi

Kahutu Rarara ya taya Tinubu murna tare da gwangwaje shi da waƙar zaɓen 2023

Kahutu Rarara ya taya Tinubu murna tare da gwangwaje shi da waƙar zaɓen 2023

Daga AISHA ASAS a Abuja biyo bayan tabbatar da jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa, babban mawaƙin jam'iyyar, Dauda Kahutu Rarara, ya taya zaɓaɓɓen ɗan takarar murna tare kuma yin alƙawarin zai shirya tsaleliyar waƙa da zata shiga layin makaman yaƙin neman zaɓe. Rarara ya bayyana hakan ne a wata ziyarar taya murna da ya kai wa tsohon gwamnan Iko, shugaban jam'iyyar APC kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu. Babban mawaqin ya nuna jin daɗin sa kan nasarar da tsohon gwamnan ya samu…
Read More
Su waye Iyayen ‘Safara’u Kwana Casa’in’?

Su waye Iyayen ‘Safara’u Kwana Casa’in’?

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A sakamakon halin da fitacciyar jarumar shiri mai dogon zango na 'Kwana Casa'in' Safiya Yusuf, wadda aka fi sani da Safara'u Kwana Casa'in ta samu kanta a wannan lokacin ya zama wajibi a yi wani abu domin ceto rayuwar wannan jarumar, ba don komai ba, sai don kasancewar ta ƙanwa, yaya, 'ya wadda in sha Allahu nan gaba kaɗan take shirin zama uwa ga ya'yan da za ta haifai. Idan muka yi duba ga rayuwar Safara'u tun a baya kafin shigar ta shirin 'Kwana Casa'in', bincike ya tabbatar da cewar ta shiga wata rayuwa ne…
Read More
Salman Khan ya musanta samun saƙon barazanar da aka aika wa mahaifinsa

Salman Khan ya musanta samun saƙon barazanar da aka aika wa mahaifinsa

Daga AISHA ASAS A jiya Alhamis jarumi Salman Khan ya bayyana wa jami’an tsaro cewar bai samu saƙon wasiƙar barazana ga rayuwarsa ba kamar yadda ake ta yayatawa. Ya kuma ƙara da cewa, bai samu wata hatsaniya ko saɓani da wani ba a wannan ɗan lokaci ba, duk da cewa kwana ɗaya kafin wannan furuci na jarumin, ‘yan sanda sun shigar da koken ƙarar wanda ba a san ko wane ne shi ba kan aika wa mahaifin jarumin, Salim Khan takardar da ake masa barazanar kisa a cikinta. A wasu rahotannin sun tabbatar wasiƙar biyu ce, inda bayan ta mahaifin…
Read More
Na amince ina da matsalar ƙwaƙwalwa, don haka zan nemi taimako, cewar jarumi Terry Crews

Na amince ina da matsalar ƙwaƙwalwa, don haka zan nemi taimako, cewar jarumi Terry Crews

Daga AISHA ASAS Ɗaya daga cikin baƙaƙen da suka yi babban tsalle a masana’antar finanfinai ta Hollywood kuma masana’antar ta ke ji da alfahari da su, Terry Crews, ya yaye labule kan lamarin da ya shafi lafiyarsa, inda ya bayyana wa duniya cewa, a yanzu ya amince ƙwaƙwalwarsa ba a saite take ba, don haka yana buƙatar taimako. Jarumin da yafi ƙarfi a ɓangaren barkwanci ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Amy Morin, ya bayyana cewa, a yanzu ya gaji da yawo da nauyin da yake kan kafaɗarsa na matsalolinsa, don haka zai fara zuwa…
Read More
Wani mutumi ya maka jaruma Gabon kotu kan ƙin amincewa da aurensa

Wani mutumi ya maka jaruma Gabon kotu kan ƙin amincewa da aurensa

Wani mutumi ya maka jaruma Gabon kotu kan ƙin amincewa ya yi wuf da ita Daga AISHA ASAS Wani ma’aikacin gwamnati, mai kimanin shekaru 48 a duniya, mai suna Bala Musa, ya maka fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood Hadiza Gabon kotun shari’ar Musulunci a Kaduna, don qin amincewa da ƙoƙon baransa na zama maigidanta. Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin ɗin da ta gaba ne, inda Bala Musa ya gurfanar da jaruma Gabon gaban alƙali, kan ƙin amincewa su yi wuf da juna. Mai ƙarar ya sanar da kotu cewa, sun jima suna…
Read More
‘Yar wasan barkwanci Helen Paul ta zama Farfesa

‘Yar wasan barkwanci Helen Paul ta zama Farfesa

Daga AISHA ASAS Sananiyya kuma sharararriya a fagen nishaɗantarwa Helen Paul, ta kafa tarihi a duniyar barkwanci ta hanyar zama 'yar wasan barkwanci ta farko a Nijeriya da ta fara zama farfesa. Idan ba mu manta ba, a ‘yan kwanakin baya ne ta samu kammala digirinta na uku a ɓangaren wasan kwaikwayo wato Theatre Arts a jami’ar Iko. Halen ta bayyana wannan ne a shafukanta na sada zumunta. Ta kuma ƙara da taya mijinta murna kan tasa nasar ta zama dakta a vangaren karatun lauya(Doctor of Law) duk dai a jami’ar ta Iko. “Ina taya dukka ɗaukacin ‘ya’yan jami’armu. A…
Read More
‘Yan sanda sun tsaurara tsaro ga Salman Khan don kare shi daga barazanar kisa

‘Yan sanda sun tsaurara tsaro ga Salman Khan don kare shi daga barazanar kisa

Daga AISHA ASAS Biyo bayan tsananta bincike kan kisan da aka yiwa mawaqi Sidhu Moose Wala, jami'an tsaro sun bankaɗo Lawrence Bishnoi a matsayin wanda ake zargin da sa hannunsa a kisan, wanda ya kasance barazana ga babban jarumi Salman Khan. Da yake jawabi ga jaridar Hindustan Times, babban ɗan sanda na rundunar ‘yan sanda ta Mumbai ya ce, “mun ƙara tsaurara tsaro ga Salman Khan cikin ‘yan kwanakin nan, mun sanya jami’an tsaro sun kewaye gidansa, kowanne lungu da saƙo mun saka ido don tabbar da duk wani shiri na ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Rajasthan kan jarumin bai kai…
Read More
Shin ko kun san mece ce 13×13 da manufarta?

Shin ko kun san mece ce 13×13 da manufarta?

Daga HASHIM ABDALLAH Daga masu son shigarta, har zuwa kan masu rarraunar fahimta gare ta da masu neman fahimtar mece ce ko kuma dalilan adafin sunanta da sha'uku-sha'uku, duk ku buɗe kunnuwanku. Ma'anar 13x13 Thirteen-Thirteen ko in da Hausa ne, wato sha'uku-sha'uku. Ƙungiya ce samarwar mutane 13. Haƙiƙa kuma alkhairi ne, kamar yadda taken tafiyar yake, da aka yi imani zai 'yanta 'yan Najeriya domin samar da rayuwa mai inganci ko inganta rayuwar ta fuskoki daban-daban gaba da siyasa ko waƙar siyasa ko kamfe. Ba ta da wani maqiyi sai maƙiyin al'umma. A dalilin hadafi na 'yanta ƙasa, lallai 13x13…
Read More
Ku manta baya mu haɗa kai – Gidan Dabino ga ’yan Kannywood

Ku manta baya mu haɗa kai – Gidan Dabino ga ’yan Kannywood

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sabon shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Jihar Kano, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), ya ce, duk da rigingimu da Kannywood ta ke ciki zai yi iya yinsa ya ga ya ɗinke duk wata ɓaraka a matsayinsa na shugaba. Ya ce, "Wannan masana’anta da muka gina ta tun da jajayen sawunmu (mu na matasa) yau sama da shekaru 25, ya zama wajibi a gare mu da sauran ‘yan uwa da muke ta faɗi-tashi don ganin kada wannan masana’anta ta wargaje, mu haɗa hannu don mu daɗa samar mata da inganci…
Read More
Fim saƙo ne, kada a yawaita tunanin kuɗi da ɗaukaka yayin yinsa – Naziru Alkanawy

Fim saƙo ne, kada a yawaita tunanin kuɗi da ɗaukaka yayin yinsa – Naziru Alkanawy

“Komawar kasuwancin fim yanar gizo dama ce da ba a taɓa samun irinta ba” Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano  Naziru Alkanawy yana ɗaya daga cikin marubutan labarin finafinai da suka yi suna a cikin masana'antar Kannywwod, domin kuwa ya daɗe a harkar kuma duk wani babban labarin fim da ya fita ya yi suna a duniya za ka ga yana da sa hannu a ciki, musamman a tashar Arewa 24 da kuma labarun dirama na BBC da suke gabatarwa. A yanzu Naziru Alkanawy yana a matsayin mai zaman kansa kuma shine yake da shafin Rariya na YouTube da suke ɗora…
Read More