Nishadi

Dalilan Kannywood na ƙaurace wa bikin ZUFF 2022

Dalilan Kannywood na ƙaurace wa bikin ZUFF 2022

Daga BASHIR ISAH Gamayyar ƙungiyoyin masu shirya finai-finai a masana’antar Kannywood ƙarƙashin jagorancin MOPPAN da AFMAN sun aike wa Ministan Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed buɗaɗɗiyar wasiƙa suna masu sanar da shi dalilansu na ƙaurace wa bikin baje-kolin fina-fina da aka fi sani da ZUFF a taƙaice na 2022. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun Dr. Ahmad Muhammad Sarari na MOPPAN da Alhaji Sani Sule Katsina na AFMAN, ta nuna waɗanda lamarin ya shafa sun ƙi halartar bikin ne saboda nuna musu wariya da aka yi. Hukumar Kula da Harkokin Fina-finai na ta Ƙasa (NFC), ita ce mai shirya…
Read More
Nollywood ta shirya finafinai 541 a wata uku – Hukumar Tace finafinai

Nollywood ta shirya finafinai 541 a wata uku – Hukumar Tace finafinai

Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa, NFVCB, ta ce, hukumar ta karɓa tare da tace finafinai 541 da masana’antar finafinan Nijeriya ta Nollywood ta shirya a farkon kwata ta shekarar 2022. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Adedayo Thomas, Babban Daraktan NFVCB ya fitar a Juma’ar makon jiya a Abuja. Ya ce sashen Tace Finafinai da Tantancewa na hukumar ne suka fitar da wannan ƙididdiga a cikin rahotonta na kwata ta farko na shekarar bana. Thomas ya ce, rahoton ya ɗauki dukkan finafinan da aka miƙa wa hukumar daga sassan ƙasar. Ya…
Read More
Na bai wa Ado Gidan Dabino kundin warware matsalolin Kannywood – Farfesa Abdalla

Na bai wa Ado Gidan Dabino kundin warware matsalolin Kannywood – Farfesa Abdalla

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta gabatar da taron shan ruwan azumi da kuma ƙaddamar da sabbin shugabanni na Jihar Kano da ya gudana a Kannywood TV a Kano. A jawabinsa, Farfesa Abdullahi Uba Adamu, wanda shine baƙo na musamman a wurin, ya ce, a ra'ayinsa da ma babu wanda ya fi cancanta da ya riƙi shugabancin Kannywood, kamar Ado Ahmad Gidan Dabino, yana mai cewa, wannan ne dalilin da ya sa ya ba shi wani kundi, wanda idan ya bi…
Read More
Sharhin fim ɗin ‘Lamba’

Sharhin fim ɗin ‘Lamba’

Daga HABIBU MA'ARUF ABDU  Shahararren kamfanin shirya finafinai na Maishadda Global Resources Limited, wanda a baya-bayan nan ya zama kamfani mafi tasiri a masana’antar Kannywood, ya shirya finafinan barkwanci da dama tare da fitaccen Darakta, Ali Gumzak. Fim ɗinsu na ƙarshe "Ka yi na yi" shi ne wanda ya fi kowanne fim tattara kuɗi yayin haska shi a Sinima a shekarar da ta gabata.  A wannan sabuwar shekarar ma, sai ga shi sun shigo da wani fim ɗin barkwancin mai suna Lamba. Fim ne wanda, cikin barkwanci, ya ƙalubalanci yadda jama'a suke yin rayuwar ƙarya musamman a kafofin soshiyal midiya.…
Read More
Bai kamata a riƙa yi wa ‘yan fim kallon karuwai ba – Hafsat Ammi

Bai kamata a riƙa yi wa ‘yan fim kallon karuwai ba – Hafsat Ammi

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano  Jaruma Hafsat Hassan, wacce aka fi sani da Ammi, sabuwar jaruma ce da ta fara taka rawarta a masana'antar shirin finafinan Hausa ta Kannywwod. Duk da cewar ba ta daɗe da shigowa ba, amma dai a yanzu ta fara zama fitacciyar jaruma, musamman a waƙoƙin da suke fitowa a wannan lokacin. Don haka Wakilin Blueprint Manhaja, Mukhtar Yakubu, ya tattauna da ita, don jin yadda ta samu kanta a cikin harkar ta fim. Sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance: MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu…
Read More
‘Allah ya ba mu shugabanni adalai’, addu’ar Ali Nuhu ga Nijeriya

‘Allah ya ba mu shugabanni adalai’, addu’ar Ali Nuhu ga Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Jarumi a masana'antar Kannywood, Ali Nuhu, ya yi addu'ar samun shugabanni adalai kuma masu jin ƙai ga Nijeriya. Jarumin ya yi wa ƙasarsa waɗannan addu'o'i ne yayin hajjin Umarah da ya tafi kamar yadda saƙon da ya wallafa a shafinsa na facebook ya nuna. An ga Ali Nuhu tare da ɗansa Ahmad cikin harami a wasu hotuna da ya wallafa a shafin nasa na Facebook. Ali Nuhu ya yi addu'a da cewa, "Allah Ya karɓi ibadunmu, ya inganta rayuwarmu, ya sanya wa kasuwancinmu albarka, ya raya zuri’armu bisa tafarki madaidaici. Ali Nuhu tare da ɗansa Aahmad "Ya…
Read More
Sakataren MOPPAN ya zama jami’in shirye-shiryen Kamfanin Northflix

Sakataren MOPPAN ya zama jami’in shirye-shiryen Kamfanin Northflix

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An farkon makon nan aka naɗa fitaccen jarumin Kannywood, Umar Gombe, a matsayin jami’in shirye-shirye na Kamfanin nuna finafinai na Northflix. A cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun Shugaban Kamfanin Northflix, Alhaji Jamilu Abdulsalam, ta nuna cewa, an naɗa Mataimakin Sakataren MOPPAN na Ƙasa, wato Umar Gombe, a matsayin Jami'in Shirye-shiryen kamfanin na farko.Gombe zai jagoranci fannin shirye-shirye na kamfanin wajen bunƙasa harkar kasuwancin finafinan Hausa a duniya.  A yayin da ya ke yin ƙarin haske dangane da kamfanin, Alhaji Abdulsalam ya nuna cewa, musabbabin buɗe cibiyar Northflix shi ne, domin ƙara…
Read More
Kan yaƙi da cin hanci da rashawa muka shirya fim ɗin ‘Rumfar Mai Shayi’ – Nasir B.

Kan yaƙi da cin hanci da rashawa muka shirya fim ɗin ‘Rumfar Mai Shayi’ – Nasir B.

Daga IBRAHIM HAMISU Kano 'Rumfar Mai Shayi' fim ne mai dogon zango, wato ‘series’, wanda babban kamfanin shirya finafinai da horarwa a masana'artar shirya finafinai ta Kannywood, wato 'Moving Image Nig. Ltd., wanda Alhaji Abdulkarim Muhammad ke jagoranta. A wannan karon, filin Nishaɗi na Bleuprint Manhaja ya zanta da babban darakta kuma malamin da ya ke koyarwa a fagen shirya finafinai, sannan ya ke fitowa a matsayin Dogarin Gwamnan Alfawa a cikin fim ɗin 'Kwana Casa'in', Wato Nasir B. Muhammad. A zantawarsa da Wakilinmu a Kano, za ku ji manufofi da maƙasudin shirya fim ɗin 'Rumfar Mai Shayi'. Ku biyo…
Read More
Rayuwar Michael Jackson, sarkin gambarar zamani

Rayuwar Michael Jackson, sarkin gambarar zamani

Daga AISHA ASAS Ba-Amurken mawaƙi da duniya ta sani kuma ta ke bibiyar sa fiye da kowanne mawaƙi da tarihi ya san da zamansa. Ya kafa tarihin da ake tsammanin ba a nan kusa ba samun wanda zai iya kai inda ya kai bare har ya fi shi. Mawaƙi ne da ke waƙa daidai da zukatan mutane mafi rinjaye masu muradin kaɗe-kaɗe, kai har ma waɗanda ke ƙoƙarin ganin ba su bi hanyar da rawa da waƙa ta bi wasu daga cikin su na ganin ƙwarewarsa. Michael Joseph Jackson, sarkin gambarar zamani wato ‘King of hip pop’ a Turance, ya…
Read More
Rikicin Smith da Chris: Oscar Award sun dakatar da Smith shekaru 10

Rikicin Smith da Chris: Oscar Award sun dakatar da Smith shekaru 10

Daga AISHA ASAS Hukuncin da mahukunta suka sha alwashin ɗauka kan jarumi Will Smith game da labta wa Chris Rock mari a bainar jama'a, a ranar bikin karramawa na Oscar Award ya bayyana, inda ƙungiyar ta haramta wa Smith halartar taro irin wannan da ma takwarorinsa na tsawon shekaru goma. A ranar Juma'ar nan da ta gabata ne, masu alhakin shirya gagarumin bikin bayyar da kyauta na Oscar wato Academy of Motion Pictures Arts and Sciences suka bayyana abin da Smith ya aikata a matsayin abin da ba a lamunta da shi ba, kuma ba zai tafi ba tare da…
Read More