Nishadi

Mu ’yan Kannywood muna da tsarki kamar ruwan zamzam, inji Halima Atete

Mu ’yan Kannywood muna da tsarki kamar ruwan zamzam, inji Halima Atete

“Dalilin da ya sa ban taɓa tsoma kaina a rigimar Kannywood ba” Daga AISHA ASAS Sananniyar jaruma a masana'antar Kannywood kuma mai shirya fim, Halima Atete, ta shigo masana’antar tun shekaru 10 baya, kuma za mu iya cewa, ta shigo da ƙafar dama, duba da irin nasarori da ta samu, ciki kuwa har da sarautar masana’artar wato ‘Sarauniyar Kannywood” da ake yi mata laƙabi da ita. A zantawarta da Jaridar Blueprint, jarumar ta bayyana cewa, a yanzu ta cika burinta a masana’antar, ta na mai cewa, kwalliya ta riga ta biya kuɗin sabulu a zaman da ta yi a cikin…
Read More
Yadda mawaƙa suka taya Aminu ALA murnar sarautar Sarkin Ɗiyan Gobir

Yadda mawaƙa suka taya Aminu ALA murnar sarautar Sarkin Ɗiyan Gobir

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A sakamakon naɗin da aka yi wa fitaccen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar ALA a matsayin Sarkin Ɗiyan Gobir, a Masarautar Tsibirin Gobir da ke Jihar Maraɗi a Jamhuriyyar Nijar. Abokan sana'ar sa ta waƙa sun taya shi murna a wani gagarumin taro da aka shirya. Taron, wanda aka shirya shi a ranar 12 ga Maris, 2022, a wajen taro na gidan Rediyon Premier da ke kan titin filin sukuwar dawakai a cikin garin Kano, ya samu halartar mawaƙa daga jihohi daban daban na ƙasar nan, in da suka shafe tsawon wuni guda suna bajekolin su…
Read More
Komai da ruwanka: Yadda na ke tauna taura biyu a Kannywood da Nollywood – Usman Uzee

Komai da ruwanka: Yadda na ke tauna taura biyu a Kannywood da Nollywood – Usman Uzee

Daga AMINA YUSUF ALI Hausawa dai kan ce, wai taura biyu ba ta taunuwa lokaci guda a cikin baki. To, amma ba haka ba ne ga Jarumi furodusa wanda ya ke taka rawa a fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da kuma takwararta ta Kudancin Nijeriya, wato, Nollywood. Usman Uzee ɗan asalin Jihar Kwara ne, amma girman Jihar Kaduna ne. Ya yi digirinsa kala biyu a ɓangaren fannin siyasa da kuma harshen Ingilishi a jami'o'in Abuja da kuma Jos. Sannan ya cigaba da karatunsa a Afirka ta Kudu. Ya shiga harkar fim a shekarar 2003 a matsayin mai kwalliya. Usman ya…
Read More
Mawaƙi Salisu Mariri zai angonce yau Juma’a

Mawaƙi Salisu Mariri zai angonce yau Juma’a

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Idan Allah ya kaimu ƙarfe 2:30 na wannan rana ta Juma'a, za a ɗaura auren mawaƙi, jarumi kuma furodusa a masana'antar Kannywwod, Salisu Nuhu Mariri, tare da amaryarsa, Maryam Muhammad, a unguwar Rigasa da ke garin Kaduna. Kamar yadda katin gayyatar auren ya sanar, matashin jarumin yana gayyatar 'yan uwa da abokai da kuma dukkan masoyansa zuwa wajen wannan ɗaurin auren, kuma ga duk wanda bai samu damar zuwa ba, sai ya taya su da addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya. Shi dai Salisu Nuhu Mariri, yana cikin mawaƙan harkar fim sama da shekaru…
Read More
MOPPAN ta shirya taron wayar da kai kan amfanin soshiyal midiya

MOPPAN ta shirya taron wayar da kai kan amfanin soshiyal midiya

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato Motion Picture Practitioners Associations of Nigeria, tare da haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, sun shirya taron wayar da kan masu sana’ar ta shirin fim a kan yin amfani da soshiyal midiya ga ’yan Masana'antar Kannywwod. Taron na wuni guda, wanda aka gudanar da shi a ranar Alhamis, 10 ga Maris, 2022, a ɗakin taro na Kannywwod TV da ke titin Muhammadu Buhari a Birnin Kano, ya samu halartar masu gudanar da harkar fim da suke dukkan jihohi na Arewacin Nijeriya da ma…
Read More
MOPPAN da NFVCB za su gudanar da taron yini biyu a Kano

MOPPAN da NFVCB za su gudanar da taron yini biyu a Kano

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar masu shirya fina-finai MOPPAN a taƙaice ta ce, ta shirya gudanar da taron yini biyu ga masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai don bunƙasa harkar. Sanarwar manema labarai da MOPPAN ta fitar ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a na ƙasa, Al-Amin Ciroma, ta nuna taron na haɗin gwiwa ne tsakanin MOPPAN da Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa (NFVCB). Sanarwar ta ce taron na yini biyu ne kuma zai gudana ne a ranakun 9 da 10 ga Maris, 2022 a birnin Kano. Taron wanda zai maida hankalin wajen tattauna harkar fina-finai a soshiyal midiya,…
Read More
Duk inda Bagobiri ya ke ɗan uwana ne, inji Alan waƙa

Duk inda Bagobiri ya ke ɗan uwana ne, inji Alan waƙa

*Aminu Ala ya ƙara samun sarauta a Masarautar Tsibirin Gobir Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Aminu Ladan Abubakar Ala, Sarkin Waƙar Masarautar Dutse, Ɗan amar Bichi, Dujiman Ƙaraye, Ɗan Buran na Sabon Birnin Gobir, mawaƙi ne da ya shahara a fagen waƙoƙin zamani wanda samun irin sa abu ne mai wahala saboda ɗaukakar da Allah ya yi masa a cikin mawaƙan zamanin. Domin kuwa Shaharar sa ta kai shi ga samun matsayi a fadojin sarakuna da suka ba shi sarautu kamar yadda yake a sama. Kuma wannan wata ɗaukaka ce da baiwar da ba kowa yake samun ta ba a…
Read More
An ɗaura auren Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, bayan canjin waje da lokaci

An ɗaura auren Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, bayan canjin waje da lokaci

Daga WAKILINMU A jiya Juma'a aka ɗaura auren jarumar Kannywood, Aisha Muhammad Ali, da aka fi sani da Aisha Tsamiya, tare da agonta Alh Buba Abubakar. An ɗaura auren ne kamar yadda aka tsara, sai dai an samu sauyin wajen ɗaurin auren da kuma lokaci saboda dalilai na tsaro. Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna an samu sauyin wuri da kuma lokacin ɗaurin auren ne kasancewar angon babban mutum ne sananne, haka ma amaryar fitacciyar jaruma ce wadda ke da ɗimbin masoya, wanda hakan ya sa aka ɗauki matakin sauyin don kauce wa duk matsalar da ka iya…
Read More
Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, za ta yi aure gobe

Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, za ta yi aure gobe

Daga BASHIR ISAH Gobe idan Allah Ya kai mu ne za a daura auren jarumar Kannywood, Aisha Muhammad Ali wadda aka fi sani da Aisha Tsamiya. Katin gayyatar da MANHAJA ta samu ya nuna za a ɗaura auren ne tsakanin Aisha da agonta Alh. Buba Abubakar. Auren wanda za a ɗaura da misalin ƙarfe ɗaya na rana bayan an sauko daga Juma'a zai gudana ne a Masallacin Sheikh Zarban, Kwanar 'Yan Wanki kusa da gidan Tanko Yakasai, 'Yankaba, Kano. Ana sa rai da fatan wannan aure ya zama silar ƙulla zumunta tsakanin iyalan gidan Alh. Muhammad Yaya da na gidan…
Read More
Duk Kannywwod ba wanda ya kai ni kayan aiki, inji Rashida Maisa’a

Duk Kannywwod ba wanda ya kai ni kayan aiki, inji Rashida Maisa’a

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano. Fitacciyar jaruma kuma furodusa a masana’antar shirin finafinan Hausa ta Kannywood, Rashida Adamu Abdullahi Maisa'a, tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suka daɗe a na damawa da su a cikin harkar fim kafin daga baya ta juya akala ta zama 'yar siyasa. Abubuwa guda biyu sun faru a wannan lokacin, wanda ya sa a ke tambayar ko dai jarumar ta dawo harkar fim ne bayan tsawon lokacin da ba a ganinta? Abu na farko dai zaɓar ta da aka yi a matsayin Mataimakiyar Shugabar Ƙungiyar 'Arewa Film Markets Associations Of Nigeria' (AFMAN). Na biyu kuma ganin…
Read More