MOPPAN da NFVCB za su gudanar da taron yini biyu a Kano

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar masu shirya fina-finai MOPPAN a taƙaice ta ce, ta shirya gudanar da taron yini biyu ga masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai don bunƙasa harkar.

Sanarwar manema labarai da MOPPAN ta fitar ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a na ƙasa, Al-Amin Ciroma, ta nuna taron na haɗin gwiwa ne tsakanin MOPPAN da Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa (NFVCB).

Sanarwar ta ce taron na yini biyu ne kuma zai gudana ne a ranakun 9 da 10 ga Maris, 2022 a birnin Kano.

Taron wanda zai maida hankalin wajen tattauna harkar fina-finai a soshiyal midiya, amfani da illolinsa ga al’umma, za a saurari muƙalu daga masana daban-daban.

Haka nan, sanarwar ta ce MOPPAN za ta yi taronta a yini na biyu don tattaunawa kan yadda za ta warware matsalolin da aka hango yayin taronta da ya gudana a Janairun da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *