19
Feb
Daga BASHIR ISAH Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya naɗa Khalid Musa a matsayin Babban Hadimi na Musamman (SSA) kan sha'anin masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, naɗin da ya soma aiki daga ranar 8 ga Fabrairun 2022. Sanarwar naɗin na ƙushe ne cikin wasiƙar da sashen REPA da ke ƙarƙashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Kano, wadda Babbar Sakatariyar REPA, Bilkisu Shehu Maimota ta sanya wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar. A cewar wasiƙar, an naɗa Musa a matsayin SSA ne duba da jajircewarsa, sadaukarwa a bakin aiki, sanin makamar aiki, ƙwazo da kuma biyayyar da yake da su, wanda…
